Daga Camille Sari
A kasar Morocco, wadda take fuskantar sauye-sauye na tattalin arziki tun 1983, ana ta kira kamfanoni su koma hannun ‘yan kasuwa da kuma rage kashe kudin batul mali.
Duk da haka, kasar na daga cikin kasashen da Shirin Ci-gaba na Majalisar Dinkin Duniya ya saka a matsayin kasar da jama’a ke samun ci-gaba.
Akwai abubuwa da dama da ke taimaka wa ci-gaban Morocco da suka hada da karuwar samun ilimi da kara saka mutane a makarantu a kauyuka da kara gyara hanyoyin kasar, da tashar ruwa da kuma jirgin kasa da sauran ababen more rayuwa.
Samar da tsarin kiwon lafiya a kauyuka da birane da kuma inshorar lafiya ya kara kuzarin ma’aikatan na Morocco.
Bugu da kari, tsarin fitar da kayayyaki na kasar Morocco, da kuma kara habaka cinikayya tsakanin kasa da kasa, na taimakawa wurin kara bude kasuwar kasar a duniya.
Kasar tana amfana cikin gida da waje – daga tsare-tsarenta. Kasar ta dogara ne da wasu kamfanonin waje da suka hada da masaku da na fata da na fitar da tumatiri kuma ana cimma hakan ne ta hanyar habaka kamfanonin.
Wannan na samar wa kasar ta Arewacin Afirka kudaden shiga daga kasar waje. Bayan samun ‘yancin kanta, tattalin arzikin Morocco ya mayar da hankali ne ta gina madatsun ruwa da habaka noma domin dogara da kai da kuma fitarwa waje.
Sai dai tun da aka shiga shekarun 2000, an samu karin masu zuba jari daga kasashen waje ciki har da kamfanonin kera mota.
Burin ci-gaba ta tsare-tsare
A hankali, gwamnatin kasar ta ci gaba da daukar matakai da suka hada da samar da yankin masana’antu, da yin sabbin dokokin zuba jari da bayar da gudunmawa ga masu fitar da kaya, da taimaka wa kamfanonin fitar da kaya.
An samu karuwar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje daga kashi 15 zuwa 35 cikin 100, kamar yadda wani rahoto na ofishin jakadancin Faransa ya bayyana.
Damar da kasa ke da ita ta gogayya da sauran kasashe da ‘yan kasar a kasuwar duniya ta danganta da irin ci-gaban samar da kayayyaki da kasa take da su, da bayar da horo kan ayyuka da yaki da jahilci da kuma karfafa gwiwa wurin bincike da kawo ci-gaba.
A Morocco, akasarin kamfanonin sun mamaye wuri mai yawa a yanki da kuma kasar waje, duka a kudancin Afirka da arewa a Kasashen Tarayyar Turai.
Kanana da matsakaitan kamfanoni na Morocco sun shirya tsaf domin fuskantar kamfanonin waje wadanda suke sayar da kayayyaki a cikin gida da kuma fitar da su, da kuma samar da kamfanoni wadanda za su yi jagoranci.
Kara bunkasa fitar da kayayyaki
Kara tattara kudin da ake bukata domin zuba jari da shiga kasuwancin da kuma kawo sauye-sauye ya soma asali ne daga irin sabbin tsare-tsaren da bangarorin banki da kudi suka kawo.
Sun hada kai da bankunan kasashen waje domin habaka masana’antu inganta yanayin biyan kudi da kuma ci gaban hada-hadar banki da kuma tsarin bayar da bashi da zai taimaki masana’antu.
Akwai bukatar rarraba kafa a tattalin arzikin Morocco kafin kamfanoni masu zaman kansu na kasar su taka rawar gani ta bangaren ci gaba.
A ‘yan shekarun da suka gabata, Morocco ta samu ci gaba da bangarori da dama ciki har da karin kashi 7 cikin 100 na sabbin sana’o’i a duk shekara inda kuma adadin karuwar ayyukan yi ya karu da kashi 6.7 a duk shekara haka kuma akasamu karin albashi da kashi 13 cikin a duk shekara.
Kamar yadda rahoton IMF na 2022 na duk shekara ya nuna kan Morocco, kayayyakin da kamfanoni suke sayarwa ya karu da kashi13.5 cikin 100 a duk shekara inda zuba jari daga kasashen waje a masana’antu ya karu daga kashi 28 cikin 100 a 1990 zuwa 35 cikin 100 a 2010 da 2020.
Karuwar da aka samu na kudaden da masana’antu ke samarwa a duk shekara yana da alaka da masu zuba jari daga waje, da kuma yadda aka samu sauye-sauye a bangaren.
Kamfanonin da ke sarrafa kayayyaki na ci gaba da mayar da hankali kan kayan abinci wadanda su ne kashi 50 cikin 100 na abin da ake samarwa inda kuma sauran kayayyaki suna da sama da kashi 22 kamar yadda rahoton duk shekara na bankin Al Maghrib ya nuna.
Akasarin kayayyakin da ake samarwa a kamfanoni ana sarrafa su da kyau. Rahoton ya bayyana cewa a 2022, kayayyakin da Moroccon ke fitarwa ya kai biliyan €22 bayan karin da aka samu na biliyan €6.272 kan adadin a 2022.
Rahoton ya kuma ce kayayyakin da aka sarrafa rabi da rabi su ne kan gaba a jerin abubuwan da Morocco ke fitarwa inda suke samar da euro biliyan 63.88, inda aka samu karin euro biliyan 2.631 idan aka kwatanta da irin lokacin a 2021.
Kalubale
Kayayyakin da aka kammala sarrafawa domin amfani su ne na biyu daga cikin kayayyakin da Morocco ke fitarwa, inda jimillarsu ta kai euro biliyan 61.
Motocin fasinja kadai sun kai ninki biyu na kayayyakin abincin da kasar ke fitarwa da suka kai euro biliyan 2.52.
Na uku daga cikin kayan da ake fitarwa su ne kayayyakin da aka kammala na masana’antu da suka kai euro biliyan 3.59.
Wadannan sun hada da wayoyi na wutar lantarki. Kayayyakin abinci su ne suka zo na hudu inda kayayyakin da ake fitarwa a watanni shida na farko na shekarar suka kai biliyan euro 3.47 da suka hada da abincin ruwa da kifaye da tumatir da busassun kayan itatuwa, kamar yadda wani rahoton bankin duniya ya bayyana.
Akwai kalubale da ke fuskantar tattalin arzikin Morocco da cikin kasar da kuma waje. Wadannan sun hada da dogaro kan kayayyakin aiki da kuma nuna wariya ga kayayyakin Morocco wadanda za a kai Turai.
Wata matsala kuma ita ce kudin da ake kashewa wurin sarrafa kayayyaki a Gabashin Turai da Asia sun fi sauki.
Morocco na fuskantar sabuwar gasa a wuraren da tun can take da karfi da dama kamar bangaren masaku.
Duk da cewa tana samun matukar ci gaba, akwai bukatar ta fuskanci wadannan kalubalen da kuma kokarin magance su domin ci gaba da a tafiya a daidai.
Marubuciyar Camille Sari, farfesa ce a Sashen Koyar da Tattalin Arziki a Jami’ar Sorbonne da ke Paris.
Togaciya: Wannan makalar ra'ayi da fahimtar marubucin ne, amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT ba ne.