Ka’idojin amfani
Za a iya amfani a cikin gida da kuma a kasashen waje da adireshin shafin intanet na ainihi na trtafrika.com, wanda TRT ke wallafa abin da ke cikinsa ne, ta hanyar kiyaye sharudan da aka zayyana a nan kasa:
Shiga shafukan harsuna ta adireshin trtafrika.com ko kuma ta wasu adireshin, na nufin masu amfani da shafukan sun amince su kiyaye ka’idojin amfani da su.
Don Allah, a tsanake, a karanta sharuda da ka’idojin amfani da ke tafe, kuma idan ba ka amince da dukkansu ba sharuda da ke tafe ba, to ka daina amfani da shafin nan take kuma kar ka sake amfani da shi.
Ka amince ka yi amfani da shafin trtafrika.com domin dalilai da doka ta yarda da su zalla, wadanda ko kadan ba su keta, ko takaita ko kuma tauye hakkokin wasu na amfani da shi ba. Haramun ne tsantsa, a yada duk wani abu da bai dace ba ko na rashin da’a, wanda zai haifar da damuwa ko kunci ga sauran masu amfani da shafin, ko kuma kawo cikas ga mu’amalla yadda ya kamata a cikin shafukan.
Sauye-sauye – sabunta ka’idojin amfani da shafi
TRT na da hakki da ‘yancin sauyawa ko sabunta sharudan amfani da trtworld.com a kowane lokaci. Nauyi ne da ya rataya a wuyan masu amfani da shafin su duba domin sanin ko an sauya ko kuma an sabunta ka’idojin. Saboda haka ka amince da dukkan sabbin ka’idoji na amfani da shafin matsawar dai ka ci gaba da amfani da shafukan harsuna masu nasaba da shi. Muddin ba ka amince da sabbin ka’idoji ko wadanda aka sauya ba, don Allah ka daina amfani da shafin. Idan ka ga wasu sharuda na musamman a trtafrika.com, wadanda suka ci karo da wadannan sharuda, to ka’idojin na musamman su ne za a yi aiki da su.
Hakkin mallaka/Tambari
TRT ce ke tafiyar da trtworld.com kuma TRT ce da kanta ko kuma daga wasu kafofi ta ke samar da duka ko kuma wasu daga cikin abubuwan da ake wallafawa a shafin. A karkashin dokokin kasa da dokokin kasa da kasa na hakkin mallaka da kuma tambari ko alama ake samar da abubuwan da ake wallafawa a trtworld.com da kuma dukkan sunaye, da hotuna da kuma tambari ko alamomi masu nasaba da ayyuka ko kayayyaki na TRT da wasu kafofi abokan huldarta.
Wadannan abubuwa da aka ambata har da manhajoji da harufa ko lambobin sirri, ba a baka izinin sauya su, ko yin kwafensu, ko yin kwaikwayonsu, ko sake wallafawa su, ko yada su ko watsa su ko kuma sauke su a kwamfyutarka ba. Ka amince ka yi amfani da abubuwan da aka wallafa ne domin amfaninka amma ba domin neman kudi ko kasuwanci ba, tare da kiyaye hakkokin mallaka.
Ba a yarda a fassara duk wata shadara ta wannan rubutun da nufin samun damar amfani ta haramtacciyar hanya, da abubuwan da aka wallafa a shafin trtafrika.com wadanda aka zayyana a bayanin da ya gabata ba.
Ba a ba ka izinin bugawa ko wallafawa ko sake rubutawa, ko kuma kai tsaye ko a kaikace ka ka yada abubuan da ke trtafrika.com ba. Idan akwai sabani tsakanin wadannan sharuda da kuma wasu sharuda ko ka’idoji na musamman ta suka bayyana a cikin yarjejeniyoyi tsakanin TRT da kafofi abokan huldarta dangane da sake watsa shirye-shiryen rediyo ko na talibijin da ma wasu abubuwan watsawa, to sharuda na musamman da ke cikin yarjejeniyiyin ne za a yi aiki da su. Ba a yarda ka adana duka ko kuma wani bangare na abubuwan da aka wallafan a kwamfyutarka ba, fa ce domin amfaninka amma ba domin neman kudi ko kasuwanci ba.
