Ka’idoji tsare sirri
Hadafin wannan manufar ta tsare sirri da sanar da bayanai shi ne, a yi cikakkiyar warwarar bayananku, wadanda Türkiye Radyo Televizyon Kurumu (“TRT”) ke amfani da su, da kuma manufar da ta sanya suke sarrafa su.
Sirrinku na da matukar muhimmanci a wajenmu. Muna tsare tare da kare dukkan bayananku da kuka mika mana, duba da ka’idojin kundin dokar kare bayanan mutum, musamman ma Dokar Kare Bayanan Mutum mai lamba 6698 (PDPL), Dokokin Kare Bayanai Gaba Daya (GDPR) da kuma dukkan ka’idojin da wadannan dokoki suka tattara.
Wadanne bayanan mutum muke tattarawa?
A lokacin da ka yi rajista da TRT; | ||
Nau’ikan Bayanan Mutum da ake Sarrafawa | Bayanin Nau’i | Bangarorin da suka shafi sarrafawa |
Bayanan Mai Amfani | Wadannan bayananku ne da kuka gabatar ko kuma muka tattara domin ku samu damar bin TRT da kuma amfani da shafukanta. Sunayenku, sunan mai amfani, shekaru, jinsi, adreshin e-mail da lambar waya na iya zama abubuwan da za a tattara duba da hanyar bin mu. A wasu kasashen ma, ana iya daukar bayanan lambar dan kasa domin manufofin karbar haraji da bayar da rasiti. Hotonku idan ku dora shi, za a iya amfani da shi. Bayananku da za a diba sun dogara ne duba da shafukan TRT da kuke amfani da su, yadda kuke bude dandalinku, sannan da ko kun shiga da bayananku ko kun yi amfani da hanya ta uku wajen bude dandalinku, (misali, Facebook, Twitter, Google) domin shiga da su da amfani da shafukan TRT dake kansu. Idan kuka yi amfani da hanya ta uku wajen bibiyar TRT, sannan kuka bawa wannan hanya damar ba mu bayananku, to za mu yi amfani da su. | TRT İzle, TRT Dinle, TRT Bil Bakalım, TRT Market, TRT Çocuk Kitaplık, TRT Akademi |
Ta Hanyar Amfani da Kuke da Shafukan TRT; (Ana tattara bayanai game da ku da amfani da shafin da kake yi, cudanyarku da mu da tallace-tallacenmu, da kwamfuta dinku ko sauran na’urori (talabijin din zamani, wayoyin hannu, na’urorin bayar da yanar gizo da sauran na’uroririn sadarwa) da kuke amfani da su don yin amfani da shafukanmu). | |||
Nau’ikan Bayanan Mutum da ake Sarrafawa
| Bayanin Nau’ika | Bangarorin da ake sarrafawa | |
Bayanan Amfani | Bayanan Amfani da Shafi | Za mu iya amfani da bayanau na yanar gizo kamar bayanan URL, bayanan kuki da adreshin IP, lambobin bayanin mutum shi kadai, bayani game da irin na’urar da kuke amfani da ita, nau’inta, tsarin yanar gizon da kuke amfani da shi, (Misali, wireless, 3G, LTE, Bluetooth), sunan wajen da kuke samun yanar gizon da SSID, kamfanin dake ba ku yanar gizon, karfin aikin yanar gizon da nau’ra, nau’in shafin bincike a yanar gizo, samfurin shafin binciken, yaren shafin, hakkin kula da bayanan yanar gizo, karfin kyawun allon na’ura, lokacin yanki, da nau’in yanar gizon TRT; siffofin na’ura (misali, na’urar ID) ko wasu bayyanau na musamman dake kan yanar gizonku wanda zai iya dawa ga yanar gizon TRT (misali, na’urar magana ta zamani, talabijin din zamani, na’urorin yanar gizo da ake amfani da su), siffofin na’urori da manhajoji (misali, nau’insu da yadda ake hada su don amfani), bayanan fara amfani da yanar gizo, alkaluman amfani da shafin yanar gizo, masamar manhajoji (misali, adreshin USL na manhaja), dandalin bincike da bayanan kundin tushen yanar gizo, da kuma taswirar hanya ta uku, ko bigiren da na’Urarku take don gano adreshinku. | TRT İzle, TRT Dinle, TRT Bil Bakalım, TRT Çocuk Kitaplık da sauran shafukan yanar gizo da manhajoji da suke da alaka da TRT. |
