Tsawon wata guda kenan tun bayan da Kungiyar Hadin Kan Tsaro a Turai (OSCE) ta yi kira ga shugabanni da su zage damtse "wajen gina tattaunawa da yaki da kyamatar Musulmai," a lokacin da kuma kyamar Musulman ke kara yaduwa a kasashen Turai.
Duk wannan kira na a dauki mataki, Turai ta nuna ko kusa ba ta da shirin dyukar matakin hadin kai don yaki da kyamar musulunci.
Kasashen Turai da dama na ci gaba da samun rahotannin yin barazana ga Musulmai kamar a kasashe irin su Norway. Sannan kuma tsarin aikin dan sam=ndan da ake aiki da shi a kasashen na yin barazana tattakin zaman lafiya da Musulmai ke yi a Jamus.
Masu tsaurin ra'yi da Turai ke goya wa baya ma na kara ta'azzara kalubalen, inda mutanen da suke da tsananin nuna kyama ga Musulunci suke tsaya wa takara a zaben 'yan majalisar Tarayyar Turai na watan Yuni.
Duk wannan nauni ga bukatar maganace matsalar Nuna kyama ga musulunci a Turai tare da tabbatar da bayar da cikakkiyar kariya ga Musulmai da 'yancinsu daga tsana da nuna wariya.
Domin magance barazanar da ake yi ga jama'ar Musulmai, wasu kasashe sun yi kokarin amfani d akarfi. Kwanan bayan nan Norway ta dauki matakin baiwa jami'an tsaronta makamai don gadin Masallatai, inda Faransa kuma ta kafa wata rundunar tsaro ta tafi da gidanka don magance matsalar hana sanya hijabi a makarantu.
Irin wadannan matakan tsaron ba za su iya magance yawaitar nuna wariya ga Musulmai da ake yi ba, ba a tabbatar da garantin tsaro ga muhallan Musulmai ba.
Matakin na iya yin kaikayi koma kan mashekiya, inda nuna wariyar launin fata ke ci gaba da yaduwa a ayyukan 'yan sandan Turai, kamar yadda wani sabon rahoton Hukumar Kare Manyan Hakkoki ta Turai ta fitar ya bayyana.
Kasashen Turai na kan tsarin sake dawo da nuna bambanci tsakanin al'ummu da ware Musulmai, har sai ayyukan 'yan sandansu sun zama masu yaki da nuna kyama ga Musulmai, wanda abu ne nadiran.
Tasirin Gaza
A yayin da yakin da Isra'ila ke yi Gaza ya rura wutar ra'ayin kyamatar Musulmai a nahiyar, Turai na bukatar daukar ƙwaƙƙwaran matakin ba sani ba sabo don yaƙar Nuna Kyama ga Musulmai.
Bayan dukkan wannan, an lura da karuwar nuna kyama ga Musulmai tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare, kuma gwamnatin Beljiyom na yi kaffa-kaffa don kauracewa suka kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Dan kankanin yunkurin tarayyar Turai na dakatar da hare-haren da Isra'ila ke kai wa ya janyo wa Musulman Turai aibatawa. Jama'a na tsoron karya dokar hana su taro da bayyana ra'yoyinsu a kasashe da dama.
Misali, Musulmai da ke yin zanga-zanga a Jamus na fuskantar cusgunawa mummuna daga 'yan sanda, inda kaso 66 na Musulman Faransa suka bayyana a hukumance 'yan sanda na nuna musu wariya.
Wadannan abubuwa sun sabawa da ginshika d amanufofin Tarayyar Turai na 'yanci ga kowa, kuma hakan na kalubalantar nasararta ta 'yancin jama'a.
"Tarayyar Turai ta la'anci nuna tsana da wariya ga Musulmai, kamar yadda muke ;a'antar duk wani nau'i na nuna wariya. gaba d atayar da zaune tsaye saboda kan addini ko wani da aka yi imani da shi,"
Duk da haka, Musulman Turai da dama na ci gaba da fuskantar nuna wariya a gida, a yayinda Tarayyar Turai ba ta nuna wata damuwa ga bukatu da matsalolin Musulmai na.
Wani abu da ke jan hankali kuma, a ciki da wajen Tarayyar Turai, ayyukan yaki da nuna kyama ga Musulmai sun fuskanci matsalar hargitsi da tsananin muhawara daga jama'a.
Dauki Jamus, inda gwamnati ta nace cewa hari kan musulmai saboda addini ko wasu dalilai "ba za a karva wannan ba."
Wannan bai dakatar da laifukan nuna kyama ga Musulunci ba wanda a shekarar da ta gabata ya ninka sama da sau biyu. Tun wannan lokaci, hare-haren Isra'ila a Gaza sun kara ta'azzara kymatar Musulmai a Jamus.
A wayen Tayarrar Turai, Birtaniya na kokarin shawo kan sukar da ake yi mata kan sabuwar ma'ar 'Tsaurin ra'ayi' da ta fitar.
Da munaryadawa da tallata akidar rikici, tsana ko kin aminta da bakin mutane,"ma'anar na fadada halayyar inda ta ke kiran daidaikun mutane ko kungiya a matsayin barazana.
Da yawa na yi wannan a matsayin kokarin nufar kungiyoyin Musulmai da sunan yaki da Islamaphobia.
