Kamar yadda wani rahoto na gwamnatin Faransa ya ce har yanzu akwai 80 zuwa 90 cikin 100 na kayayyakin tarihin Afirka da ke ajiye a nahiyar Turai. Hoto: AFP

Daga Lisa Modiano

Bayan kwashe shekaru na matsin lamba daga Afirka da wasu cibiyoyin kasashen Yamma, an fara shirye-shiryen dawo da kayayyaki masu daraja na Afirka wadanda aka dade ana jira – kuma tagullar Benin tana daga cikin mafiya muhimmanci.

Akwai kayayyaki kamar tama da haure da kuma tagulla wadanda asalinsu aka kawata Fadar Masarautar Benin da su, wacce yanzu take jihar Edo a Nijeriya.

Lokacin da masarautar ta yi shura wato tsakanin shekarar 1450 zuwa 1650, masarautar ta kai har Kogin Neja daga gabashi, ta kuma dangana da Legas daga yammaci.

Kwararrun masu zane-zane ne suka yi wa tagullar ado wanda Oba (sarki) ya umarce su da su yi, tagullar tana nuna dadadden tarihin masarautar da nasarorin da ta samu.

Akwai kayayyaki kamar tama da haure da kuma tagulla wadanda asalinsu aka kawata Fadar Masarautar Benin da su, wacce yanzu take jihar Edo a Nijeriya. Hoto: AFP

Sai dai a karni na 19, sojojin Birtaniya sun mamaye Birnin Benin yayin da suke kokarin fadada ikonsu a Yammacin Afirka.

A watan Fabrairun 1897, dakarun Birtaniya sun yi wa masarautar dirar mikiya, wanda hakan yana cikin munanan ayyukan zubar da jinin da aka taba gani a tarihin mulkin mallakar Birtaniya.

Sun fakaice ne da cewa ana mulkin masarautar ne da salon 'mulkin jahiliyya', kuma hare-haren dakarun Birtaniyan ne suka kawo karshen Masarautar Benin.

Bayan dimbin asarar rayuka, dakarun Birtaniya sun sace abubuwa masu daraja da ke fadar sarkin a matsayin ganima.

Cikin abubuwan da suka sace har Tagullar Benin – bayan da aka kai su Birtaniya an raba su zuwa wasu wurare masu zaman kansu da wasu cibiyoyin Turai, inda suke ajiye har zuwa yau. Tun daga lokacin kayayyakin wadanda sun fi guda 5,000.

Rashin adalcin da aka yi a baya

Kalmar "Tagullar Benin" kanta tana nuna wata matsala da aka yi gado: kalmar ba ta nuna ainihin abin da kayayyakin suka kunsa gaba daya, saboda kadan ne daga cikin kayan tarihin ne tagulla, yayin da yawancinsu haure ne da kuma tama.

Babu mamaki ayyukan zane-zane da aka fi darajawa biyu a Turai a karni na 19 su na kasar Girka da Italiya kuma suna amfani da tagulla ne wajen sassaka gumakansu.

Babu mamaki ayyukan zane-zane da aka fi darajawa biyu a Turai a karni na 19 su na kasar Girka da Italiya kuma suna amfani da tagulla ne wajen sassaka gumakansu. . Photo: Reuters

Kamar yadda wata masaniya 'yar Afirka Susan Vogel ta ce, wannan kuskuren game da kalmar ya samu asali ne daga bukatar da kasashen Yamma suke da ita don su rage wa kayayyakin al'adun Afirka kima, su juya su don su dace da tunanin Turawa kan yadda manyan kayayyakin tarihi ya kamata su kasance.

Kamar yadda Aiko Obobaifo, wani masani kan tarihin baka kan al'adun Benin, ya ce tagullar ba kawai kayan ado ba ce – suna nuni ga addini da hanyar tafiyar da rayuwa da tarihin ci gaba wanda mulkin mallakar Birtaniya ya katse.

Mayar da kayayyakin zai tabbatar da rashin adalcin da aka yi a baya kuma zai nuna an kwatanta adalci a yanzu. Hoto: AFP

A shekarar 2023, shin bakinmu ba zai zo daya ba kan muhimmancin al'adarmu a matsayinmu na kasa saboda muhimmancin haka ga asalinmu da bukatar alkintawa da daraja al'adar a ainihin yadda take?

Kamar yadda wani rahoto na gwamnatin Faransa ya ce har yanzu akwai 80 zuwa 90 cikin 100 na kayayyakin tarihin Afirka da ke ajiye a nahiyar Turai.

Mayar da kayayyakin zai tabbatar da rashin adalcin da aka yi a baya kuma zai nuna an kwatanta adalci a yanzu.

Shin me ya sa hakan yake daukar lokaci?

Gidajen tarihin kasashen Yamma da wuraren ajiye kayayyaki masu zaman kansu suna yawan nuna damuwa kan yadda za a kula da yadda za a alkinta wadannan muhimman kayan tarihi idan aka mayar da su Afirka, akwai kuma batun wane ne ya mallake su a shari'ance wanda hakan yake kara dagula al'amarin.

Kamar yadda wani rahoto na gwamnatin Faransa ya ce har yanzu akwai 80 zuwa 90 cikin 100 na kayayyakin tarihin Afirka da ke ajiye a nahiyar Turai. Hoto: Reuters

Damar Nijeriya ke da ita

Samar da mafita da za ta yi kowa da kowa dadi zai ci gaba da rataya ne a wuyan gwamnatoci da ci biyoyi da kuma manyan hukumomin duniya.

Ko da yake cibiyar Smithsonian Institution da gidan tarihi na Metropolitan Museum of Art da kuma gwamnatin kasar Jamus duka sun bayyana aniyyarsu ta mayar da dimbin kayayyakin tarihin kuma an fara samun ci gaba ta fuskar gina sabon gidan tarihi a Birnin Benin da fatan ya rika baje-kolin kayayyaki da kuma kula da kayayyakin tarihi masu daraja da za a dawo da su.

Sai dai wannan shiri ya fuskanci cikas bayan da tsohon shugaban kasar Nijeriya ya ce a mayar da ikon mallakar kayan da za a dawo da su ga iyalan sarakunan masarautar da aka sace kayayyakin daga wurinsu.

Hakan yana nufin cewa za a mayar da kayan ne zuwa fadar Oba, ko kuma duk wani waje da sarkin masarautar ya aminta da tsaronsa.

The Benin Bronzes symbolise rich African art, culture and technology. Photo: Getty

Yayin da kasashen duniya suke fama da kalubalen mayar da kayayyakin, akwai wata gaskiya da ta fito fili: Tagullar Beninin ragowa ce daga cikin kayan galimar mulkin mallaka kuma kamar duk wani kaya da aka sace da karfin tuwo, babu abin da ya fi idan ba mayar da shi aka yi ba ga mai shi.

Nijeriya ce take da dama, amma tsofaffin 'yan mulkin mallaka ba, kan makomar kayayyakin. Hoto: AFP

Kayayyakin tarihin suka nuna labarin Masarautar Benin kuma suna da alaka mai karfi da mutanen da aka sace su daga wurinsu da kuma kasar. Nijeriya ce take da dama, amma tsofaffin 'yan mulkin mallaka ba, kan makomar kayayyakin.

Marubuciyar, Lisa Modiano, kwararriya ce a fannin tarihin Afirka.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta gabatar ba sa wakiltar ra'ayoyi da manufofin TRT Afrika.

TRT Afrika