Bayanai da Suka Shafi Lokutan Amfani da Shafi | Binciken da aka yi da tarihin binciken da ya wuce (Tarihin abunda ka yi da suka hada da rana da lokacin abunda ka bincika). | TRT İzle, TRT Dinle, TRT Çocuk Kitaplık da sauran shafukan yanar gizo da manhajoji da suke da alaka da TRT. | |
Bayanai masu sauti kamar waka, podcast, sautin murya da littafin sauti da kuke sauraro, da kuma abunda kuke yi a kansa kamar saka shi a jerin sautukan da kuka fi kauna, zabar lokacin sauraro, nuna son sautin ko ma yada shi. | TRT Dinle da sauran dukkan shafukan TRT dake bayar da sakonnin sauti. | ||
Bidiyo ko hoto mai motsi kamar shirin TV mai dogon zango, fina-finai, labaran gaskiya ko shirye-shirye da kuke kallo, da kuma matakin da kuke dauka a kansu, kamar saka su a jerin wadanda kuka fi so, yawan lokacin kallo da tsallake tallace-tallace. | TRT Izle da dukkan shafukan TRT dake bayar da sakonni cikin bidiyo | ||
Wasannin da kuke yi, da matakin da kuke dauka a manhajojin wasannin, kamar sauya dandalin wasan, zabar yadda za ku yi wasan, da sakamakon wasan. | TRT Bil Bakalım, TRT Çocuk Kitaplık da TRT Çocuk | ||
Daukar mataki kan manhajoji kamar wanne littafi aka fi karantawa, lokacin da aka fi dadewa ana karanta littafi, da kuma lokacin da aka dauka wajen amsa tambobyoyin wasa dake karshen littafin, domin samun damar fitar da sakamakon ga iyaye a manhajar. | TRT Çocuk Kitaplık da TRT Çocuk | ||
Sharhi da shawarwarin da kuke bayarwa. | TRT Market, TRT İzle, TRT Dinle, TRT Bil Bakalım, TRT Çocuk Kitaplık, da sauran shafukan yanar gizo da manhajoji da suke da alaka da TRT. |
Bayanan da Kuke Zaba don Ba Mu Su, da Kuma Ba Mu Iziinin Mu samar Muku da Karin Bayanai;s | ||
Nau’ikan Bayanan Mutum da ake Sarrafawa | Bayanin Nau’ika | Bangarorin da ake sarrafawa |
Sayen Bayani | Suna, Sunan Mahaifi, Lambar waya, E-mail, Adireshi | TRT Market, TRT Akademi |
Gasa, Jin Ra’ayi, Sadarwar Yanar Gizo, Caca, Mahadar Bayanan Manhaja da Sadarwa | Muna karba da tattara bayananku (Suna, sunan mahaifi, adireshin e-mail, lambar waya, lambar dan kasa ta Turkiyya da lambar waya don sarrafa hanyar tattara bayanai) da kuke ba mu a lokacin da kuka cike fom, amincewa da aika sako, amsa wani bincike ko tambayoyin jin ra’ayi ko halartar wata gasa. | TRT İzle, TRT Dinle, TRT Bil Bakalım, TRT Çocuk Kitaplık da sauran shafukan yanar gizo da manhajoji da suke da alaka da TRT. |
Ta yaya muke karba da tattara bayananku?
Muna tattara bayananku kai tsaye ta shafukan yanar gizo da manhajojinmu na waya:
- A lokacin da kuka biyo mu don zama mamba,
- A lokacin da kuka yi amfani da kayanmu, manhajoji da shafukan yanar gizo,
- A lokacin da kuka aika da wani bayani zuwa gare mu ta hanyar cike fom ko wata hanya ta daban.
- Za kuma mu iya tattara wadannan bayanai ta hanya ta uku.
