Gwamnatin Trump ta yi amfani da zarge-zargen da babu su na harar manoma farar fata da gwamnati kenyi din kawai ta kaddanar da nata hari a kan gwamnatin.

Donald Trump da Elon Musk sun yi kokarin bakantawa tsagin siyasa a Afirka ta Kudu a yayin da kasar take kokarin daidaita bakake da farare ta hanyar zaman lafiya, kwanciyar hankali da adalci, da kuma kawar da rashin adalci da daidaitin daka samar a baya.

Gwamnatin Trump ta yi amfani da zarge-zargen da babu su na harar manoma farar fata da gwamnati kenyi din kawai ta kaddanar da nata hari a kan gwamnatin.

A yayin yin hakan, ya samar da saka rai na karya ga wasu kungiyoyin kamun kafa din cim ma sakamakon siyasa da suke so duk kuwa da daidaiton jiga-jigan siyasa a kasar.

Kungiyoyin kamun kafar da a koyaushe ke kirkirar tsoron farar fata a Afirka ta Kudu, na sake amfani da wannan dama a yanzu haka. Sun yi tsammanin za su iya kara wa da karfin zaba niyar gwamnatin dimokuradiyya tare da barazanar siyasar da ke fito wa daga Washington.

Sai dai kuma, matakain nasu ya fuskanci martani daga dukkan bangarorin jama’a - wasu ma masu tsananin sukar gwamnatin Afirka ta Kudu ne - nan da nan suka koma masu kare gwamnati saboda fahimtar cin duduniyar kasar da Trump da Elon Musk ke yi.

Shafukan sada zumunta da ma manyan kafofin yada labarai na cika da masu mayar d amartani, manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasa gama-gari na ta sukar dabarunTrump wanda ke kare manufofin Elon Musk da Benjamin Netanyahu.

Musk ya zautu da yadda gwamnatin Afirka ta Kudi ta nace kan sai kamfaninsa na Starlink ya yi aiki da dokar karfafawa bakar fata kafin a ba shi damar shiga kasuwannin kasar.

A nasa bangaren, Netanyahu na bata ransa saboda saboda karar da Afirka ta Kudi ta kai Isra’ila Kotun Kasa da Kasa bisa zargin aikata kisan kiyashi a Gaza.

‘Yan Afirka ta Kudu na ta fadin cewar zumudin Washington ba shi da wata alaka ta goyon bayan fararen fata tsiraru na kasar da ake cewa an mayar saniyar ware, wadanda suna rayuwarsu cikin jin dadi a manyan gidaje na hutu.

Ba za iya tafiya Amurka da suna gudun hijira su bar wadannan manyan dukiyoyin nasu ba. Duk da cewa ba su wuce kashi 8 na jama’ar Afirka ta Kudu da ke da yawan mutane miliyan 63, fararen fatar su ne mafiiya arziki da wadata.

A gefe daya, Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashen duniya da ke da farar fata Turawa ‘yan kama wuri zauna, wadanda gaamnatocinsu suka karkashe kabilu, kisan kiyashi da sauran keta hakkokin dan'adam, kuma ake ci gaba da kallon su a matsayin ‘yan kasa masu ‘yanci kamar sauran bakaken fata mafi rinjaye.

A saboda haka, suna gida a Afirka ta Kudu, kasar da da yawa ke kira gidansu tun 1600 da aka fara mulkin mallaka.

A wani waje a nahiyar, jama’ar Turawa ‘yan kama wuri zauna sun bar wuraren bayan samun ‘yancin kasashen, saboda yadda shugabanci ya koma hannun ‘yan kasa da suka jagoranci gwagwarmayar korar masu mulkin mallaka.

An ga mu’ujiza wajen mika mulki a Afirka ta Kudi a shekarun 1990.

A 1994 an gudanar da zabe na dimokuradiyya, an samar da sabon kundin tsarin mulki da ale yi wa kallon ya fi kowanne kyau a duniya a 1996, kuma tun wannan lokacin kasar ke yin zabuka lami lafiya.

Wani babban bangare a kudin tsarin mulkin Afirka ta Kudi shi ne dikar hakkokin dan adam, kuma bangarori da dama na dokar sun bayyana daidaito da ‘yancin ‘yan kasa, hakkin mallakar kasa da bukatar gwamnati ta yi duk mi yiwuwa don kawar da bambancin daidaito da ke tsakanin bakake da fararen fata a kasar.

Kundin tsarin mulki ya tanadi daidaito tsakanin ‘yan kasa da kuma rabon arziki daidai.

A tsawon lokacin dimokuradiyya, kotunan kasar sun zama muhimman jigogin siyasa da dimokuradiyya, an yaba musu saboda warware rikicin siyasa da ake kawo musu ba tare da numa bangaranci ba, inda ake kalubalantar gwamnati ma.

Gwamnati ta sha yin rashin nasara a manya da kananan kotuna a fadin kasar.

‘Yan kasa gama-gari, jam’iyyun adasa, kungiyoyi masu kare manufofinsu, da ‘yan kasuwa sun samu damar kai kara da kalubalantar gwamnati tare da yin nasara a kotunan.

Kotunan sun dinga hana bangaren zartarwa da na majalisa daga amfani da larfinsu ta mummunar hanya, har ta kai ga suna bata wa manyan jami’an gwamnati rai, wadanda ke tunanin ‘yan adawa ne ke juya kasar.

A tsarin dimokuradiyya na gaskiya, jam’iyya mai rinjaye ce ke yin dokokin da take tunanin za su taimaka mata wajen cim ma muradunta na siyasa da cigaban tattalin arziki inda ‘yan adawa ke amfani da kotuna wajen kalubalantar matakan da suka saba wa kundin tsarin mulki.

Wannan ne salon dimokuradiyya a Afirka ta Kudi.

Saboda haka, abu ne mai kyau yadda Shugaban Kasa Cyril Ramaphosa ya bayyana cewar Washington na son tirsasawa Pretoria ta janye dokar mallakar kasa da karar kisan kiyashi da Afirka ta Kudu ta kai Isra’ila amma matakin “ba zai yi nasara ba”.

TRT Afrika