Daga Claire Taylor
A ranar 10 ga watan Fabrairu ne aka harbe shahararren mawakin hip-hop Kiernan Forbes (AKA) a wajen wani wurin cin abinci a birnin Durban.
Al'amarin ya sake dawo da matsalar tashe-tashen hankali masu alaka da bindiga wanda hakan yake kashe mutum 30 a kullum a Afirka ta Kudu. An fi mayar da hankali ne kan batun kama wadanda suka kashe AKA.
Amma kuma gurfanar da su gaban shari'a yana da muhimmanci sosai, musamman ga iyalansa da abokansa saboda su samu natsuwa. Sannan ya kamata a gano hanyoyin da za a kawo karshen tashe-tashen hankula masu alaka da bindiga.
Jinsi da manyan laifuka
Manyan laifuka da tashin hankali a Afirka ta Kudu sun bambanta da juna musamman idan aka yi la'akari jinsin wanda abin ya shafa.
Maza da mata suna fuskantar hakan ta hanyoyi daban-daban. Maza irinsu AKA su ne suka fi fuskantar matsalar – 63 cikin 73 na wadanda ake wa kisan gilla a rana a Afirka ta Kudu maza ne.
Yayin da yake da wuya ka ga an yi wa mace kisan gilla, su sun fi fuskantar hadarin kisa daga hannun abokan zamansu maza a gidajensu kuma sun fi fuskantar matsalar cin zarafi.
Yawancin masu aikata laifukan ga maza ko mata – maza ne. Don fahimtar abin da yake ingiza maza aikata laifukan yana da kyau a iya raba zare da abawa tsakanin jinsin maza da yiwuwar aikata laifi.
Misali wani bincike da aka wallafa a Mujallar The Journal of Criminal Law and Criminology a shekarar 1987, ya tabbatar da cewa akwai alaka tsakanin kasancewa mai laifi da wanda ake azabtarwa.
Wannan ya nuna yadda maza suka fi fada wa hadarin fuskantar harbin bindiga da kuma muhimmancin kare mazan don kawo karshen matsalar.
Takaita yawan bindigogi
An kera bindigogi ne don su yi kisa kuma iya yawan bindigogi iya yawan yadda ake harbi da kashe mutane ko ji musu rauni ko kuma yi musu barazana.
Saboda haka idan aka takaita yawan bindigogin da ke hannun mutane, to za a ceto rayuka kamar yadda aka taba gani a Afirka ta Kudu.
Yayin da adadin bindigogi ya yi kasa a farkon shekarun 2000 saboda dokar takaita mallakar bindiga ta shekarar 2000, an ga raguwa a adadin mutanen da ke mutuwa a Afirka ta Kudu sanadin harbin bindiga.
Wani bincike da Richard Matzopoulos ya yi wanda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta American Journal of Public Health, ya ce kimanin mutum 4,500 ne aka ceto su daga mutuwa sanadin harbin bindiga a biranen Afirka ta Kudu biyar tsakanin shekarar 2001 zuwa 2005 saboda matakan da aka dauka.
Sai dai kuma yayin da adadin bindigogi suka karu a Afirka ta Kudu daga shekarar 2010 zuwa 2011 saboda gazawa wajen bin dokokin takaita bindigogi saboda karancin ma'aikata da zamba da rashin tsari da cin hanci da rashawa da sauransu, hakan ya sa tashe-tashen hankula masu alaka da harbin ya karu.
Daga shekarar 2022, adadin wadanda aka kashe sanadin harbin bindiga ya kusa kamo na shekarar 1998, inda a kullum ake kashe mutum 34.
A duk duniya, bincike ya gano cewa takaita mallakar bindiga yana ceto rayuka. Daya daga cikin irin wadannan muhimman bincike shi ne na Colombia daga Vecino-Ortiza et al a shekarar 2020.
Ya gano cewa haramta wa mutane daukar bindiga a bainar jama'a a biranen Bogotá da Medellín yana kare rayukan mutum 30 a duk wata, kuma za a iya kare rayukan karin mutum 45 idan aka saka irin wannan haramci a wasu karin birane bakwai.
Mece ce mafita?
Yawancin kashe-kashen da aka aikata ba su da alaka da manyan laifuka amma sukan faru ne bayan gardama ko rashin fahimta. Hakazalika galibin kashe-kashen suna faruwa ne yayin wata takaddama.
Hakan yana da tasiri daban-daban na shiga tsakani. Daya daga ciki shi ne kiraye-kirayen da ake cewa 'yan sanda su shawo kan matsalar aikata manyan laifuka a Afirka ta Kudu, sai dai ana ganin da wuya hakan ya yi tasiri sosai.
Maimakon aikewa da karin jami'an 'yan sanda, kamata ya yi a fahimci yadda laifukan da tashe-tashen hankulan suke, saboda hakan yana da muhimmanci wajen magance matsalar.
Abu na biyu shi ne yawaitar yadda kungiyoyi masu dauke da manyan makamai wadanda suke kare al'ummomi.
Wanda hakan zai iya ci gaba da jawo takaddama wadda daga karshe take kawo asarar rai.
Rage rikice-rikice da manyan laifuka a Afirka ta Kudu ba abu ba ne mai tsauki, amma ya kamata a dauki matakai kwarara kuma a yi la'akari da jinsi da makami da kuma dalili.
Babban matakin da za a dauka shi ne na rage yawan mallakar bindigogi. Yayin da rundunar 'yan sanda ba za ta iya sanya ido kan takaddamar da ke faruwa tsakanin mutane ba, tana da muhimmiyar rawar da za ta iya takawa wajen kwacewa da lalata dimbin bindigogi a kasar musamman manyan makaman da mallake su ba bisa ka'ida ba.
Ko da yake karbe makaman zai yi aiki ne kawai, bayan mun toshe kafar da haramtattun makamai suke shigowa al'ummominmu.
Akwai dimbin bindigogi da aka mallake su bisa ka'ida wadanda suke hannun jami'an gwamnati da fararen hula, sai dai sukan kawo rahoton cewa bata ko sace akalla bindigogi 24 a kowace rana.
Wannan yana nufin dole sai mun karfafa dokokin mallakar bindiga da harsasai saboda kada su rika zulalewa zuwa hannun gurbatattu.
Muna fatan kisan AKA ya sa a farga don daukar matakai don dakatar da tashe-tashen hankula masu alaka da bindiga a Afirka ta Kudu.
Marubucin, Claire Taylor, yana bincike ne kan yadda za a kawo karshen tashe-tashen hankula masu alaka da bindiga a Afirka ta Kudu wato Gun Free South Africa (GFSA), a karkashin wata kungiya mai zaman kanta.
A kula: Wannan ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT ba.