Har yanzu gwmanatin Landan ba ta yi watsi da wannan ra'ayi ba. Duba da haka, Turai ba ta da hadin kai wajn yaki da daya daga cikin manyan matsalolin da Musulmai ke fuskanta.
Tasowar kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi
Manyan bangarorin da ke kara ingizawa da rura wutar su ne jam'iyyu masu tsaurin ra'ayi na Turai, inda suke kara yada nuna kyama a Musulunci.
'Yan siyasa da dama a wannan bangare na sansano wata dama da za a yi amfani a ita wajen yin yakin neman zabe da sunan nuna kyama ga Musulunci, a juya sitiyarin Tarayyar Turai zuwa tsaurarawa.
Bayan hakan, Brussels na jiran zaben 'yan majalisa mai zafi a watan Yuni, kuma jam'iyyun ECR - kungiya mai tsaurin ra'ayi na ta samun karbuwa.
Jam'yyun da suke da tarihin nuna wariya da kyamatar Musulmai irin su Vox da ke Spaniya da "Brothers da ke Italiya, duk sun shiga karkashin inuwar ECR don tsayawa takara, kuma suna gangami da nuna kyama ga Musulmai.
Wadannan jam’iyyun ma ba su kadai ba ne. Ana sa ran da yawa daga cikin masu adawa da Turai za su yi zabe a kasashe tara na Turai, wanda zai samar da isasshen sarari ga 'yan majalisar dokoki masu tsaurin ra'ayi don hada kawancen masu ra'ayin riƙau tare da goyon bayan masu rinjaye.
Yayin da tasirin masu tsaurin ra'ayi ke girmama, zai iya zama ma da wahala EU ta samar da yarjejeniya mai fa'ida kan kare 'yancin Musulmai.
Ga al'ummar Musulman Turai, wadannan alamu ne masu ban tsoro. Na farko, kasancewa mai ƙarfi na hannun dama a majalisa na iya ƙara tasiri mai tsauri kan abubuwan da EU ta sa gaba, gami da ƙoƙarin yaƙi da ƙyamar Musulunci.
Ban da haka kuma, jam'iyyun masu ra'ayin riƙau masu ƙiyayya da Musulunci za su so su yi kira ga madogararsu, bayan da suka shafe shekaru suna inganta sabani tsakanin Musulunci da Ƙasashen Yamma.
Kungiyar Alternative for Germany (AfD) ta dama ita ce misali: ta gudanar da zanga-zangar nuna ƙyama ga Musulmai shekaru da suka wuce kuma yanzu tana daya daga cikin manyan jam'iyyun kasar.
Yayin da tasirin masu ra'ayin riƙauhannun dama ke girma, zai iya zama ma da wahala EU ta samar da yarjejeniya mai fa'ida kan kare 'yancin Musulmai.
Wannan wani muhimmin abin la'akari ne don tsara matakin da kungiyar ta dauka na dogon lokaci game da kyamar Musulunci a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna kyama, kyama da kuma cin zarafin musulmi a fadin nahiyar.
Mafita
Akwai matakai na zahiri da Turai za ta iya ɗauka don magance kyamar Musulunci.
Misali, shugabannin EU na iya yin la'akari da fitar da takamaiman ƙa'idodi kan sa ido kan 'yan sanda da buƙatun horarwa ga duk ƙasashe mambobin. Haka kuma su sanya wajabta wa dukkan jami’an ‘yan sanda sanya ƙyamar Musulmai a matsayin wani bangare na horar da su.
Bugu da ƙari, ya kamata jam'iyyun EU masu ra'ayin rikau da masu ra'ayin rikau su fitar da faifan bidiyo da suka bambanta 'yancin fadin albarkacin baƙi da ƙyamar Musulmai da ƙyamar Musulunci.
Wannan matakin zai haifar da bambanci ga kalaman ƙiyayya da shahararrun jam'iyyun masu ra'ayin riƙau suka yi da sunan "ƙimar Yammacin Turai." Ta fuskar zabe, hakan na iya bai wa jam'iyyu masu ra'ayin riƙau damar shiga bankunan jefa kuri'a na miliyoyin Musulman Turai a yayin da jam'iyyunsu ke fafutukar ganin sun dawo da farin jini a majalisar dokokin kasar.
EU za ta iya taimakawa wajen sauya zuƙata da tunani ta hanyar aiwatar da kamfen na ilimi game da Musulmai a cikin makarantu, jami'o'i da tarukan ilimi.
Waɗannan ayyuka za su iya taimakawa wajen kawar da fahimtar juna da nuna alaƙa tsakanin wannan rukuni da gaba ɗaya, da kuma jadada buƙatar haɓaka zaman tare.
Waɗannan matakan na iya zama tubalan gini don taimaka wa yaƙi da ƙyamar Musulunci tare da muhimmancin da ya cancanta.
Marubucin, Hannan Hussain, ƙwarare ne kuma marubuciya kan harkokin kasa da kasa. Shi masanin Fulbright ne na tsaro na kasa da kasa a Jami'ar Maryland, kuma ya tuntubi Cibiyar Sabbin Layukan Dabaru da Manufofi a Washington. An sha wallafa rubuce-rubucen Hussain a Cibiyar Zaman Lafiya ta Ƙasa da Ƙasa ta Carnegie Endowment for International Peace da Georgetown Journal of International Affairs, da kuma Express Tribune.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyanana ba sa wakiltar ra'ayi, fahimta, ko manufofin Editocin TRT Afrika.