Turkiyya ta sake sanar da kara wa'adin yarjejeniyar safarar hatsi daga Yukren da Rasha/ Hoto: Rueters

Daga Hannah Ryder

Sabunta yarjejeniyar safarar hatsi, wanda Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka fara shiga tsakani a watan Yulin 2022, na da matukar muhimmanci, saboda ta bayar da damar safarar hatsi da takin zamani daga Yukren da Rasha zuwa yankunan Bahar Maliya, sannan zuwa sauran sassan duniya da suka hada da Afirka.

Wata guda kafin yarjejeniyar farko, Shugaban Tarayyar Afirka Moussa Faki da kuma jagoranta na wannan lokacin kuma shugaban kasar Sanagal Macky Sall, sun tafi zuwa Moscow don matsa lamba da a samar da zaman lafiya, sannan a kuma tattauna tasirin yakin kan Afirka.

Manyan wakilan na Tarayyar Afirka sun yi taron neman mafita a taron shugabannin kasashen nahiyar a watan Mayun 2022.

Shugabannin na Afirka sun fitar da matsalolin da ake fuskanta, saboda kaso takwas na hatsi da kaso 12 na takin zamani da ake kai wa Afirka na zuwa ne daga Yukren da Rasha, inda da zarar an samu tsaiko wajen kai hatsi da kayan, to za a shiga matsalar hauhawar farashi.

Zabin da Turkiyya ta yi na jibintar lamarin wannan batu da ba shi muhimmanci a manufofinta na kasashen waje ta hanyar tuntubar Rasha, ba abu ne mai sauki ba.

A matsayin Turkiyya na mamba a NATO da G20, ta kasance karkashin matsin lamba kan ta saka wa Rasha takunkumi, sannan ta daina mu’amala da ita – kuma idan ta ki yin hakan to ta amince da yakin da ake yi kenan.

Sauraron bangaren Afirka

Duk da haka, a wajen manyan taruka na kasa da kasa, Ankara ta bayyana matsayinta karara. Misali, Turkiyya a ko yaushe na amincewa da kuri’ar da ake jefawa a Majalisar Dinkin Duniya don sukar Rasha bisa afka wa Yukren da ta yi.

Amma kuma duba da yadda aka mika me Afirka ke bukata, kasancewar Turkiyya mamba a NATO da G20, sannan ta zama makusanciyar Rasha da yankin Afirka, ya ba ta damar samun muhimmin waje a harkokin kasa da kasa.

Shiri da kokarin gwamnatin Turkiyya na sauraren Afirka ba wai ya faro ne a 2022 ba. Tun 1998 Turkiyya ta kaddamar da shirinta na karfafa alaka da Afirka, kuma ya zuwa yanzu ta gudanar da manyan tarukan hadin kai uku tsakaninta da Afirka-, a 2008 da 2014 da kuma 2021.

A yayin kaddamar da taron farko, an gabatar da Yarjejeniyar Istanbul da kuma Kundin Hadin Kai – wanda ya kunshi bangarori da yawa – da suka shafi noma da kiwo da kasuwancinsu da ayyukan kula da lafiy da, hadin kai don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma matakan kare muhalli.

Babban taro na biyu kuma ya amince da Yarjejeniyar Malabo, inda taron karshe na Istanbul da aka yi a 2021 kuma ya amince da ya samar da Yarjejeniyar Hadin gwiwa tare da kundin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da adalci ga kowa da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

A matsayin abokiyar Afirka kan ci gaba, Turkiyya ta sha nanata kudirinta na taimaka wa Afirka ba tare da sharadin siyasa ko tattalin arziki ba, inda take amincewa da ‘yancin mulkin Afirka tana kuma nuna shirinta na aiki da kasashen nahiyar don cimma manufar Tarayyar Afirka ta 2063, da ake cimmawa karkashin shirye-shirye 15.

Yarjejeniyar Malabo ta 2014 ta yi bayani karara game da Manufofin Tarayyar Afirka na 2063 da kuma ayyuka da suka hada da bayar da muhimmanci wajen aiki tare da Turkiyya.