Bai wa TRT abubuwa
Gudummowarka ga shirye-shiryen TRT kamar rubutu, hoto, bidiyo ko sauti, na nufin ka bai wa TRT da kuma shafukan intanet na kasa-da-kasa da masu amfani da TRT za su iya shiga, sahihin izini na yin kwafe, ko gyara (ciki har da sauyawa ko yin kwaskwarima domin dacewa da tsarin aiki ko ka’idojin watsa labarai), ko watsawa, ko yayatawa ko kuma gabatar da abin da ka ba da gudummowar, ba tare da wani nauyi na biyan kudi na hakkin mallaka ba.
TRT na da damar bayar da gudummowar taka ga wasu amintattun kafofi abokan hulda a yanayi na musamman. Hakkin mallaka na gudummowarka, zai kasance naka ne, amma ba kebantacce ba. Duk da haka za ka iya bai wa wasu wannan abin da ka ba da gudummowar. Za ka ba da tabbacin cewa abin da ka ba da gudummowar mallakinka na asali kuma bai kunshi tozarci ko cin fuska kuma keta dokokin Turkiya da dokokin kasa da kasa ba, kuma kana da hakkin ka bai wa TRT izinin amafni da abin bisa dalilan da aka zayyana a baya, sannan kum ka samu amincewar mutumin dake cikin aikin naka ko kuma iyaye ko amintacce nasa/nata idan bai kai ko ba ta kai shekara 18 da haihuwa ba.
Mashigun wasu shafukan intanet
Trtafrika.com na da damar sanya mashigun shafukan intanet da wasu abokan huldarta ke tafiyarwa. TRT ba za ta tafiyar ko sa ido kan bayanai, ko abubuwa ko kuma ayyuka da suka samar ba, kuma ba za ta fito karara ko a kaikaice ta ba da tabbaci game da abubuawan da aka wallafa a wadannan shafukan ko kuma amfani da su ba.
Kasancewa mamba da kuma shafi na kashin kai
TRT za ta goge dukkan shafukan mutum mai bibiyarta wanda aka samu yana da shafuka fiye da daya da nufin jawo damuwa ga sauran masu amfani da shafinta ko kuma kawo rudani. Dole ne masu amfani da shafi su shiga da sahihin adireshin imel, wanda su ke amfani da shi a kai a kai. TRT za ta soke duk wata rajista da aka yi da adireshin imel na wucin gadi ko na wani mutum dabam ba tare da ta bayar da sanarwa ba. TRT ce ke da hakkin goge duk wani shafi na mai bibiyarta muddin muddin ta gano cewa mai amfani da shafinta na da damar shiga ta adireshin na’urar wani da nufin yin bat-da-bami don amfani da shafuka daban-daban na TRT ko idan mai bin shafin ya yi amfani da duk wasu ayyuka na TRT ta hanyar da ba ta dace ba.
Trtafrika.com ka iya samar da damar martini da kuma dandalin dattaunawa kai tsaye domin cudanya ko mu’amalla tsakanin ma’abota shafinta. TRT ba ta sa ido kan sakwanni, ko bayanai ko kundaye da aka tura ga wadannan dandula ko zauruka. Ba ka da damar yin wadannan abubuwa yayin da ka ke amfani da zaurukan:
Ba ka da damar takaita damar wasu masu amfani da zaurukan ko dandalin tattaunawar ko kuma hana su shiga baki daya.
Ba ka da damar wallafawa ko watsa duk wani bayani da ya saba doka, ko mai yin barazana, ko mai tayar da hankali, ko na tozartarwa, ko na izgili, ko na batsa ko kuma na rashin da’a, wanda ya keta ko ya karfafa gwiwar keta duk wata doka ta kasa ko ta kasa-da-kasa (har da dokoki na yankuna ko jihohi), ko ya zama aikata babban laifi ko kuma ya kunshi batanci da fatar baka ko a rubuce.
