Daga Burak Elamali
Daga samar da hasken rana zuwa sayar da makamai da kuma ba da shawarwarin warware matsalolin da suka dade tare da mamaye yankin, muhimmiyar rawar da kasar China ke takawa a yankin Gulf na Tekun Fasha ya zarce duk wani yanayi na samun riba da suna.
Irin gayyatar da Shugaba Xi Jinping ya yi a taron kolin China na GCC a shekarar da ta gabata kan shirin samar da tsaro a duniya wata babbar alama ce da ta bayyana aniyarsa ta nuna iko kan tsarin tsaron yankin.
Sai kuma yarjejeniyar da China ta kulla tsakanin Saudiyya da Iran, wanda ta yi matukar tasiri a harkokin duniya baki daya, lamarin da ya nuna irin karfin diflomasiyyar China da ke dada karuwa.
Abun da ke dada daukar hankali shi ne yadda Amurka ke daukar kasashen yakin Tekun Fasha a matsayin matattara ta masu arzikin fetur, wanda a hankali ta fara janyewa saboda samun 'yancin kai da take samu a fannin makamashi.
Ko da yake, wannan hasashe ba shi da wata ma'ana saboda har yanzu yankin na Gulf na da mahimmanci ba kawai ta fuskar samar da makamashi ba har ma a matsayinsa na zama tsakiyar hanyar zuwa kasuwanci.
Don haka, ya zama wajibi a yi duba kan wannan mataki na janyewar Amurka daga yankin. Kila da akwai yiwuwar Washington ta yi kokarin jan Beijing cikin wani tarko ne.
Shekaru da dama da suka wuce, shugabannin kasar China sun kaurace wa shiga tsakani a duk wani rikicin soji na kasashen ketare, inda suka gwammaci tattare hankulansu kan batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki.
Don haka, a mahangar Amurka na kawo cikas ga girma da bunkasar China, tana bukatar ita ma ta shiga lamuran da suka shafi tashe-tashen hankula da ake fuskanta wanda ke daukar tsawon lokuta ana yi sannan a kashe makudan kudade.
Haka kuma, yana da muhimmaci a yi la’akari da tasirin China a yakin Gulf da irin ayyukan da take yi.
Tasirinta a kasashen yankin Pacific da Afirka na nuna irin karfin da take da shi wanda ya wuce misali na samun wasu riba.
Yanayin da ya haifar da kalubale wajen samar da tsarin ka’idojin kasa da kasa.
Karfin iko
Wata takardar ra'ayi ta GSI da ma'aikatar harkokin wajen kasar China ta wallafa a bara, ta bayyana ra'ayin Shugaba Xi Jinping wajen tsara ka'idoji ga duniya.
A ire-iren kalamai da aka saba ji - kamar hadin gwiwar yanki da kasa da kasa da batun zaman lafiya da tattaunawa a tsakani da mutunta 'yancin kai - duniyar Jinping dai ba ta ba da wata dama ba wajen nuna ikon Amurka.
Ba da fifiko ga ci gaban tattalin arziki, wata dabara ce da China ke amfani a kusan duk wata ganawa da za ta yi na diflomasiya.
Sannan, a hankali take nuna ikonta na karfin tattalin arziki ga duniya, kamar misalin da ta bayar wajen bude cibiyar farko ta Confucius a Riyadh a makon da ya gabata.
A shekarun da suka gabata, China ta zama babbar abokiyar kasashen yankin Gulf, inda ta rage fitar da mai daga yankin zuwa Amurka.
Ta fadada hanyoyin sadarwarta ta BRI, China ta kulla alaka iri daban-daban da kowace kasa a yankin, tare da yin taka tsan-tsan wajen nuna bangaranci da hadin kai.
China dai ta yi kokari wajen rike matsayinta a yakin Gulf da Iran.
Dangantakar tattalin arziki da ke tsakani ta matukar rage yawan damuwar da ake da ita kan tasirin matsalar tsaro da dabarun sayar da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami da jiragen sama.
Ta kuma rage damuwa kan yawan maganganu da ake yi kan Falasdinu duk manuniya ce da ta bayyana an shiga tsaka mai wuya fiye da mai da hankali kan duk wasu hada-hada na kudi.
A gefe guda kuma, wadanda ke ganin manufar Amurka a yankin a matsayin wata dama ta neman fetur ce kawai, sun kasa fahimtar cewa har yanzu Amurka na ci gaba da zama babbar aminiyar Isra'ila ta fuskar tsaro.
Wannan batu na janyewar Amurkawa da kuma kasancewar China a yankin, ya sa wasu na hasashe game da yadda hauhawar kudin ‘petroyuan’ na China ya maye gurbin karfin da kudin dalar Amurka ke da shi.
Amurka da Yakunan
Fahimtar wannan dabara ba ta da wuya. A baya Amurka ta zama kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a duniya, yanzu ta fahimci cewa ba za ta iya kasancewa a wannan matsayin ba ganin tana da abokan hamayya a duniya.
Duk da cewa China na sane da wannan mataki, tana amfani da wasu ayyuka da take yi duk da cewa ba ta da wasu dabaru ko shiri na kalubalantar tsarin sha'anin tsaro a yankunan, fannin da ke samar gagarumin riba ga Amurka.
Akasin haka, Washington na son yaudararta wajen shiga cikin rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Idan ta yi nasarar yin haka, China za ta gane cewa, ba za ta iya yin komai ba a fannin da ya shafi samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yanayin da suka fi daukar hankali a yankin da ke cike da tashe-tashen hankula.
Sannan cigaba da gina wani sansani kusa da tashar jiragen ruwan Khalifa da ke Abu Dhabi bai saba wa manufofin harkokin wajen Amurka ba.
A maimakon haka, tana da burin tasa keyar China shiga cikin rikicin da ya mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.
China dai tana sane da rashin shirinta a wannan fanni. Don haka, shi yasa take taka tsan-tsan, wajen daukar matakai da ketare iyaka.
Kasancewar Saudiyya a matsayin daya daga cikin abokiyar huldar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da taron kasuwancin kasashen Larabawa da China da ake shirin yi nan gaba, ya zama babban mataki da ke cigaba da haifar da damuwa ga Washington.
Yunkurin Saudiyya ga samun sauyi ta fuskar tattalin arziki, za a iya cewa wata mafita ce ga kasuwancin duniya musamman a tsarin samun wasu kasashe da ke da karfin tattalin arzikin kasa a duniya.
Ko da yake har yanzu dai ba a san takamaimai inda neman iko na yankin Gulf din zai je ba, amma ana iya cewa da sauran rina a kaba ga China wajen kafa kanta a matsayin wata madafa mai inganci.
Masu sharhi na ganin Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman Al Saud, MBS - yana kokarin samar da wata kafa ko yanayi da zai tunkari manyan kasashen yankin biyu, kamar yadda Amurka ta jawo China cikin yankin.
Akwai dalilai masu kyau da za a iya yin duba kansu wadanda ke nuna matakin mai cike da hadari a matsayin rashin hikima.
Ban da haka kuma, yadda China ta dauki batun Falasdinu da batun samar da maslaha tsakanin kasashe biyu ba wani abun a zo a gani ba ne.
Amma idan China ta ci gaba da inganta huldar da za a iya cewa za ta inganta tasirin Teheran a yankin - da ka zama babban jigo a Syria da Lebanon da Yemen da kuma Iraki - zai iya zarce duk mataki na juriya ga Washington sannan ya sauya alkiblar Amurka ta inda za ta kasa kai wa matsayin Beijing.