Daga Talha Yavuz
Donald Trump bai taba nuna sanya ba wajen amfani da sanya haraji a matsayin makami, kuma wa'adinsa na biyu ma bai bambanta da na farkon ba.
A ranarsa ta farko da ya kama aiki a karo na biyu, Trump ya sake jaddada tsattsaurin matsyinsa na yin barazanar kara haraji da kashi 100 kan duk wata kasar BRICS da ta ci gaba da dabbaka manufar daina amfani da dalar Amurka wajen gudanar da kasuwanci.
Tuni Trump 2.0 ya fara sanar da karin haraji da kashi 25 kan Mexico, kashi 25 kan Canada a kashi 10 kan China kuma ya yi alkawarin za a karo wani sosai ga kayayyakin da kasashen ke shigarwa Amurka.
A yayin da yake kokarin janyo wani sabon yakin kasuwanci, shin Washington na iya jure sa in sar tattalin arziki da kawancen da ke da yawan rabin al'ummar duniya?
Kuma idan Trump ya ci gaba da matsa lamba, ta yaya BRICS za ta jure matsin lambar?
Dala a matsayin kudin rara na ajiya
Tsawon shekaru, dalar Amurka ta zama kashin bayan kasuwancin duniya, mamayar da da Bretton Woods suka sake karfafawa da karfin tattalin arzikin Amurka.
A karni na 20, Fan din Birtaniya ya taka rawa irin wannan. Sai dai kuma, bayan Yakin Duniya na II, durkushewar tattalin arziki da ykin basussuka ya janyo dalar Amurka ta zama kudin da ke mu'amala da shi a dukkan duniya wajen kasuwanci.
Washington ba ta gaza ba wajen amfani da wannan dama a matsayin jigon mamaya da karfa-karfa.
Rasha ta yi fama da wannan, bayan mamayar Ukraine, Amurka ta rike daruruwan biliyoyin kadarorin Rasha, ta saka musu takunkumai, tare da cire Mozscow daga tsarin sha'anin kudi na duniya.
Kazalika, a loakcin rikicin Brunson, Turkiyya ta fuskanci matsin tattalin arziki daga Amurka, tana mai bayyana yadda Washington ta ke amfani da sha'anin kudi wajen murkushe abokan adawa.
Amfani da takunkumi, haraji, tsarin SWIFT, da karfin dala na zama makamai a kowanne lokaci ga Amuka.
Baya ga wasu lokuta da aka gani a kawancen BRICS, rikicin rasha da Ukraine ya zama kamar kiran a tashi a farka ga kasashe da dama, ana tunatar da su kan dogaro da suka yi a kan dalar Amurka.
A 'yan shekarun nan, kasashe da dama sun dauki matakan rage dogaro kan dalar Amurka.
Misali, China da Barazil ba gudanar da kasuwanci da kudadensu ta hanyar kaucewa dala. India da Malaysia ma sun sanya hannu kan yarjejeniyar kara yawan kasuwanci da kudin rupee.
Bankin Indonesia ya rage dogaro kan dalar Amurka ta hanyar kulla kawance da bankin RBI na India.
Kazalika, Koriya ta Kudu da Indonesia sun sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kudade tsakanin won da rupiah.
Dadin dadawa, rasha da China suna kaucewa amfani da dala tsawon shekaru da yawa.
Tun 2019, Moscow da Ankara suna da yarjejeniyar da ta tanadi gudanar da kasuwanci da kudaden kasashensu.
Kawancen tattalin arziki ko gwada kwanjin yankuna da siyasa?
Tare da yadda mambobinta ke da kashi 30 kudaden icikin gida ada ke samu a duniya kuma na uku wajen fitar da man fetur a duniya, ana ci gaba da kallon BRICS a matsayin mai kalubalantar Yammacin duniya.
BRIC da aka kafa fara kafawa a 2006 - Barazil, Rasha, India, da China - a 2010 ta kara fadi bayan an kara Afirka ta Kudu, sannan aka kara Iran, Hadaddiyar Daular Larabawa , Masar, Ethiopia da Indonesia.
Turkiyya ma ta nuna sha'awar shiga kawancen kuma an ba ta matsayin "kasa abokiya" tare da Aljeriya, Belarus, Bolivia, Cuba, Indonesia, LKazakhstan, Malaysia, Nijeriya, Thailand, Uganda, Uzbekistan da Vietnam.
A 2014, BRICS sun kaddamar da Sabon Bankin Cigaba don daukar nauyin gudanar da manyan ayyuka, kuma an samu tattaunawa don samar da kudin bai daya - duk da dai ba a dauki wasu kwararan matakan tabbatar da hakan ba.
Ana yi wa BRICS wani sauyi mai kalubalantar kawancen G7 da hukumominsu.
Amma duk da haka, duk da burinsu, BRICS na fuskantar babbar jarabawa: Ta yaya za su mayar da martani ga barazanar lafta haraji ta Trump?
Rasha, ta sha wahala sosai daga kasuwannin Amurka saboda takunkumi, za ta iya zama a ware daban.
