Daga Aliyu Usman Tilde
Idan har a zamanin mulkin Abasiyya na karni na 9 za a yi tunkaho da fitaccen mawakin baka, Abu Tammam, Afirka ma za ta iya yin tunkaho da Abubakar Ladan Maccido.
Kamar Abu Tammam, daga cikin gwagwarmayar Abubakar Ladan akwai "zagaya kowane bangare na duniya ko neman sanin kowane bangare."
Tafiye-tafiyensa a tsakanin nahiyar Afirka - a matsayinsa na mawakin baka - sun kai shi zuwa ga dukkan kasashen Afirka, ban da takwas.
Lokacin da aka gano shi a wani yanki na Gabashin Afirka aka bukaci ya koma gida, ya riga ya samo dukkan bayanan da yake bukata game da nahiyar domin tsara kundin wakoki hudu masu tsayi, wadanda suka sa ya zamo mawakin Tarayyar Afirka.
Abubakar, wanda aka haife shi a birnin Zaria na Arewacin Najeriya a shekarar 1935, ba mutum ne da ke son zama wuri daya ba kamar mahaifinsa, wanda Bafulatani ne.
Ya yi aiki a Kamfanin Tarayyar Afirka a Kano tsawon shekara biyu bayan ya kammala sakandarensa kuma daga bisani ya tsallaka zuwa Nijar don kai ziyara.
Ba da dadewa ba kuma ya sake fita ta hanyar Nijar, inda ya kwashe shekaru bai dawo ba.
In ban da kasar Masar ta Gamal Abdel Nasser da ya zauna kusan shekara 10, inda a can ne ya karasa baitocin wakarsa ta -Al'ajubban Masar- Abubakar Ladan bai taba zama wuri daya ya kwashe tsawon lokaci ba.
Ya zagaye kasashe da dama, inda yake zantawa da mutanen kasar sannan ya fahimci mutanenta da rayuwarsu da shugabanninsu.
Gudunmawarsa ga ilimi
Abubakar Ladan ya gana da daruruwan sarakuna, inda ya rera wa da yawa daga cikinsu baitoci, yayin da su kuma suke ba shi ihsani da yake amfani da shi domin guzuri zuwa wani gari ko kasa ta gaba.
Ya samu kusanci matuka da Nasser, sannan ya gana sosai da jiga-jigan masu wakar baka na kasar Masar.
Da aka fara kiraye-kirayen hadin kan Afirka, musamman a shekarun 1960, sai Abubakar Ladan ya zama jigo a nahiyar.
Masanin bai yi wata-wata ba ya kasance a sahun gaba. Shi ne ya rera waka mafi dadi a game da kishin kasa da hadin kan nahiyar da Hausa; harshen da aka fi amfani da shi a Yamma da Tsakiyar Afirka.
An nadi baitocin wakar ne da muryarsa ta maza mai matukar dadi a gidajen rediyo da dama, ciki har da Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a shekarun 1960.
Wasu lokutan Abubakar Ladan yakan jefa Larabci a wakokinsa, abin da ke nufin ya iya Larabci da kara tabbatar da saninsa na nahiyar ta Afirka.
Tuni wakokin suka zama ababen nazarta a jami'o'i da kwalejoji, musamman a tsangayun koyon zama malamai.
Miliyoyin mutane sun haddace wakokinsa, sannan sun taimaka wajen karfafa gwiwar wasu su zama mawakan baka.
Fitacciyar wakar Abubakar Ladan ta hadin kan Afirka-Yarda da Abota, Soyayya- waka ce da ta bayyana irin burin nahiyar Afirka bayan mulkin mallaka da kuma muradun Kungiyar Tarayyar Afirka, wadda a wajensa ita ce hanyar cimma nasara.
Kaunar Afirka
Kungiyar Tarayyar Afirka, kungiya ce da William Wilberforce, wanda Abubakar Ladan ya rera wa baitoci hudu na yabo saboda yaki da kasuwancin bayi da ya yi, zai so a ce shi ya kafa tare da gwagwarmayar ganin samun nasararta.
An kafa Kungiyar Tarayyar Afirka ce a shekarar 1963, shekara 80 bayan mutuwar Wilberforce, wanda a lokacin alhakin tabbatar da nasararta ya ta'allaka a kan shugabannin kasashen Afirka.
Soyayyar Abubakar ga Afirka ta sa ya tuntubi dukkan shugabannin Afirka a shekarar 1969, inda ya roki su tabbatar da dorewar kungiyar.
Burinsa na ci gaban nahiyar ya ta'allaka ne a kan kokarin hada kan yankin da kokarin hada kafada da sauran kasashe ta hanyar yaki da talauci, da jahilci da kishin kasa da shugabanci mai kyau.
