Daga Nadim Siraj
Tsohon babban lauyan Amurka Ramsey Clark ya taɓa yin wani dogon nazari game da rawar da Amurka ke takawa a siyasar duniya: “Babban laifin da aka aikata tun Yaƙin Duniya na biyu shi ne manufofin kasashen waje na Amurka.”
Maganar mai ƙunshe da gaskiya ta yi kamar ba a taɓa yin irinta ba yayin da duniya ke fafutukar ganin an cim ma matsaya game da mummunan shirin Donald Trump na mamaye Gaza.
Shugaban na Amurka wanda ba a iya sanin inda ya sa gabansa ya yi abin da ya shallake tunanin mutan lokacin da ya fito da wani mugun tsari kwanan nan wanda ya wargaza duk iyakokin diflomasiyya da mutunci.
Ya ba da shawarar wani shiri cewa Amurka za ta karbe iko da yankin Gaza wanda yaƙi ya ɗaiɗaita, ya kuma raba Falasdinawa miliyan 2.1 da muhallansu, da nufin zai sake gina da bunƙasa yankin da sauya masa suna zuwa "Dausayin Gabas ta Tsakiya", wato "Riviera of the Middle East."
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da sakatariyar yada labaran Fadar White House, Karoline Leavitt, sun yi kokarin rage tasirin tayar da hankalin da maganar ta yi, inda suka ba da tabbacin cewa shiri ne na wucin gadi kuma ba za a samu wata matsala ba.
Amma shugaban ƙasar nasu ya yi watsi da kalaman kwantar da hankalin da suka yi, yana mai jaddada cewa tabbas Amurka "za ta karɓi Gaza".
"Za mu karɓe ta, za mu riƙe ta, za mu ji dadinta," kamar yadda ya shaida wa manema labarai a Ofishin Oval.
'Mun kaɗu', 'abin ban mamaki', 'ba zata', 'abin da ba a taba ganin irinsa ba' - waɗannan su ne wasu daga cikin kalaman da ake amfani da su a cece-kucen da aka yi don bayyana rashin dacewar shirin na Trump.
Amma idan mutum ya ɗan yi waiwaye baya kaɗan kuma ya yi nazarin lamarin da kyau, zai fahimci cewa shirin Trump na Gaza ba zai zama abin mamaki ba.
Bai zo da mamaki ba
A taƙaice dai, idan aka yi nazari na tsawon lokaci kan manufofin harkokin wajen Amurka masu tada hankali, za a ga salonsu ke nan - za a fahimci cewa shirin Trump na Gaza cigaba na faɗaɗa manufofin Amurka na dogon zango.
Batun shirin karbar Gaza na ɗaya daga cikin aƙidun Amurka na son yin katsalandan da shiga sharo ba shanu da mamaya da ta'azzara yaƙi da ƙwace iyaka wanda ya saɓa wa dokokin na diflomasiyya.
Ku tuna cewa a lokacin yakin neman zaben Trump da kuma nasarar da ya samu a zaben, ba a kan Gaza kawai yake da wannan manufar ba. Ya dade yana ihun cewa yana son Amurka ta ƙwace ko sayen Canada da Greenland, ta ƙwace mashigin ruwan Panama.
Ko yankunan tekun da ke kusa da Amurka ba su tsira daga haɗamar Trump ta son mamaye su ba. Fadar White House kwanan nan ta sanya manhajar taswira ta Google Map ta sake wa Mashigin Mexico wato Gulf of Mexico suna zuwa 'Gulf of America' ga masu amfani da manhajar na ƙasar.
Dogon tarihi mai muni
Tarihi ya nuna cewa Trump shi ne babban kwamandan kwamandoji na baya-bayan nan na fitattun jerin shugabannin daular Amurka da ta yi ƙaurin suna a yin katsalandan kan iyakoki da mamaya daga wannan zuwa wancan tun farkon ƙarni na 19.
Dangane da bayanai daga kungiyar da ke sa ido kan yawan jama'a ta duniya, sojojin Amurka sun mamaye kasashe kusan 68 tsakanin shekarar 1812 da 2024.
Ba da daɗewa ba bayan samun 'yancin kai na Amurka a cikin 1776, Amurka ta dinga yaɗa ginshiƙanta na burin mulkin mallaka a cikin nahiyoyi - yaƙe-yaƙe na hukuma da na cacar baka da yin katsalandan cikin harkokin wasu ƙasashe da kuma kwace yankuna.
An rubuta tarihin cin zarafi na Amurka da manufofin kasashen waje a cikin wani littafi da aka wallafa a 2014 mai taken, America Invades: How We've Invaded or Been Militarily Involved with Almost Every Country on Earth’. wanda ya yi duba kan mamayar Amurka da katsalandan a kusan harkokin kowace ƙasa ta duniya.
A cewar littafin, daga cikin kasashe 194 da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su, Amurka ta mamaye akalla 84 daga cikinsu kuma ta yi ƙawance da 191 - wanda ya bar kasashe uku kawai: Andorra, Bhutan, da Liechtenstein.
