Daga Jakkie Cilliers
Idan aka kwatanta tarihin nahiyar Afirka bayan samun ‘yancin kai da kuma na sauran yankuna, a bayyane take cewa an bar nahiyar a baya a fannoni da dama ta bangaren ci-gaba, kamar yadda ya nuna a taswirar matsakaicin darajar kayayyakin da nahiyar ke samarwa a duk shekara.
Taswirar ta nuna bayanai har zuwa 2023 da kuma hasashen bayanai har zuwa 2043, inda aka saka tasirin da annobar korona ta yi a shekarun 2020/2021.
Ana samun ci gaba a Afirka amma kuma ana samun tafiyar hawainiya.
Akwai kananan kasashe da tattalin arzikinsu ke habaka cikin sauri.
Akwai duk hujjoji da za su sa a damu kan tasirin wannan bambanci a siyasance da kuma sauran bangarori.
Sai dai akwai kuma wasu wurare da suka nuna batun ci gaba da aka samu ta bangaren rayuwar dan adam da suka hada da tsawon rayuwa da kuma mutuwar kananan yara.
Karuwar tattalin arziki
Abubuwan da ke faruwa yanzu da suka hada da samar da kyakkyawar gwamnati da ribar da ake samu ta bangaren noma da kuma aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci maras shinge – duk suna nuna ci gaban Afirka a idon duniya.
A 2022, ma’aunin tattalin arziki na GDP ko kuma darajar kayayyakin da Afirka ke samarwa a shekara ya kai dala 4,955.
A hanyar da ake kai ta ci gaba, ana sa ran zai kai dala 7,157 a 2043, wanda a shekarar ne za a kawo karshen aiwatar da shirin Kungiyar Tarayyar Afirka na shekara 13 kan ci gaban nahiyar. Idan aka hada ta fuskoki biyu, ma’aunin na GDP zai iya karuwa da kashi 54 cikin 100.
A maimakon tattalin arzikin Afirka na dala tiriliyan 3.2 a 2022 wanda zai karu zuwa dala tiriliyan 8.7 a 2043, akwai yiwuwar tattalin arzikin na Afirka ya kai dala tiriliyan 15.2.
Wadannan bambance-bambance ne masu dimbin yawa kuma suna nuni da bunkasar Afirka.
An yi hasashen ne kan yadda za a bunkasa duniya (kawo ci gaba mai dorewa a duniya) wanda zai yi matukar amfani ga ci gaban Afirka.
Sakamakon karuwar fargabar da ake samu tsakanin Kasashen Yammaci da kasar China, kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine da kuma sauran ci gaba, aikin ya fito da wasu mau’du’ai da suka fito da tasirin hakan kan ci gaban Afirka ta bangarori daban-daban.
An fito da hanyoyi uku da za a kalli Afirka a duniya wadanda suka hada da: Rarrabuwar duniya da duniya na cikin yaki da kuma ci gaban duniya.
Ta bangaren duniya na cikin yaki zai kasance lamari mafi muni ga kowa sakamakon babu wani ci gaba ga kowa.
Ta bangaren ci gaban duniya kuwa hakan zai kai ga samun sakamako mai kyau ta bangaren tattalin arziki amma kuma hakan na tattare da illolin da suka shafi gurbata muhalli wanda hakan kuma zai kai ga matsalolin sauyin yanayi.
Bayan an gudanar da taruka masu yawa na kara wa juna sani, sakamakon tarukan ya nuna an fi kallon duniya kan tana cikin halin rarrabuwa.
Raba Afirka gida-gida
Girman tattalin arzikin Afirka, da ma’auninta na GDP da kuma matakin talauci duk sun sha bamban ta bangarori hudu.
Wannan taswirar na nuna jimlar tattalin arzikin Afirka a 2019 da kuma yadda ake hasashensa a 2043.
Yana nuna irin alfanun ci gaban tattalin arziki ga Afirka a tsarin ci gaba mai dorewa na duniya.
Duk da yawan jama’a da nahiyar take da shi, Afirka har yanzu karama ce ta bangaren gogayya da sauran nahiyoyi ta bangaren tattalin arziki.
An daga darajarta, a wasu lokuta saboda gasa tsakanin kasashen Gabas da Yamma, da kuma rawar da take takawa wurin samar da albarkatun mai, da kuma a lokutan yaki da ta’addanci da kuma mayar da hankali kan muradun karni da kuma ci gaba mai dorewa.
A baya-bayan nan, nahiyar Afirka ta zama wani wuri na gasa tsakanin kasashen Yamma da China da Rasha da kuma gasa da ake yi kan albarkatun kasa da kuma kara kaimi zuwa sauyi zuwa sabbin hanyoyin masana’antu karo na hudu.
Domin samar da duniya wadda za a samu ci gaba mai dorewa, akwai bukatar kawo karshen zaman fargaba tsakanin Amurka da China da kuma fito da sabbin tsare-tsare wadanda za su hada kan China da Amurka da Tarayyar Turai da kuma ganin ci gaban Kudancin Duniya.
Halin da ake ciki na rabuwar kan duniya na kawo cikas wurin ci gaban nahiyar Afirka. Idan aka kwatanta da kallon duniya ta bangaren ci gaba mai dorewa, duniya wadda kanta ya rabu na samar da karin hayaki mai gurbata muhalli wanda kuma ke kaiwa ga samun sauyin yanayi cikin sauri.
Duk da haka, sai an samu ci gaba matuka ta bangaren tattalin arziki da siyasa a Afirka gami da samun tattalin arziki mai dorewa cikin sauri sa’annan nahiyar za ta kara samun murya wurin tafiyar da harkokin duniya.
Marubucin, Jakkie Cilliers, shi ne shugaban African Futures and Innovation da ke nazarin makomar Afirka a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Pretoria.
Togaciya: Ra’ayin da marubucin ya bayyana ba lallai shi ne ra’ayi ko mahanga ta TRT Afrika ba.