Ba ka da damar wallafa ko watsa duk wani bayani, ko manhaja ko kuma wasu abubuwa, ciki har da wadanda ke samun kariya daga dokokin hakkin mallaka da wadanda aka debo daga cikinsu, wadanda suka keta hakkin sirri ko hakkin watsa labarai na wasu, ko kuma suka yin karan-tsaye ga hakkin wasu, ba tare da samun izinin ainihin mamallakin aikin ba,
Ba ka da hakkin wallafawa ko watsa duk wani irin bayani, ko manhaja ko kuma wasu abubuwa wadanda ke dauke da abin cutarwa ga na’urar kwamfyuta wato bairos ko kuma duk wasu abubuwa masu jawo lahani,
Ba ka da damar wallafawa ko watsawa ko kuma amfani da duk wani bayani ko manhaja ko kuma wani abu mai dauke da tallace-tallace da niyyar kasuwanci,
Ba tilas ba ne ga TRT ta sa ido kan zaurukan, da sauran dandulan tattaunawa, kuma amfani da wadannan zaurukan na nufin ka amince da matsayin TRT na cewa bai wajaba a kanta ta sa ido ba. To amma TRT na da ‘yancin sauyawa, ko gogewa ko kuma yin kari a kan duk wani bayani ko wani abu da wanda ta gag aba dayansa ko kuma wani bangarensa ya saba da ka’idodjin da aka ambata a baya, domin ta ki watsa shi ko ta haramta watsa shi, tare kuma da bayar da sanarwar ko wane irin bayani yayin da aka bukata a hukumance domin bin tsarin shari’a ko na gudanarwa.
Tsaro
Ana bayar da shawara da babbar murya cewa kada ka/ki bayar da lambar wayarku ko ta wani daban da adireshin imel da na gidajenku da makamantansu yayin da kuke mu’amala da zaurukan tattaunawa ko wasu zauruka masu alaka da su domin tsare lafiyarku.
Sharudan da doka ta shimfida
Ba za a watsa duk wani rubutu ko bidiyo ko shiri ko sakon murya da aka jirkita ba a trtafrika.com.
An haramta kitsa aiwatar da zanga-zangar da ba ta halasta ba ko kuma wani shiri ko talla domin aiwatar da zanga-zanga ta amfani da trtafrika.com.
Yana da muhimmanci duk bayanan da masu mu’amala da trtafrika.com za su tura a zaurukan hirarrakin shafin da ma sauran wurare masu alaka da su su kasance sahihan bayanai. Bai kamata bayanan su ci karo da dokokin kasa ko na kasashen duniya (ciki har da a matakin jihohi da kananan hukumomi ) ba ko kuma su saba wa dokar hakkin mallaka.
Kulawar iyaye
Ku nemi amincewar iyayenku kafin ku soma shiga zauruka da sauran kafofin tattaunawa na trtafrika.com idan shekarunku ba su wuce goma sha biyu. Ana matukar shawartar kada ku bayar da bayananku kamar su sunan makarantarku da lambar tarhonku da adireshin gidanku da makamantansu yayin amfani da wadannan wurare.
TRT Podcast
“TRT Podcast” wani tsari ne na TRT, wanda kuke iya samunsa ko ku sauke ko ku kalla da ma saurara ta hanyar shafin intanet na TRT Podcast. Kuna iya amfani da shafin intanet nan TRT Podcast domin samu da sauke ko kalla ko kuma sauraren TRT Podcast da TRT ta samar a na’urarorin da suka dace da tsarin. Dole ne a nuna TRT Podcast a labaran da TRT take bayarwa ta hanyar TRT Podcast. Ba za ku iya ko karawa da rage TRT Podcast ba ta kowacce hanya, ko kuma hada shi da wasu bayanai. Ba ku da ‘yancin amfani da duk wasu bayanai na TRT ko wani tambari nata a na’urorinku ko wani wuri sai dai abin da TRT Podcast da kansa ya samar.
TRT RSS Feeds
“TRT RSS feeds” wani tsarin intanet ne da TRT ke samarwa. Wani tsari ne na RSS da API da ma wasu tsare-tsare da ke ba ku dama wajen samu ko gani ko kuma sauraren shirye-shiryen TRT.
Dole ku nuna cikakken tsarin TRT RSS Feeds da kuka yi sahihiyar rajista da shi a shafinku na intanet.
Mai yiwuwa ba za ku iya canza shi da kara ko rage wani abu a cikinsa kai-tsaye ba, ko kuma samar da takaitaccen bayani na wani shiri na trtafirka.com ko kuma sanya cikakken labara a tsarin TRT HTML. Ba ku da damar yin amfani da duk wani labara na TRT ko tambari a shafinku na intanet ko wani wuri sai bisa tsarin TRT RSS Feed.