A game da tsarin shugabanci mai kyau, ya rubuta cewa:
Zamanmu da ku dai ya kare
Daimon da kuzanmu da zinare
Komai mun kwace mun tare
Ba sa son wai su ga mun more
Yau sun dage su ga mun dare.
Duk da cewa Afirka tana dogaro da kanta ne lokacin da aka kafa Kungiyar Tarayyar Afirka, tun a lokacin Abubakar Ladan ya yi hasashen cewa hadin kai ne kawai zai kawo ci-gaba. A cewarsa:
Turawan mulki sun tashi
Mun kakkabe hannu ba bashi
Su ne Afirka muke kishi
Hada kai ne yau mai kaushe shi
An samu hadadden harsashi
Saura a Mozambique da Angola
Da Guinea sun saura cikin wahala
Hada kai ne babbar bulala
Wallahi da zaran mun tsala
Duka sauran za ka ga sun lula
A baya can, ana ganin samun 'yancin kasashen Rhodesia (Zimbabwe a yanzu) da Namibia da Afirka ta Kudu zai gagara.
Amma Abubakar Ladan ya yi hangen nesan cewa hadin kai ne kawai zai taimaka wajen cika muradun Kungiyar Tarayyar Afirka.
Kan kauna ya tsayu ba kishi
Daga baya abota zai bi shi
Daga zaran ga abu ya tashi
An shawarta bisa karshe shi
Koko a tsaya kan samo shi
Hada kai ne babban harsashi
A baitoci da dama, shaukinsa na hadin kan Afirka ba ya boyuwa. Wannan ya bayyana burinsa ne na ganin an hada kasashen ta hanyar barin shiga da fice a tsakaninsu:
A aminta Afirka da hanyoyi
A yi yawo ba wani juyayi
Daga Asmara har ya zuwa Kayi
Daga Khartoum har Mauritania
Bayan kusan shekara 50, inda kasashe da dama suka samu 'yancin kai, an fara samun hadin kan nahiyar ta hanyar kudin bai-daya da manyan tituna masu hada kasashe, da bizar kyauta da shaidar shiga kasa ta bai-daya da sauransu.
Kalubalen da ya fuskanta
Duk da cewa yabon shugabanni yake yi, kamar duk wani mawaki makamancinsa, Abubakar Ladan bai damu da wadanda suke yi wa muradun Kungiyar Tarayyar Afirka na samar da zaman lafiya da hadin kai zagon kasa ba.
Ya fuskanci kalubale ta fannin kasashen waje da wasu shugabanni masu son rai.
Abubakar Ladan yana sane da masu katsalandan din daga kasashen musamman "wadanda suke karbar makudan kudade" domin haddasa rikici, inda ya rika nanata bukatar da ke akwai wajen mayar wa wadannan masu zagon kasan da aniyarsu:
Fitina barci take ba ta fita
Allah wadaran mai tado ta
Da wadanda suke dada jawo ta
Haka nan da wadanda ka kawo ta
Allah ka tsare mu da tashinta
Abubakar Ladan ya yi tsawon rayuwa inda ya gane wa idonsa ci-gaba da kalubalen da Afirka ta rika fuskanta a kusan shekara 50 bayan baitocinsa.
Duk da cewa an gina dubban makarantu da asibitoci da hanyoyi, nahiyar na fama kalubale da dama.
Duk kuma kokarin da shuganninta suke yi, har yanzu an kasa magance matsalar talauci musamman duba da yadda ake ci gaba da samun karuwar mutane a yankin.
Ya bar wa Afirka wani abu da ya bayyana burinsa game da yankin, wanda wannan abun shi ne waka da za ta cigaba da zaburar da shugabannin yankin wajen hadin kai da neman 'yanci.
Abubakar Ladan ya yi rayuwa cikin kankan da kansa duk kuwa da daukakar da ya samu.
A lokacin da na ziyarce shi a 24 ga Disamban 2014, na same shi yana cikin matsananciyar rashin lafiya, amma duk da haka kwakwalwarsa tana iya tunawa da karasa baitocinsa idan an jawo su.
Lura da cewa ba zai rayu mai tsawo ba daga lokacin saboda yanayin tsufa, sai na ji shaukin in dora daga inda ya tsaya.
Amma aiki ne babba. Allah Ya jikan Abubakar Ladan. Allah Ya sa Afirka ta ci gaba da samun hadin kai da daukaka.
Marubucin, Aliyu Usman Tilde, mai sharhi ne a kan harkokin yau da kullum, kuma aboki ga marigayi Abubakar Ladan.
Togaciya: Wannan rubutu ra'ayi ne na marubuci, kuma hakan ba ya nufin ya zo daidai da na kafar TRT Afirka ba.