Sharar robobi da ledoji: Wata babbar matsala da ya kamata a magance tun yanzu

Sharar robobi da ledoji: Wata babbar matsala da ya kamata a magance tun yanzu

Roba ta ci gaba da kasance babbar matsalar duniya wadda ke gurbata kasa da ruwa da kuma iska.
Ana tara kimanin tan miliyan 300 na roba da ta zama shara a fadin duniya a kowace shekara. Hoto: James Wakibia

Daga James Wakibia

Roba tana da dadin amfani amma kuma tana jawo babbar matsala ga muhalli - Ana ci gaba da samun kiraye-kirayen kan wannan matsala.

Shin duniya za ta iya magance wannan matsala da roba ke jawowa?

Lokacin da na fara gangamin kan yadda za a rage amfani da jakar leda wacce suke yi sau daya, kimanin shekara 10 da suka wuce, a wancan lokacin mutane kadan ne suke magana kan matsalar, ba kamar yanzu ba.

Na ga yadda abubuwa suke kara tabarbarewa kuma ina fatan za mu hada hannu wuri guda wajen magance matsalar. Hankalina yana tashi idan na ga robobi da ledoji a magudanar ruwa da kan tituna da kan rassan bishiyoyi.

Jakunkunan leda a ko ina. Mun ga hotuna da bidiyo a kafafen sada zumunta, inda tsuntsaye da kunkuru da sauran dabbobi suke fuskantar matsala daga robobi ko su mutu bayan sun ci roba ko leda.

Yanzu ana samun roba da leda a kowace kusurwa a duniyarmu. A cikin tekunanmu da kasa da ruwan sha kai hatta cikin jinin jikinmu.

Barnar da roba da leda ke jawowa babba ce musamman a kasashe kamar Kenya. Hoto: James Wakibia

A fadin duniya, ana tara sharar roba da leda da ta kai nauyin tan miliyan 300 a kowace shekara, kuma da yawa daga ciki tana komawa karkashin kasa ne ko cikin kogi da kuma sauran muhallinmu.

Akwai jan aiki a gaba

Matsalolin suna da tayar da hankali, akwai fiye da tan miliyan 8 na robobi da leda da ke shiga cikin teku a kowace shekara, wannan yana jawo matsala ga dabbobin ruwa da kuma duka sauran halittu.

A tsawon shekara 10 da na yi na wayar da kan jama'a kan hadarin mafani da roba, zan iya cewa kusan na ga komai.

Na wallafa munanan hotunan barnar da roba da leda suka yi a fadin duniya don mutane su ga irin girmar matsalar da fatan cewa ta haka ne za a fara tattaunawa kan yadda za a fara daukar mataki. Sai dai abin takaici yawancin mutane ba su damu da matsalar ba.

Duk da alkaluma suna ci gaba da nuna girmar matsalar, wanda hakan yake nuna bukatar daukar mataki cikin gaggawa don yaki da matsalar, sai dai a bayyane yake kokarin da daidaikun mutane suke da wayar da kadai ba za su iya magance matsalar ba.

Wani dan Nijeriya yana narkar da roba don yin bullo. Hoto: AA

Akwai bukatar samar da canji da kuma hadin gwiwa don magance wannan matsala da ta karade ko ina.

Sai dai maganar gaskiya bai kamata a yi wasa da yarjejeniyar da aka kulla a kan robobi da leda ta birnin Paris a kasar Faransa ba. Wannan abu ne da ya sani farin ciki.

Muna da babbar dama don mu tabbatar cewa mun kawo karshen gurbatar muhalli da roba ke jawowa, tafiyar za ta iya kasancewa mai nisa kuma mai wahala, amma an riga an fara, kuma kamar yadda ake fada tafiyar mil dubu da sahu daya ake fara ta.

Matsalar robobi da ledoji matsala ce mai wuyar sha'ani duk da cewa an fara ayyukan sake sarrafa sharar roba. Hoto: AA

A wani sabon rahoto na hukumar da ke kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), kasashe suna hanyoyin da za su iya rage gurbatar muhalli da robobi ke jawowa da kaso 80 cikin 100 nan da shekarar 2040 ta hanyar kawo hanyoyin sake amfani da roba ko leda fiye da sau daya da fito da hanyar sarrafa sharar roba zuwa wasu abubuwa da kirkiro wasu abubuwan da za su maye gurbin roba wadanda ba sa gurbata muhalli da sauransu.

Roba a cikin huhu

Ana da tabbacin cewa shirin bayar da lada ga wanda ya kawo sharar roba zai taimaka sosai wajen rage gurbacewar muhallin da roba ke jawowa idan aka fara shi.

Fatana shi ne mu yi nasarar magance matsalar cikin lokaci, muna da burin haka nan da shekara 10. Kodayake, James ne yake maganarsa.