Bidiyon da kuka bukata
Video on demand (VoD) na daya daga cikin tsare-tsare da ke bai wa masu mu’amala da mu damar zaba da kuma kallon bidiyon da suke so a talabijin ko kwamfutoticinsu. Kuna iya amfani da wannan tsarin domin kallon dukkan bidiyon da ke trtafrika.com a duk lokacin da kuke so. Ba ku da damar yin amfani da bayanan TRT ko tambarinta a shafukanku na intanet ko wasu wurare a VoD.
Bidiyon Youtube da ake makalawa
Tsarin intanet na TRT yana ba ku damar samun bidiyoyin Youtube da ake makalawa, wadanda masu mu’amala da mu ke iya amfani da su muddin suka bi “Ka’idodjin Amfani” a wannan link din link: https://www.youtube.com/t/terms?gl=CA
Manhajojin TRT
“Manhajojin TRT” wani tsarin intanet ne da TRT ta samar da zai ba ku damar samu da kallo da kuma sauraren labaran TRT. Ana iya amfani da manhajojin ta hanyar kashin kai muddin aka bi “Ka’idojin Amfani”. Ana iya amfani da manhajojin TRT domin sabunta duk wani tsari da TRT ta bayar da damar samunsa ko kallonsa ko kuma saurarensa a kan na’urori. Mai yiwuwa ba za ku iya sauyawa ko karawa da ragewa ko kuma samar da takaitaccen bayani game da duk wani labara ko bayani na TRT a wadannan manhajoji ko kuma wallafa cikakken labara na TRT a tsarin HTML. Ba ku da damar yin amfani da bayanan TRT da tambarinta a kan manhajojinku ko wasu wurare sai dai idan an bayyana hakan a jikin manhajar.
Ba da yawunmu ba
An samar da shafin TRT kamar yadda yake. Doka ta hana a tuhumi daraktocinta da ma’aikatanta da masu samar da labaranta da wakilanta da kawayenta bisa wani abu da ba a fahimta ba. TRT ba ta da hannu game da duk wata illa da aka fuskanta sakamakon amfani da shafinta ko labaranta. Ba za mu ba ku tabbacin cewa dukkan abin da kuka gani a TRT ba za a iya gurbata shi ba. TRT tana yin bakin kokarinta wajen tabbatar da ta bayar da sahihan bayanai kuma gamsassu. Shafin TRT yana dauke da wuraren da za a iya dannawa domin neman karin bayani. TRT ba ta da alhakin duk wani bayani da aka samu bayan danna wurin da za a samu karin bayani.
Iyakar nauyin da ya rataya a wuyanmu
Babu wani yanayi da zai sa TRT da daraktocinta da mambobinta da ma’aikatanta da wakilanta su dauki alhaki na kai-tsaye ko a kaikaice game da duk wata illa, da ta hada da haddasa asara ko bayanan kashin kai da suka same ku sakamakon amfani da bayanai daga wurinmu. Kazalika ba za mu dauki alhaki, ta hanyar sanya hannu a kan kwataragi ko makamancinta ba, sanadin amfani da wasu labarai ko bayanai da kuka samu daga wurin TRT ba. Kuma ba za mu biya diyya ba sakamakon wani abu da ya shafe ku bisa amfani da shafin TRT ba.
Dokokin da suka shafe mu da wuraren shari’a
A yayin da ake yin wata takaddama da ke da alaka da yadda kuka yi amfani da shafinmu, za a gudanar da shari’a ne a Ankara, Turkey. Dokokin Jamhuriyar Turkiye ne za su kasance abin dubawa wajen gudanar da duk wata shari’a, kuma dukkan wadanda ke da ruwa da tsaki a shari’a za su amince a yi shari’a a kotunan Jamhuriyar Turkey game da dukkan rikice-rikicen da ke da alaka da wannan batu. Kazalika TRT na da damar neman kariya daga duk wata kotu.
Takaita dama
Za a aika sakon imel ga masu mu’amala da mu wadanda suka ki amincewa da sharudan amfami da shafinmu da kuma na tsare sirri domin hana su samun damar shiga wasu zaurukan muhawara.
Za a goge duk wasu shafuka na kashin kai da suka bude a TRT idan suka ci gaba da kin bin umarni bayan gargadin da aka yi musu. TRT tana da ikon bai wa wasu bayananku (kamar su hukumomi da ma’aikata da jami’an makaranta dss.) domin hana ku yin abin da bai dace ba a wadannan bangarori.