Bayanan da Abokan Mu’amala na Uku ke samarwa
Abokan Mu’amala na Uku | Bayanan da aka samar |
Abokan tantance waye mutum | Idan kuka bibiyi ko shiga shafinmu da bayananku ta hanya ta uku, (misali, Facebook), za mu dauki bayananku daga wannan hanya ta uku, domin ku samu saukin bude dandalinku a shafinmu. |
Abokan kula da aiki | Muna aiki tare da abokai don kula da aikinmu, wadanda suke ba mu wasu bayana, kamar hada adireshin IP da bigiren da ake amfani da shafi (misali, gari kasa,), domin mu samu damar gudanar da aikin TRT, bayanai da siffofi. |
Abokan biyan kudi | Idan ka zabi ka biya kudi maimakon rasiti don sayen wani abu, za mu iya neman bayanai daga abokan biyan kudinmu don su aika muku da rasiti, tabbatar da biyan kudin naku, ta kuma mika muku kayan da kuka saya. |
Masu talla da sauran abokan hadin kai | Za mu iya tattara wasu bayanai game da ku, misali bayanan kuki, bayanan wayar hannu, adireshin e-mail da kuma tsoma baki game da abun da kuka fi zaba, daga wajen wasu masu tallace-tallace da abokan tallarmu, don bayar da talla, shirya gangami da turo da sakonni da suka shafe ku, tare da auna tasirinsu. |
Abokan nazari da bincike kan aiki | Za mu iya tattara bayanai daga abokanmu huldarmu ta fuskar nazari da bincike kan aiki da shafukanmu, domin taimaka mana wajen sanin masu amfani da shafukan yanar gizonmu, manhajojinmu da maziyartanmu, haka kuma domin sanin mene ne masu amfani da shafukanmu suke tsammani daga wajenmu, don bayar da gudunmowa ga cigaban abubuwan da muke gabatarwa, da kuma domin daukar matakan da suka dace wajen bayar da garabasa da tallace-tallace. |
Manufofinmu na Sarrafa Bayanai da Madogarar Shari’a Kan Sarrafawar
Muna sarrafa bayananku duba da ka’idojin gama-gari da sukekarkashin sashe na 4 na kundin PDPL da sashe na 5 na kundin dokar GDPR, da kuma aiki da sharuddan amfani da bayanan mutum dake karkashin PDPL da GDPR.
Bayan mutum da ake sarrafawa | Manufarmu da ta sa muke sarrafawa | Madogarar shari’a |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanan Saye da Sayayya, Gasa, Jin Ra’ayi da Caca. | Domin samarwa da kula da aiyukan TRT (misali, shafukan yanar gizo, manhajoji, shafukansada zumunta da sauran su), domin samar da bayanan kimiyya da kididdiga da kyautata kayayyakinmu da aiyukanmu yadda ya kamata, don kara gamsuwa game da aiyukanmu, da kuma tsara yadda maziyarta ke amfani da shafukanmu yadda ya dace | A lokacin da ya zama dole a yi amfani da bayanan wani ko kamfani da aka kulla yarjejeniya da su, domin aiki ko tabbatar da wannan yarjejeniya A lokacin da ya zama lallai ala tilas a yi amfani da bayanan mutum domin halascin tsarin dake kula da bayanan, matukar dai an tabbatar da ba za a cutar ko tauye hakkokin dan adam da suka shafin bayanan ba Bayyanar amincewa karara |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani | Don fahimta, ganowa da magance matsaloli, da kuma warware matsaloli game da aiyukan TRT | A lokacin da ya zama dole a yi amfani da bayanan wani ko kamfani da aka kulla yarjejeniya da su, domin aiki ko tabbatar da wannan yarjejeniya A lokacin da ya zama lallai ala tilas a yi amfani da bayanan mutum domin halascin tsarin dake kula da bayanan, matukar dai an tabbatar da ba za a cutar ko tauye hakkokin dan adam da suka shafin bayanan ba |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani | Domin nazari da cigaban manhajoji, fasahar kere-kere da kyautatuwar aiyukan TRT. | A lokacin da ya zama lallai ala tilas a yi amfani da bayanan mutum domin halascin tsarin dake kula da bayanan, matukar dai an tabbatar da ba za a cutar ko tauye hakkokin dan adam da suka shafin bayanan ba |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanan Saye da Sayayya | Domin sadarwa ta duk wata hanyar sadarwa, a wani bangare na aiyukan cikin gida da