Ba na cikin wakilan kwamitin da gwamnati ta kafa na (INC), amma ina da yakinin akwai hazikan mutane maza da mata daga ko ina a duniya da muke magana da murya daya wadanda kuma za su yi duk abin da ke yiwuwa wajen kawo canji.

Iya yawan robobi da ledojin da ake samarwa, iya yawan yadda suke taruwa da kuma haddasa gurbatar muhalli. Masana'antu suna kona mai don samar da robobi masu yawa.

Bari fayyace komai, sun nunnunka yawan robobin da suke samarwa. Misali kamfanin Coca Cola, ya ce yana samar da robobi tan miliyan 3 kowace shekara wanda hakan yake nufin cewa a duk minti daya ana samar da kwalaben robobi guda 200,000, tab di jam!

Abin takaicin shi ne wadannan kamafanoni suna samar da shara mai yawa da duniya ba za ta iya da ita ba, abu ne da ke jiran wani kankanin lokaci kafin ya zama wata babbar matsala kuma wajibi ne sai mun yi wani abu!

Akwai lokutan da jakunkunan leda suke jawo mutuwar dabbobi. Hoto: James Wakibia

Sharar robobi ta zama wani bangare na rayuwarmu. Wani bincike na baya-bayan nan ya bayyana cewa akwai robobi a jininmu da kuma can cikin huhunmu wanda hakan yake nuna yiwuwar samun matsala ga lafiya.

Yayin da adadin masu cutar kansa ke karuwa ba tare da sanin dalili ba, yana muhimmanci a san ko roba tana da tasiri kan lafiyarmu.

Kasashe da ke yankin kudancin duniya su ne wadanda matsalar gurbatar muhalli da roba ke jawowa ya fi shafa kuma da yadda muka kasa magance matsalar sarrafa shara, ganin cewa ba mu da na'u'rorin sake sarrafa shara mai tarin yawa wacce take karewa a karkashin kasa.

Kasashen da suka ci gaba su daina turo shararsu kasashe masu tasowa wadanda ba su da hanyoyin da za su iya tafiyar da su. Ya kamata kowace kasa ta iya tafiyar da shararta.

Aiki da yarjejeniya

A shekarar 2020, Kungiyar Masana Ilimin Sinadarai ta Amurka ta yi yunkurin sa Kenya ta sassauta tsauraren dokokinta kan robobi a kokarinta na cika kasar da sharar robobi yayin da mu kanmu muke fama da ita sharar robobi da leda da ke karkashin kasa a duk fadin kasar Kenya.

Matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa ita ce ta yadda rarraba shara, wanda hakan ke sanya alamar tambaya kan ko ana samun riba.

Bincike-binciken da aka gudanar ya nuna cewa kasa da kaso 10 cikin 100 na robobi da ledojin da aka samar a duniya ne ake kara sarrafa su zuwa wasu abubuwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashe za su rage gurbatar muhalli da robobi ke jawo da kaso 80 cikin 100 nan da shekarar 2040. Hoto: James Wakibia

Mafi yawan adadin yana karewa ne a karkashin kasa da muhalli inda ake konawa ko kuma a bar ta ta gurbata muhalli.

Robobi da leda suna da wasu sinadarai masu cutarwa wadanda a duk lokacin da aka kona su, sinadaran suna shiga cikin iska kuma jawo matsala ga lafiyar dan Adam. Duk ta hanyar da ka kalli abin, robobi ko leda suna da matsala ta kowace fuska.

Kwanan nan, na kalubalanci kaina inda na ce bari na shiga kogi wanda aka gurbata ruwansa da robobi da ledoji don na gani kamar guda nawa zan tsinto. Na sawa kaina tsawon sa'a daya domin na tsinto robobin da za a iya sake sarrafa su.

Bayan lokaci maj tsawo, na yi nasarar tsinto akalla kwalaben roba 700 wadanda na sayar a kan kankanin kudi Ksh na 100. Wannan bai kai dala daya ba.

Dole ne yarjejeniyar kan robobi da ledoji su dakatar gurbatar muhalli. Idan ana so a samu haka, to sai a mayar da shi doka wato hana amfani da roba ko leda sau daya, sannan a ware kudi don gyara muhallin da aka bata da kuma ya kamata a taimakawa kasashe da ke kudancin duniya da ke fama da gurbatar muhalli.

Abu mafi muhimmanci shi ne, kasashe da ke arewacin duniya su daina tura wa kasashe matalauta sharar robobinsu. Ya kamata ya zama doka cewa haramun ne ka tura wa wata kasa sharar robobinka.

Marubucin, James Wakibia, mai rajin kare muhalli ne a kasar Kenya.

A lura: Wannan makalar ra'ayi da fahimtar marubucin ne, amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT ba ne.

TRT Afrika