Sakamakon haka, alakar kasuwanci da ta siyasa tsakanin Turkiyya da Afirka ta samu ci gaba sosai a tsawon wannan lokaci.

Yawan jarin kasuwanci tsakanin Turkiyya da Afirka ya kai dala biliyan 25 a 2020, wanda ya karu daga biliyan biyar a 2000, wanda ya kuma habaka fiye da jarin da ke tsakanin Afirka da abokan huldarta na yau da kullum.

Gwamnatocin Afirka na bai wa ‘yan kwangilar Turkiyya ayyuka inda ya zuwa yanzu sun samar da ayyuka 1,150 da kudinsu ya kai dala biliyan 70, wanda ya taimaka wa Afirka cike gibin karancin kayan more rayuwa.

Wani sabon aiki abun maraba shi ne gina layin dogo mai tsayin kilomita 368 kan kudin da ya kai dala biliyan 1.9 a Tanzaniya.

Kuma watakila, abu mafi ban mamaki shi ne yadda zuba hannun jarin ‘yan kasuwar Turkiyya a kasuwannin hannayen jari na Afirka ya kai kusan dala biliyan 2 a 2019, kusan kaso 3.5 na darajar hannayen jarin – wanda ya fi na sauran kasashen G20 yawa kuma yana habaka da sauri.

A kokarin da suke na tabbatar da kwanciyar hankali a yankin, ta hanyar nisantar kalubalen kawo kayayyaki da hauhawar farashi, duba da manufofoin Afirka ake aiwatar da hakan.

Musamman yadda yake wannan ne abin da Ankara ta yi inda ta dauki matakin gaggawa da wuri na shiga tsakani kuma ta samu nasara.

Samar da yarjejeniyar fitar da hatsi

A yanzu ta bayyana karara kayan amfanin gona na Rasha da suke da mihimmanci ga kasashen Afirka da yawa, za su ci gaba da tabbatar da ana yin kasuwanci da Afirka, har ma samar da bayan kara wa’adin da aka yi.

Tambayar da za a yi a nan ita ce, bayan samun nasarar sai kuma me? Ta yaya Turkiyya za ta bayar da karin gudunmowa don biyan bukatar Afirka?

Bayan yarjejeniyar safarar hatsin, akwai karin matakai da dama da Turkiyya za ta taimaka wa ci gaban Afirka.

Wata dama ta musamman da Turkiyya ke da ita wajen amsa kiran da Shugaba Macky Sall ya yi a matsayin jagoran Tarayar Afirka, na ganin Afirkan ta samu kyakkyawan wakilci a G20, kamar yadda Tarayyar Turai take, saboda akwai kasashenta da yawa a cikin G20.

China da ta goyi bayan Afirka a wannan mataki, tuni ta fara daukar matakan shigar da Afirka fagen kasa da kasa don ganin ana damawa da nahiyar yadda ya kamata.

Haka zalika, yadda Turkiyya ke kara kaimi wajen ganin an samu cikakken wakilcin Afirka a Kwamitin Tsaro na Majalisar DInkin Duniya, zai kara samar da tasirin siyasa da tattalin arziki ga kasar.

Sama da haka, yana da muhimmanci yadda Turkiyya ke kara kokarin sayo kayayyaki daga Afirka, sannan tana kuma kara karfafa gwiwar zuba jari da kafa masana’antu a nahiyar.

Wannan na da matukar muhimmanci musamman yadda a wannan shekarar yayin da shugabannin Afirka suke ci gaba da ayyukan farfadowa daga annobar Covid-19 da sauran matsalolin samarwa da isar da kayayyaki ga jama’a.

Ayyukan sun hadar da na samar da taken shekarar 2023 na ‘Gaggauta tabbatar da fara aiki da AfCFTA a nahiyar ta Afirka.’

Marubuciyar wannan makala Hannah Ryder, tsohuwar jami'ar diflomasiyya ce, kuma masaniyar tattalin arziki da ke da kwarewa ta shekara 20.

Sannan kuma babbar jami’a ce a Shirin Afirka na Cibiyar Nazarin Dabarun Cigaban Kasa da Kasa (CSIS).

TRT World