cigabansu, da kuma aiyukan shirye-shirye, don manufofin tallatawa, bayar da ciyarwa gaba da tallace-tallace. | Wanzuwar amincewa karara |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanan Saye da Sayayya, Gasa, Jin Ra’ayi da Caca. | Domin aiki da abun da doka ta tanada, da bukatar hukumomin tabbatar da an yi aiki da dokoki. | A lokacin da amfani da bayanai ya zama dole domin a tabbatar da an yi aikki da abubuwan da doka ta tanada, wanda suka shafi tsarin kula da bayanan |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanan Saye da Sayayya | Domin tabbatar da an yi aiki da yarjejeniyar da aka kulla da bangare na uku, 8misali, yarjejeniyoyin lasisi) da kuma daukar matakan da suka dace game da rahotannin da suke bayarwa. | A lokacin da ya zama lallai ala tilas a yi amfani da bayanan mutum domin halascin tsarin dake kula da bayanan, matukar dai an tabbatar da ba za a cutar ko tauye hakkokin dan adam da suka shafin bayanan ba |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanan Saye da Sayayya, Gasa, Jin Ra’ayi da Caca. | Domin shigar da kara, don gamsar da karar ko kuma kare kai daga karar. | A lokacin da ya zama tilas a yi amfani da bayanan mutum don karbowa, tabbatarwa ko kare wani hakki, |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanan Saye da Sayayya, Gasa, Jin Ra’ayi da Caca. | Don yin shirin kasuwanci; don adanawa, warwara, bayar da rahoto da yin hasashe duba da bayanan dake hannu domin hana bacewar bayanai. | A lokacin da ya zama lallai ala tilas a yi amfani da bayanan mutum domin halascin tsarin dake kula da bayanan, matukar dai an tabbatar da ba za a cutar ko tauye hakkokin dan adam da suka shafin bayanan ba |
Bayanin Mai Amfani, Bayanin Sayayya | Gudanar da saye da sayarwa. | A lokacin da ya zama dole a yi amfani da bayanan wani ko kamfani da aka kulla yarjejeniya da su, domin aiki ko tabbatar da wannan yarjejeniya A lokacin da amfani da bayanai ya zama dole domin a tabbatar da an yi aiki da abubuwan da doka ta tanada, wanda suka shafi tsarin kula da bayanan |
Bayanan Mai Amfani, Bayanan Amfani, Bayanin Gasa da Jin Ra’ayi | Don shirya bincike, gasa, jin ra’ayi da caca. Domin karbar bukatu don halartar irin wadannan tarukan horaswa da karawa juna sani. | A lokacin da ya zama dole a yi amfani da bayanan wani ko kamfani da aka kulla yarjejeniya da su, domin aiki ko tabbatar da wannan yarjejeniya A lokacin da ya zama lallai ala tilas a yi amfani da bayanan mutum domin halascin tsarin dake kula da bayanan, matukar dai an tabbatar da ba za a cutar ko tauye hakkokin dan adam da suka shafin bayanan ba A lokacin da ya zama tilas a yi amfani da bayanan mutum don karbowa, tabbatarwa ko kare wani hakki, |
Aika Bayanan Mutum
Muna aikawa da bayanan mutum da muka yi amfani da su zuwa ga abokan mu’amala domin gudanar da kasuwanci, da kuma bawa mahukunta da hukumomin gwamnati izini, domin tabbatar da mun yi aiki da doka da oda.
Adanawa da Lalata Bayanan Mutum
TRT na adana bayanan mutum duba da manufar sarrafa su. Ana aiki da dukkan tanade-tanaden PDPL da GDPR don tabbatar da kariya da tsaron bayanan.
A lokacin da manufar amfani da bayanan mutum suka kau ko suka zo karshe, ana dana bayanan har zuwa lokacin da doka ta tanadi a ajje su, sannan muma muna duba ga hakkokinmu na doka da shari’a. A lokacin da dalilin adana bayanan mutum suka gushe, to ana lalatawa da zubar da wadannan bayanai da zarar damar da doka ta bayar na rike su ta zo karshe ita ma.
Batutuwa Masu Muhimmanci Game Da Yara
TRT na nuna matukar kulawa game da kare bayanan yara kanana. Duba da yadda yake da wahala a iya sanya idanu kan yara kanana a yanar gizo, dole ne iyaye su dinga kula da yanar gizon da yaransu za su amfani da su, kuma iyaye su bayar da izininsu karara, a lokacin da aka nemi a bayar da izini karara.