China, duk da daukar darussa daga yakin kasuwanci a lokacin mulkin Trump na farko, a yanzu ta samu 'yanci sama da a baya. sai dai kuma, har yanzu ita ce ta fi kwaruwa da cutuwa daga manufofin kasuwanci na Trump.
Amurka ce babbar kawar kasuwanci ta China. Yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 574 a 2023, inda China ke amfana da dala biliyan 279.
Wani sashe babba na kayan da China ke fita da su kasashen waje sun hada da wayoyin hannu, kayan gyaran kwamfuta, kayan lantarki, kayan sa wa na kasa, kayan dakin girki, da kayan masana'antu.
India ma, na iya samun damarmaki, a yayin da gibin kasuwanci yake kan dala biliyan 43 wanda India ke amfana, a yayin da adadin jarin kasuwanci ya kai dala biliyan 124 a 2023.
Abubuwa mafi yawa da India ta fi fitarwa zuwa kasshen waje sun hada da duwatsun carbi, duwatsu da karafa masu daraja, kayan magunguna da albarkatun mai.
Sakamakon bayyana cewa hrajin Trump zai janyo daukar fansa da ramuwar gayya da kan iya janyo hauhawar farashi ga masu sayen kayayyaki a Amurka.
Lokaci mai muhimmanci
Ko ma ba tare da katsalandan din Amurka ba, ba lallai kudin BRICS ya samu karbuwa ba.
Kudin da za a karbe shi a duniya na bukatar samun gurbin zama a cikin gida, kamar dai yadda Turancin Ingila ya mamaye duniya, amma Esperanto ya kawo karshe.
Kudin IMF na SDR, wani kudi da aka samar don shiga tsakanin kudaden kasashe, bai samu karbuwa ba saboda ba shi da tsayayyen mai samar da shi da aka aminta da shi.
Idan kudin BRICS zai yi gogayya da dalar Amurka, to dole ne kasashen BRICS su hakura da kudaden kaashensu tare da samar da hadin kan amfani da kudin bai daya a karkashin babban banki guda daya - wanda akwai kalubalen siyasa da tattalin arziki.
Kuma tuntuni ma, kasashen BRICS ba sa tattauna batun samar da kudin bai daya, kamar yadda kakain fadar Cremlin Dmitry Peskov ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a karshen watan Janairu "A madadin hakan, BRICS sun mayar da hankali wajen kafa zuba jarin bai daya don amfanar juna da gudanar da ayyuka a kasashe masu tasowa," in ji shi.
Babban kalubalen ma shi ne cewa tattalin arzikin kasashen BRICS ya bambanta da juna a saboda haka ba zai iya rungumar wannan tsari ba.
Kawancen amfani da kudade da ya yi nasara, kamar na Turai, na wanzuwa ne da dorewa a tsakanin tattalin arzikin a ke kama da juna da kuma kasuwanci iri guda, alakar kasuwanci mai zurfi, da kuma samun ayyuka da wurwuri.
Amma sabanin haka, BRICS na tattare da tattalin arziki mabambanta a yayin da China da Afirka ta Kudu, India da Rasha - kowanne na da manufofin kudi, fasalin tattalin arziki da fifikon siyasa da suka sha bamban da na dayan.
A irin wannan yanayi, kudin bai daya na iya haifar da rashin daidaito, inda tattalin arziki guda daya zai danne dayan inda dayan kuma zai durkushe, ba tare da ikon daidaita kudin ruwa da na farashin kudaden kasahenw waje.
Ba tare da wata mafita ba ta tsare-tsare - tsallakwa wata kasa a samu ayyukan yi ko tsarin siyasa mai karfi - wadannan bambance-bambance na iya kai wa ga haifar da rikici maimakon zaman lafiya.
Trump na iya kallon BRICS a matsayin kalubale ga mamayar da dalar Amurka ta yi, amma sabanin da ke cikin kawnacen ne babban kalubalensu.
Kasashen BRICS+ na cikin nahiyoyi hudu, na magana da yaruka daban-daban, kuma a tarihi ma suna rikicin kan iyakoki, kamar yadda aka gani tsakanin sojojin China da India.
Tattalin arzikinsu na bin salon kasuwanci mabambanci - hauhawar farashin makamashi na amfanar masu samar da mai irin su Rasha da Barazil amma na kuntatawa masu saya irin su China da India - wana ke sanya batun samar da kudin bai daya na da wahala kuma na rage yiwuwar samar da kudin BRICS mai dorewa.
Gargadi da wa'adin Trump ya fi karfin batun rikicin kasuwanci kawai - jarrabawar hadin kan BRICS ce.
Idan har zuka zauna daram, BRICS na iya yin karfi sosai, su hanzarta tsarin samar da kudi da ka iya kawar da mamayar yammacin duniya a kan su.
A yayin da ba za a iya kawar da dalar Amurka dare daya ba, adawa da Trump ke nuna wa na iya hanzarta kokarin kasashen BRICS su samar mafita a harkokin sarrafa kudade don kawar da mamayar da dala ta yi.
Marubu, Talha Yavuz, tsohon wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ne a Kiev kuma a yanzu na tare da Sashen Tsara Fitar da Labaran Kasashen Waje a AA. Yavuz na yi rubutu kan Rasha, Ukraine da Eurosia.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.