Ban da ma abin da ya faru a cikin karni na 19, ko da tarihin baya bayan nan - bayan yakin duniya na biyu - Amurka ta yi munanan yaƙe-yaƙe da shisshigi waɗanda suka take haƙƙin ɗan'adam da mamaye yankuna.
Tabo na baya bayan nan
A nan ga wani ci gaba mai ban sha'awa na wasu mashahuran munanan manufofin harkokin waje na Amurka tun ƙarshen yakin duniya na biyu a 1945.
A cikin 1953, Amurka ta tura CIA a Iran don shirya juyin mulkin da aka yi wa zababbiyar gwamnatin firaminista Mohammad Mossadegh.
A cikin 1960, Amurka ta aika da CIA don kashe shugaban Kongo Patrice Lumumba saboda karkatar da ya yi ga USSR.
Hukumar leken asiri ta CIA da kanta ta yi alfahari da nuna munanan ayyukanta a Kongo a shafinta na intanet.
Daga nan sai Amurka ta shafe shekaru 20 tana lalata alaƙarta da tsohuwar Tarayyar Soviet a cikin mummunan yakin Vietnam, wanda aka yi shi daga shekarar 1955 zuwa 1975.
Amurka ta faɗaɗa yakin Vietnam ta hanyar kutsen soja na rashin tausayi a cikin Cambodia a 1970. Shekaru uku bayan nan, Amurka ta shiga cikin Chile don kawo ƙarshen mulkin kama-karya na Augusto Pinochet a 1973.
Sannan mun shaida yadda sojojin Amurka suka mamaye yakin Gulf a 1991 a Iraki, da mamayar Amurka a Afghanistan a 2001, da dawo da yaƙin Gulf a Iraƙi a 2003, da kifar da gwamnatin Haiti a 2004, da tarwatsa Libya a 2011, da kuma shiga cikin Syria a 2014.
Gaba ɗaya batun na ba da labarin mummunan tarihin gwagwarmayar manufofin ƙetare na Amurka wanda ke fahimtar da mu gaskiya guda ɗaya ta son mamaye iyakoki da ƙasar ke yi, duk kuwa da sauyin shugabannin da ake samu a Fadar White House, amma manufofin duk iri ɗaya ne.
Shiga tsakani a baya da a yanzu
A lokacin baya, mun ga yadda ta kaya a Vietnam da tayar da bama-baman Hiroshima-Nagasaki da Yaƙin Gulf da Afghanistan.
A yau, muna da Gaza da, Kanada da Greenland, da Panama a kan burin. Tabbas, katsalandan na nan gaba ba zai haɗa da zubar da jini ba. Amma ko yaya dai, burin mamayar zai cigaba da fakar sabbin wurare.
Yana da muhimmanci a lura cewa barazanar da Trump ya yi ta mamaye Gaza ba za ta zama mai sauƙi ga duniya ta yi watsi da ita ba. Saboda Amurka ta fi kowa daɗewa tana cin zali a duniya idan aka zo ga batun mamaya da kafa sansanonin soja a ƙetare.
Har zuwa kwanan nan, an bayar da rahoton cewa, ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon tana da sansanonin soji akalla 750 a sassa daban-daban na duniya, wanda ya ƙunshi ƙasashe kusan 80.
Amurka ta fi saka hannun jari a cikin sojojinta fiye da kasashe goma idan aka haɗa. Yawancin sansanonin Amurka suna cikin Japan da Jamus, da Koriya ta Kudu.
Wannan yanayin na kasancewar sojojin Amurka a ƙetare yana jadada fa'idar daular Amurka ta zamani.
Har ila yau, ya bayyana dalilin da ya sa Fadar White House ta Trump, duk da cewa ba ta nemi ƙaddamar da yaƙe-yaƙe na al'ada ba, tana da ƙarfin ikon neman haƙƙin Gaza da sauran sabbin hare-hare.
Tsohon jami'in diflomasiyyar Amurka, Marigayi Henry Kissinger, ya taba rubuta cewa - "Sabuwar odar ƙasa da ƙasa ba za ta yuwu ba ba tare da muhimmiyar gudunmawar Amurka ba."
Abin baƙin ciki, fiye da shekaru 200 har zuwa yanzu, wannan 'muhimmiyar gudunmawar ta Amurka' ta kasance mai cin rai wadda ba a maraba da ita.
Trump da makircinsa na Gaza misali daya ne kawai a cikin dogon batun da Kissinger ya kira gagarumar gudunmawar Amurka. Abin baƙin ciki, za a iya samun wasu da yawa masu zuwa - a lokacin Trump da ma bayan saukar sa.
Marubucin, Nadim Siraj, ɗan jarida ne a Indiya, kuma marubuci a kan harkokin diflomasiyya da rikice-rikice da harkokin ƙasa da ƙasa.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.