Daga Burak Elmali
Taron NATO da aka kammala kwanan nan a Vilnus ya tabo wasu batutuwa na matsin lamba – kamar su yakin Rasha da Yukren, bukatar Sweden na zama mamba, karfafa alaka da Yukren, da kuma karfafa alakar tsaro da kawayensu na Asiya.
Wani abu da ke jan hankali shi ne, sanarwar bayan taro mai sakin layi 90 da aka fitar ta ambaci China sosai wanda hakan ke nufin an tattauna kan kasar a yayin taron.
Amma kuma, wata babbar tambaya ita ce: Shin kalubalantar China zai zama abu mai sauki kamar yadda manazartan NATO ke bayyanawa?
Kamar yadda aka zata, China ta fassara wannan sanarwa ta fuskar yakin cacar baki. Bangaren China ya yi amfani da wannan dama wajen jaddada adawarta ga duk wata mamaya da za a yi wa gabashin duniya zuwa ga yankin Asia-Pacific, inda ta ce “Duk wani abu da zai taba ikon China to za a mayar da martanin da ya dace.”
A lokacin da China ke kokarin nuna kanta a matsayin kawar makotanta na yankin Asia-Pacific, kasashe makota na kallon ayyukan China da manufofinta na kasashen waje a matsayin barazana gare su, wanda hakan ke sanya wasu kusantar kawancen NATO.
Amma kuma, wasu a yammacin duniya har yanzu wasu na kwala kawunansu a kasa, suna nuna aminta da siyasa ta zahiri, suna fassasa al’amura a matsayin ‘dimukradiyya’, inda suke nisantar makotansu da bas a dabbaka dimukradiyya.
A yayin da irin wannan abu ke da tasiri sosai a shekarun 1990, a lokacin da Amurka ke jagoranci a matsayin mafi karfi a duniya, kuma abun ban mamaki ne a ce a yau za a iya nuna aikin wannan tsari a Gabashi da Kudancin tekun China.
Ba tare da duba ga wadannan bayanai ba, sako na karara shi ne an fara wasa dora laifi a kan abokin hamayya, inda dukkan bangarorin biyu ke nuna wa juna yatsa.
Amurka da ‘yan kanzaginta na amfani da bayyana China a matsayin kalubale gare su, wajen samun karfin fada a ji a Asiya.
Batun shi ne, wannan yunkuri na iya zama na kai tsaye, amma kuma kuskure ne a bayyana yana da sauki tunkarar China a yau.
Manyan kalubaloli
A matsayin kawancen tsaro, dole NATO su magance manyan kalubalane da ke gabansu kan wannan aiki mai rikitarwa. Dole ne ta magance barazanar gaza ayyuka kai hade, inda tabbatar da aminci da rage yawan rabuwar kai suka zama wajibi matukar ana son a cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Amma fa a sani kasashe mambobin NATO bas u da kauli daya ko fata iri daya kan wannan batu.
Misali, Faransa – ta samu zuba jari mai yawa daga China - shi ya sa ba ta son shiga duk wani abu da zai bakantawa China rai musamman kan batun Taiwan. Hakan ya sanya Macron ya yi watsi da bukatar kafa ofishin sadarwa na NATO a Japan.
Idan za balle daga jinginuwa da tattalin arzikin China, to za a yi tafi tare da Tarayyar Turai kenan. Babbar alakar kasuwanci ta China da daidaikun kasashe mambobin NATO da kuma a dunkule ta hanyar Tarayyar Turai ne ya sanya kamar abun da ake so a yi ba zai yiwu ba.
Kokarin da aka yi a baya ya rage dogaro kan makamashin Rasha bayan fara rikicin Yukren.
Lalata kasuwancin dala biliyan $943 da ke tsakanin China da Tarayyar Turai zai cuci dukkan bangarorin biyu ne.
Masu zuba jari na Turai da mahukunta ba sa gaggawar zuwa ga lalata wannan tsari da kawance na kasuwanci.
