Wajibi ne daftarin karatu ya dace da abubuwan da ƙarni na 21st ke buƙata. Hoto: AP      

Daga Nana Dwomoh-Doyen Benjamin

Afirka tana kan wata muhimmiyar gaɓa a harkokinta na ilimi. Duk da gagarumin cigaba da aka samu wajen ƙaruwar samar da ilimi da ilimantarwa, manhajar karatu ta Afrika, ta fi la'akari da abubuwan da suka shuɗe, da ba za su iya bai wa ɗalibai ƙwarewar da ta dace da duniyarmu ta yau mai saurin canjawa ba.

Taken Tarayyar Afrika na shekarar 2024: "A bai wa ɗan Afirka irin ilimin da zai dace ƙarni na 21st", ya yi yunƙurin shawo kan wannan gaggautacciyar matsalar ta hanyar bayar da shawarar a samar da tsare-tsaren karatu masu inganci, sha-kundum kuma na zamani.

A shekarar 2024, na samu damar halartar jerin tarurrukan tuntuɓar juna waɗanda Hukumar Kula da Tattalin Arziƙi, Zamantakewa da Al'adu ta Tarayyar Afrika (ECOSOCC) ta shirya.

Waɗannan tarurrukan sun haɗo kan ƙungiyoyin fararen hula, da ƙwararru a harkar ilimi da kuma masu shata manufofi waje guda, domin su tattauna kan buƙatar gaggawa da ake da ita, ta sauya fasalin manhajar karatu a Afrika.

Matsayar da aka cim ma a bayyane take: Wajibi ne manhajar karatunmu ta dace da tunani mai zurfi, da azanci, da kuma fasahohi na zahiri da suka dace da buƙatun ƙarni na 21st.

Babbar matsalar tsarin ilimin Afrika na yanzu ita ce yana samar da ɗaliban da ba su da cikakkiyar ƙwarewa wajen magance manyan ƙalubalen nahiyar.

Tsawon shekaru,galibin ƙasashen Afrika sun mayar da hankali kan horas da ɗalibai su ci jarrabawa, a maimakon samar da fasahohin da za a yi amfani da su.

A galibin lokaci suna haddace ɗimbin bayanai, su amayar da su yayin jarrabawa, daga bisani kuma su manta galibinsu.

Yawancin ƙasashen Afrika suna bai wa ɗalibai ilimi ne domin su ci jarrabawa, a maimakon su samar da fasahohin da za a yi amfani da su. Hoto: Reuters

Wani ɗalibi zai iya koyan ilmummuka kamar Pi R Squared, da centrifugal force, ko laws of motion, amma bai san yadda ake amfani da waɗannan ƙa'idojin a ilimi na zahiri ba.

Wannan giɓin da ke tsakanin ilimi a rubuce da ilimi a aikace na nufin cewa Afrika na faman shawo kan ƙalubalenta ta hanyar hanyar horaswar da take bai wa ɗalibanta.

Ghana, alal misali, ta ɗauki kyawawan matakai wajen kawa sauyi a harkar karatu.

Sabuwar gwamnatin ta ƙaddamar da Zauren Ilimi na Ƙasa, wata cibiya da aka tsara ta da hadafin tattaunawa mai ma'ana da masu ruwa da tsaki daban daban game da makomar ilimi.

Shirin na da hadafin yi wa manhajar karatu da ake da shi a halin yanzu garam-bawul, domin a gusa daga hadda zalla zuwa wani tsari mafi inganci da ya fi mayar da hankali kan magance matsala da kuma yin ƙirƙira.

Har wa yau, Ruwanda ta fara gudanar da shirye shiryen kawo sauyi a fannin Ilimi. Jami'ar The African Leadership University (ALU) a Ruwanda tana koyar da kwas na musamman a matakin digiri a kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta "Global Challenges", karatu ne haɗe da bincike da ke buƙatar ɗalibai su tsara sannan su aiwatar da masalahohi ga matsalolin duniya na zahiri da nahiyar ke fuskanta.

Wannan mataki na kai-tsaye bai taƙaita ga kyautata sakamakon koyo ba kaɗai, har wa yau, yana yassare wa ɗalibai su zama masu karsashin kawo sauyi a al'umominsu. Amma, waɗannan yunƙurin ɗaiɗaiku ba su wadatar ba.

Wani rahoto daga wajen the Global Partnership for Education ya bayyana cewa zuwa ƙarshen shekarar 2025, ƙasashen Afrika na da hadafin zaftare adadin yaransu da ba sa zuwa makarantar firamare da rabi zuwa kashi 11% sannan su tabbatar da cewa kashi 46% na ɗalibai sun iya karatu sosai kafin su kammala makarantar firamare.

Cim ma wannan babban burin ne ya wajabta buƙatar mayar da hankali kan sauya manhajar karatu a faɗin nahiyar.

