Daga Ovigwe Eguegu
Ga duk wani mai sa ido kan lamura, tsarin gudanarwa na duniya da kuma alaka Ta kasa da kasa na sauyawa.
A yammacin duniya, gwamnatocin kasashen da ke kudancin nahiyar Amurka suna kaurace wa shugabancin kasar Amurka.
A nahiyar Asiya, akwai yadda kasar China ta yi fice a duniya, kuma yadda ake barin shugabancin yankin Turai zuwa tsarin duniya mai shugabanni da dama da ya mayar da hankali kan ‘yancin kai na kasashe.
A wannan makalar, manufarmu ita ce a fahimci muhimmancin Afirka ga abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman yadda gwamnatocin kasashen nahiyar suke sauyawa don dacewa da yadda wadannan abubuwan ke sauyawa.
Sannan mu yi duba kan abun da ya kamata a yi don kasancewa a bangare mai karfi nan gaba.
Masu sharhi da kuma masu tsare-tsare sun yi imanin cewar ana sabon wawaso kan Afirka, kuma a wannan tsarin, kasashe masu karfi a duniya sun mayar da hankali ne kan yadda za su tsare hanyar samun muhimman albarkatu don cigaba da kuma kera fasahar da ke habaka fasahar zamani.
Alal misali, a cikin wasu takardun a manufofinta, Amurka ta bayyana muhimmancin tsare hanyar samun muhimman ma’adinai da ke da yawa a Afirka irin su jan karfe da karfen lithium na hada batur.
Kazalika kasar China, wadda take da alaka ta da-kut kan harkokin tattalin arziki da kasashen Afirka wadanda suka bude wa tattalin arzikin kasar China din hanya.
Wadannan su ne abokan hamayya na tattalin arziki, amma tambayar ita ce: Me gwamnatocin Afirka za su iya cewa game da wannan?
Zimbabwe ta yi yunkurin sarrafa muhimman ma’adananta irin su karfe da kuma karfen platinum a gida.
Nijeriya ta ayyana karfen lithium dinta a matsayin muhimman ma’adinai, kuma kasar Gini ta sake dabara kan yadda za ta yi amfani da ma’adinanta yayin da take kare muradun kasar.
Yayin da ake maganar “sabon wawaso kan Afirka," gaskiyar lamarin ita ce gwamnatocin kasashen waje ba su da ‘yancin duba abin da suke so, sabanin yadda lamarin yake a taron Berlin da aka yi a cikin zafin yakin Cacar Baka.
Yadda yanayin siyasar Afirka take a yanzu ‘yan Afirka ba sa son abin da zai bata muhalli, raba mutane da gidajensu da kuma matsalolin da aka fuskanta a karni na 19 da na 20 da sunan cigaba na masana’antu.
A yanzu kasashen Afirka da yawa sun fara fifita kansu duk da cewa sun san kasuwanci a yanzu abu ne da ake yi da duniya gaba daya.
Harkar siyasar a yanzu na nuna cewa gwamnatocin Afirka suna da damar tsara yanayin harkar diflomasiyya, lamarin da ke nuna cewa alal misali an sauya yanayi na cinikayya da diflomasiyya tsakanin Mali da Faransa.
A halin yanzu Washington tana kara kokarin diflomasiyya don kara samun goyon baya a nahiyar.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyara wasu kasashen Afirka inda ya yi magana a kan bukatar da ke akwai ta sarrafa ma’adanai a karkashin jagorancin Amurka, cikin kasashen nahiyar Afirka.
China ma wata hanya ce da za a iya duba wannan maganar, saboda Beijing ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ga Afirka cikin ‘yan shekarun nan.
Wannan kuma ya sa ta kasance zabin da shugabannin Afirka suka fi so.
Bugu da kari, gwamnatocin Afirka kamar na Burundi da Habasha da kuma Nijar suna amfana da ragin kashi 98 cikin 100 na harajin fitar da kaya zuwa China a wani yunkurin Beijing na kara abubuwan da take shigarwa da su daga Afirka.
Tanzaniya da Uganda ma sun fara amfana da tsarin da ya cire haraji daga kan wasu kayayyakin da za su fitar zuwa China.
Ta hanyar amfani da tsarin da ya kunshi abubuwa sama da 8,800, China tana kokarin habaka yawan abubuwan da take shigowa da su daga Afirka zuwa dala biliyan 300 nan da shekarar 2025.