Shugaban Zartarwa na kamfanin Jamus na Merck, Belen Garijo na bayyana ba zai yiwu a wargaza kasuwancin ba, wannan zai dauki shekaru ashirin kafin ya tabbata.
Haka kuma, Shugaban Kungiyar masu Masana’antu na Jamus (DIHK) ya bayyana shakku game da yanke kasuwanci da China, inda ya jaddada bukatar da ke akwai na magance dogaro kan wasu da kuma hatsarin da ake fuskanta.
‘Yan kasuwar Jamus na adawa da wannan abu, duba da yadda Jamus ta zama cibiyar tattalin arziki a kasashen Tarayyar Turai.
Duba da wadannan damuwa da aka zayyana, kalubalantar China ba tare da yin wani kwakkwaran shiri ba, zai kawo hatsari da illa ga Amurka, saboda yadda kawayenta na Turai ba su shirya shiga wannan rikici ba.
Abokai da makiya
Kamar yadda aka gani, sanarwar bayan taron NATO mai sakin layi 90 ta jaddada muhimmancin sulhu.
A wannan gaba, saboda wasu dalilai na siyasa, shugaban Amurka Joe Biden na kiran Xi Jinping a matsayin ‘dan kama karya’, dukkan bangarorin biyu ba su so abun ya ta’azzara ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya sha nanata biyayya ga manufar China ita kadai, inda babu batun amincewa ga samun ‘yancin kan Taiwan.
Amma kuma, NATO za ta fadada kawancenta a Asiya a nan gaba, ba tare da mika wa kasashen neman su zama mambobinta ba. Wannan yunkuri ya danganci gamsuwar kawayen Amurka a yankin Pacific kan fadadar hadin kansu da tare da zamam mambobin na NATO ba.
Ziyarar firaministan Indiya Nerendra Modi zuwa Fadar White House na nuni da hakan.
Wasu makotan China na bibiya da sanya idanu kan wannan wabuwar dabarar kulla alakar da aka samar. Sanarwar da aka fitar a hukumance kan ziyarar Modi – wadda ta bayyana mafi kankantar damuwa kan ‘yan kishin kasa mabiya addinin Hindu da suke rike da gwamnati kuma suke nuna wariya ga marasa rinjaye – na nuni da lalacewar dimukradiyya da yadda akw amfani da ita wajen take hakkokin wasu da goyawa wasu baya.
Akwai misalai makamantan wannan da za su iya jan hankalin wasu kasashen Asiya su kara karfafa dabarun kulla alaka da Amurka don kalubalantar China.
A wajen China, lokaci na da muhimmanci. China amfani da duk wata sa’a wajen amfani da kudadenta tana karfafa karfin tattalin arziki da sojinta.
A yayin da babu yiwuwa gwabza yaki kai tsaye da China saboda Taiwan, China na amfana da duk wani jinkiri d aAmurka ke yin a mamayar Asiya.
Duk da mamayar Asiya ga NATO abu ne da ba zai yi wu a nan kusa ba, kara hadin kan soji da musayar bayanan sirri zai zama babban abun mayar da hankalin China.
A saboda haka, Dakarun ‘Yantar da Jama’a za su ci gaba da gwada kwanji a yankin Taiwan.
Marubucin wannan makala Burak Elmali, mai bincike ne a Cibiyar Bincike ta TRT World da ke Istanbul. Ya yi digiri na biyu a Alakar Kasa da Kasa daga jami’ar Bogazici. Bangaren da ya fi gudanar da bincike a kai su ne manufar Turkiyya a kasashen ketare da siyasar mamayar siyasa wajen mayar da hankali kan alakar Amurka da China da yadda hakan ke tasiri a yankin Gulf.
Jan hankali: Ra’ayin da wannan marubuci ya bayyana ba lallai su zama ra’ayin TRT Afirka ba.