'Yan Afirka da ke kalubalantar  kallon rainin da ake yi wa nahiyar

'Yan Afirka da ke kalubalantar  kallon rainin da ake yi wa nahiyar

Ana sa ran babban taron zai share fagen ayyukan Afirka da shirya wa nahiyar kyakkyawar makoma.
Matasa sun halarci horaswa kan yadda ake hada mutum-mutumi mai sarrafa kansa (robotics) da kuma yadda ake samar da manhajar kwamfuta a birnin Nairobi. Hoto: AA.      

Daga Nana Dwomoh-Doyen Benjamin

An dade ana alakanta ta da abubuwa marasa kyau da kuma koma-baya wanda hakan ya sa ba a kallon dimbin arziki da al'adu da ke kwance a nahiyar.

A kokarin ganin an kalubalenci wannan kallo da ake wa nahiyar, taron Gyara Sunan Afirka (the Africa Image Conference) ya shirya gayyato 'yan Afirka daga ko ina a duniya a ranar 25 ga watan Mayu a kasar Ghana.

Babban taron yana da fatan bunkasawa da gyara kimar Afirka, inda yake jaddada muhimmancin kowane dan Afirka, walau yana zaune a cikinta ko kuma yana kasashen ketare, don gyara kimarta.

Manyan abubuwan da za su taimaka wajen gyara kimar su ne gyara halayya da dabi'unmu. Yana da kyau 'yan Afirka su fahimci karfin da suke da shi wajen canja irin kallon da ake musu.

Ta hanyar daukar matakai za mu iya rushe irin wadannan tunanin kuma mu rika nuna kyakkyawan abubuwan da ya kamata a rika dangantawa da Afirka.

Wannan yana bukatar canji, da kuma bai wa 'yan Afirka kwarin gwiwa kan cewa su rika alfahari da asalinsu, da yin murna kan nasarorin da suka samu kuma su rika kalubalantan zantukar da ke mayar da nahiyar baya.

Taron Gyara Sunan Afirka zai kasance waje ne da za a tattauna batutuwa da suka jibanci gyara Sunan Afirka.

Abin alfaharin Afirka

Wannan taron da ya kunshi mutane daga bangarori daban-daban zai taimaka wajen bunkasa shirye-shiryen Afirka da za su samarwa nahiyar makoma mai kyau.

Duk da cewa an samu ci gaba da bangarori daban-daban a Afirka, ana ci gaba da yi mata kallon kashin baya. Hoto: Reuters

Wadannan shirye-shiryen za su saka wa 'yan Afirka kaunar sayan kayan Afirka, domin saka musu alfahari da al'adunsu da karfafa musu gwiwa dangane da hadin kai da darajawa da mutunta dan Adam da aiki tare da samar da hanyar tattaunawa a matsayinmu na 'yan asalin Afirka.

Ko da yake akwai munanan kallo da dole 'yan Afirka da kuma Afirka su kalubalanta, daya daga ciki da aka dade ana yi mata shi ne kallon da ake wa Afirka da wani wuri da talauci da cututtuka da kuma yake-yake ya yi kakagida.

Duk da cewa an samu ci gaba sosai a bangarori daban-daban, har yanzu akwai irin wannan tunani a zukatan mutane da yawa.

Yana da muhimmanci a kawar da wannan tunanin ta hanyar bayyana yadda tattalin arzikin Afirka zai iya bunkasa da ci gaban fasaha da al'adu da sauran nasarorin da aka samu.

Daya daga cikin manyan kalubalen shi ne sauya kallon da ke yi wa Afirka na cewa kasa daya dunkule waje guda, maimakon kallonta a matsayin kasashe mabambanta ta fuskantar al'adu da kuma tarihi.

Ana yawan kallon Afirka a matsayin abu guda, inda ake watsi kasancewar kowace kasa daban yake kuma haka gudunmuwar da take bayarwa.

Matasa a matsayin jagorori

Don magance wannan tunani yana da muhimmanci ga 'yan Afirka su fahimci asalinsu, su rungumi al'adunsu sannan su rika baje-kolinsu da kuma amfani da harsunansu.

Matasa suna babbar rawar da za su taka wajen sake tunani da fasali da kuma gyara kimar Afirka. Su ne jagororin kawo canji wadanda suke da sabon tunani da kirkire-kirkire da kuma sanin muhimmancin kai.

Wasu masu bushe-bushen Afirka ta Kudu, yayin da suke bayyana basirarsu a birnin Johannesburg. Hoto: AA

Idan ana so a sauya kimar Afirka, dole ne matasa su hada karfinsu da fikirarsu waje guda.

Hakan zai iya samuwa ne ta hanyar ilimi wanda zai bunkasa fahimtar tarihin Afirka da al'adu da nasarori da kuma karfafa sana'o'i da fasaha da kirkire-kirkire da kuma tsare-tsaren ci gaba mai dorewa.

A kashe taron Gyara Sunan Afirka ya kasance wata babbar nasara a kokarin farfado da kimar Afirka.

Ta hanyar hada kan 'yan Afirka daga kowace kusurwa ta duniya, yana fatan sauya dabi’u da zantuku.

Ta hanyar shirye-shiryen Afirka, taron zai saka wa 'yan Afirka kaunar amfani da kayan Afirka, su rungumi al'adunsu da daraja dan Adam da kuma hanyar tattaunawa a matsayinsu na 'yan asalin Afirka.

Wannan aiki ne na kowa da kowa wanda sabon tunani zai jagoranta wanda kuma zai kalubalanci wancan kallon da sake zayyana tarihin Afirka da zai bude hanyar samun nasara da hadin kai a nahiyar.

Marubucin, Nana Dwomoh-Doyen Benjamin, Babban Darakta ne a Africa Chamber of Content Producers, wato wata kungiya ce da ta dukufa wajen samar kyawawan labarai da bayanai game da nahiyar Afirka.

A kula: Wannan ra'ayin marubucin ne, ba na kafar yada labarai ta TRT ba.

TRT Afrika