Abin lura a nan shi ne yayin da kasashe masu karfi irin su Amurka da China ke neman kara tasiri cikin gwamnatocin Afirka.
Kasashe a nahiyar sun samu sabuwar damar sauya abokan cudanya, musamman idan ana tunani kan amfanin tattalin arzikin da za a samu a dangantaka tsakanin Afirka da China.
Daga tsarin yafe bashi da kuma fitar kaya zuwa China ba tare da haraji ba, gwamnatocin Afirka na da ikon yin tasiri kan hamayyar kasashe masu karfi da kuma yiwuwar iya sauya yanayin yadda duniya take kallon inda jargoranci yake.
A harkar ruwa ma, nahiyar Afirka ta nuna cewa tana da karfin iya yin tasiri a yadda ake gudanar da duniya.
Idan aka yi la’akari da cewar hanyoyin ruwa irin su Suez Canal da ke kusa da Masar da kuma sashin tekun Bad-el Mandeb da ke kusa da yankin kusurwar Afirka, wanda ke yi wa Turai da Asiya hidima ta fagen mai da iskar gas.
Kasashen Afirka sun yi yunkurin inganta karfinsu na iya tinkarar barazanar fashin teku yayin da suke da ‘yancin kai wajen ayyana muradunsu na waje.
Akwai kasashe da dama da ke wawaso kan kifaye da makamashin gas da ke wasu wurare irin su gabar tekun Guinea da kuma yankin kusurwar Afirka.
A wannan yanayin, inganta hadin kai wajen gudanarwa a nahiyar ka iya sa albarkatun ruwa na nahiyar Afirka su kawo amfani mai dorewa ga nahiyar.
Alal misali an rattaba hannu kan yarjejeniyar Yaounde ne tsakanin kasashe 25 a shekarar 2013 don samun karin hadin kai wajen musayar bayanai da katse matsala da kuma bincike.
Ana hakan ne duk don a dakile barazanar tsaro irin su fashin teku da fasa kwabri da kamun kifi ba bisa ka’ida ba da kuma gurbata yanayi
Irin wannan hadin kan, duk da cewa ana yaba masa, bai samar da abin da ake bukata ba, kamar yadda wani rahoton cibiyar nazarin harkokin kasashen duniya ta Chatham House ya bayyana.
Rahoton ya ce garkuwa da mutum 130 da aka yi daga cikin 135 a duniya gaba daya ya faru ne a gabar tekun Guinea.
Amma an alakanta irin sakamakon da yarjejeniyar Yaounde ta samar da yadda yarjejeniyar ta zama wadda ba dole ne a bi ta ba da gibi na kudi da kuma kwarewa na aiwatarwa.
Yayin da gwamnatocin Afirka suka fara kaddamar da tsare-tsaren habaka tattatlin arziki mai alaka da ruwa, za su iya kasancewa abokan hamayyar wasu kasashe masu karfi.
akan kuwa zai faru ne saboda yanayin gudanarwa na kasashen da ke makwabtaka da juna ka iya tasiri kan huldar kasa da kasa da ta shafi harkar ruwa.
A takaice abubuwan da ke faruwa a halin yanzu, kamar yadda muka ambata cikin wannan makalar, sun nuna cewa duniya tana juya akalarta daga kasancewar wadda Amurka ce kawai take jan ragamarta, zuwa wacce kasashe daga nahiyar Asiya da nahiyar Kudancin Amurka da kuma nahiyar Afirka ke samun karfin fada a ji kan yadda ake gudanar da ita.
Wannan ya kawo wa Afirka sabbin abubuwan da za ta iya samu yayin da gwamnatocin cikin nahiyar ke taka sababbin rawa a harkar siyasar duniya, kamar yin tasiri kan iya ba da damar samun muhimman ma’adinai da kuma wasu albarkatun.
Wannan tasirin a kan yadda ake gudanar da duniya ya bayyana a harkokin kasashen duniya irin su taron gama-gari na mambobin MDD, da kuma damar habakar kungiyoyi kawancen kasashe irin su BRICS da EAC da kuma kawancen kasashen ‘yan ba ruwanmu.
Daga neman karin yawan wakilci a taron kasashe masu karfin tattalin arzki na G20 da kuma kwamitin tsaro na MDD, Afirka tana kara matsawa daga matsayin mai kallo kawai zuwa matsayin mai taka rawar gani.