Hakkokin Bayanan Mutum (Wanda Abun Ya Shafa)
Kowa yana da wadannan hakkoki dake kasa duba da sashe na 11 na dokar PDPL:
1. Su san ko ana amfani da sarrafa bayanansu ko kuma akasin haka.
2. Za su iya neman bayanai game da hanyar da aka bi, idan har an yiamfani da bayanansu.
3. Za su iya neman bahasi kan manufar amfani da bayanansu, da kuma ko an yi amfani da su da wannan manufa.
4. Mutane na da hakkin samun bayanai game da hanya ta uku da aka mikawa bayanansu a cikin gida ko a kasar waje.
5. Idan ba a iya amfani da bayanan mutum gaba daya kuma ba daidai ba, za a iya neman a gyara, sannan kuma a sanar da wasu na daban da aka aikawa bayanan game da wannan gyara da aka yi.
6. A yanayin da aka yi amfani da bayanan mutum duba da tanade-tanaden kundin doka na PDPL da sauran dokoki, sai kuma dalilan da suka sanya aka yi amfani da su suka gushe; za su iya neman bukatar a goge bayanansu, sannan a tabbatar da an sanar da bangare na uku ya goge bayanan shi ma.
7. Za a iya nuna rashin amincewa sakamakon bayyanar wani sakamako dake cutar da mutumin da aka sarrafa bayanansa, a lokacin da ake amfani da su ta hanyar aiki da na’ura.
8. Mutane za su iya neman a biya su diyya don cutarwar da aka yi musu sakamakon amfani da bayanansu da aka yi ba bisa doka ba.
Za ku iya aiko mana da tambayoyinku a karkashin sashe na 11 na kundin dokokin PDPL “dake kula da hakkokin sarrafa bayanai” duba da Sanarwar Bayan Taro kan Ka’idoji da Hanyoyin Sarrafawa da Kula da Bayanai . Za a duba bukatun naku sannan a yanke hukunci kyauta kuma cikin kankanin lokaci, amma ko an dade ba za a wuce kwanaki 30 ba. Idan har ta kama wannan nazari da hukuncin da za a yanke na bukatar kashe kudi, to za a yi amfani da farashin da Hukumar Kula da Kare Bayanai ta bayyana.
Hakkokinku duba ga kundin doka na GDPR
A matsayin daidaikun mutane, kuna da wasu hakkoki game da yadda muke sarrafawa da amfani da bayananku, hakkokin sun hada da shigar da korafi ga hukumomin dake sanya idanu.
A karkashin GDPR, kuna da hakkoki da suka hada da:
● Hakkin samun bayanai- Kuna da hakkin ku tambaye mu kwafin bayananku. Wannan zai ba ku damar samun kwafin bayananku da muke rike da su game da ku, sannan ku ga yadda muke amfani da su bisa doka da oda.
● Hakkinku na neman gyara- Kuna da hakkin ku nemi mu gyara wasu bayananku da suke ba daidai ba. Sannan kuna da hakkin ku nemi mu cika bayananku da ba su cika ba.
● Hakkinku na a goge- Kuna da hakkin ku nemi mu goge bayananku a wasu yanayi. Wannan na ba ku damar ku nemi mu goge bayananku a lokacin da babu wani dalili da zai sanya mu ci gaba da amfani da su. Sannan kuna da hakkin ku nemi mu goge bayananku gaba daya idan ba kwa son mu yi amfani da su. (Duba nan kasa).
● Hakkinku na hana sarrafa bayanai- A wasu lokuta ko yanayi, kuna da hakkin ku nuna rashin amincewa da amfani ko sarrafa bayananku ( a inda muka dogara kan halastaccen batu (ko na hanya ta uku), sannan aka samu wani abu da ya shafi wani hali da kuke ciki wanda ya sanya ku nuna rashin amincewar). Sannan kuna da hakkin nuna rashin amincewa da sarrafa bayananku a lokacin da muka yi amfani da su wajen talla kai tsaye.
● Hakkinku na takaita sarrafawa- Kuna da hakkin ku nemi mu takaita sarrafa bayananku a cikin wani yanayi.
● Hakkin neman tura bayanai- Kuna da hakkin ku nemi mu aika bayananku da muka sarrafa zuwa gare ku ko wata hukuma.
Ba za a nemi ku biya wani kudi ba don neman hakkokinku. Idan kuka nemi wani abu, muna da tsawon wata guda don ba ku amsa.
Bayanin Wanda Ke Kula Da Bayanai
Suna : Türkiye Radyo Televizyon Kurumu
Shafin Yanar Gizo : www.trt.net.tr
Lambar waya : 444 0 878
Adireshin e-mail : [email protected]
Adireshi : TRT Sitesi Turan Güneş Bulvarı 06540 Or-An Ankara