Wani jigon sauya manhaja dole ya kasance an haɗe ilimin STEM a aikace (ilimin Kimiya,fasaha,Ƙere-ƙere, lissafi) a faɗin makarantun Afrika.

Bincike sun nuna cewa ɗaliban da aka koya wa ilimin kai tsaye na STEM, ba su taƙaita ga samun ingantaccen ilimin warware matsalolin ba kaɗai, har wa yau, suna samun sauƙin fahimtar sauran madoji kamar lissafi da tunani mai zurfi.

A cewar wani rahoton UNESCO, an alaƙanta koyar da ilimin STEM na bai-ɗaya da samun ƙaruwar ƙwazo a kimiya da lissafi da kashi 30%.

Idan Afrika za ta samar da ɗalibai da za su iya ƙirƙira wa nahiyar da ma gaba, to dole tsarin karatunta ya jiɓanci fuskantar kimiya da fasaha a aikace.

Sauya manhajar karatu ya ƙunshi yin amfani da karatun STEM a aikace a faɗin Afrika. Hoto: AA 

Ƙungiyoyin fararen hula sun taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyin. The African Progressive Research and Innovations LBG.

(APRIL) na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin fararen hula da ke jagorantar fafutikar.

APRIL tana haɗin guiwa tare da cibiyoyin ilimi a faɗin Afrika domin sauya salon koyarwa na gargajiya da ya fi mayar da hankali kan koyarwa don a ci jarrabawa zuwa salon koyarwa da ya mayar da hankali kan raya al'umma.

Shirye-shiryen nasu sun ƙarfafa wa ɗalibai su yi amfani da ilimin karatu da rubutu ya koma ƙalubale a aikace, da ke samar da wani zamani na masu zurfin tunani da masu aiwatarwa da za su bayar da gudummawa a aikace wajen cigaban Afrika.

Muhimmancin koyon karatu a aikace (PBL)ba zai misaltu ba. Bincike ya nuna cewa tsarin PBL yana koyar da bunƙasa tunani mai zurfi da kuma fasahar warware matsaloli tsakanin ɗalibai.

Idan aka rungumi aiki a aikace,masu koyo suna fahimtar darasin da yadda ya kamata idan aka bi hanyar koyon karatu a aikace, ɗalibai na ƙara fahimtar abin da ake koya musu da kuma gudanar da shi a zahiri.

Duk da waɗannan cigaban, akwai sauran rina a kaba.UNESCO ta rawaito cewa Afrika na buƙatar sabbin azuzuwa aƙalla miliyan tara da kuma ƙarin malamai su miliyan 9.5 zuwa shekarar 2050, domin su iya ɗauke adadin ɗalibanta da ke ci gaba da bunƙasa.

Wannan alƙaluman na nuna buƙatar gaggawa ta yin sauyin yadda ake bayar da ilimi da ilimantarwa da ya zarci gine gine kuma ya ƙunshi zamanantar da manhaja.

Bugu da ƙari, annobar COVID-19 ta ƙara ta'azzara matsalolin fannnin ilimi da ke ƙasa.

Yayin da wasu ƙasashen Afrika suka fito da dabarar koyarwa daga gida, amma dai rashin shirya wa irin wannan yanayin ya fito fili da buƙatar da ke akwai ta samar da manhajar karatu da zata iya dacewa da kowane irin yanayi da iftila'i kamar wannan ba zai iya kawarwa ba.

Hanyar kaiwa ga gaci na buƙatar haɗin gwiwa.

Wajibi ne gwamnatoci su muhimmantar da harkar ilimi a cikin kasafinsu, wajen tabbatarwa an samar da kuɗaɗe ba wajen gine gine ba kaɗai, har ma da na horas da malamai, da inganta dabarun koyarwa da kuma tsara manhaja.

Masu ruwa da tsaki masu zaman kansu, da suka haɗa da ƴan kasuwa da ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, suna da rawar da za su taka ta hanyar zuba jari a fasahohin ilimi da kuma tallafawa dabarun koyarwa na zamani.

Daga ƙarshe, makomar Afrika ta dogara ne kan yadda ta samar wa matasanta ƙwarewa da ilimi da ake buƙata wajen kurɗawa da yin jagoranci a wannan duniya mai yawan sauyawa.

Idan aka rungumi sauyin manhajar da ta muhimmantar da ilimi mai zurfi fasaha da kuma aiwatar da ilimi a aikace, musamman kan gwadaben tsarin STEM na bai ɗaya, za mu iya sauya tsarin karatunmu daga tsohon yayi zuwa wanda zai kai mu ga samun wadata nan gaba.

Marubucin, Nana Dwomoh-Doyen Benjamin marubuci mai kishin Afrika ne kuma wani ne a tafiyar Ubuntu Connect project.

Togaciya: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba lallai ba ne ya zo daidai da ra'ayi,hange da manufofin editan TRT Afrika.

TRT Afrika