Daga Makhosonke Buthelezi
Bayan taro karo biyar na kungiyar kasashe masu habbakar tattalin arziki (BRICS) kan matasa a birnin Johannesburg a farkon wannan watan, wakilan matasa na kungiyar kasashe ta BRICS da kuma kasashe da ke Kudancin Duniya, sun tattauna kan yadda za su magance matsalar makamashi.
Taron kwana biyun ya samu halartar fiye da wakilai 250 daga kasashe 17 kuma ya kasance wani bangare na shirye-shirye taron BRICS karo na 15 daga 22 zuwa 24 ga watan Agusta a Afirka ta Kudu.
Yayin da yake jawabin bude taron, Darakta Janar na Bangaren Albarkatun Makamashi (DMRE) Mista Jacob Mbele ya bayyana babban taron "a matsayin wata damar tattaunawa da kuma samar da makamashi a duniya da kuma hanyar samar da amfani da makamashi da fasaha."
Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Afirka miliyan 600 ba sa samun tsaftataccen makamashi.
Makoma mai kyau
Ko da yake bangaren matasa na kungiyar BRICS ya bukaci shugabannin kasashe mambobin kungiyar da kuma shugabannin sauran kasashe da kungiyoyi da su kula da kalubalen da ke tattare da makamashi da ke damun nahiyar Afirka.
Ya kamata kuma su nuna goyon baya ga ci gaba da aiwatar nazarin binciken BRICS kan Afirka, bunkasa kwarewa da kasuwanci da yada fasahar makamashi da musayar dalibai da sauransu, inda za a bai wa matasa fifiko.
“Mun yi tsayuwar daka don warware matsalolin makamashi saboda kokarinmu na cimma maradu masu dorewa da samar da kyakkyawar makoma ga kasashenmu da Kasashen Kudancin Duniya da kuma gaba daya duniyar," kamar yadda matasan suka ayyana.
Yayin batutuwan da aka tattauna suka fi mayar da hankali kan warware matsalar karancin makamashi ga mambobin kungiyar BRICS, wakilai sun jaddada muhimmancin makomar makamashi a Afirka, ta yadda za a samar da makamashi mai tsafta da sauki kuma mai dorewa.
Ware kudin kula da yanayi
Kafin hakan ya faru, akwai bukatar samar da bangaren makamashi na zamani, kuma ya zama mai dorewa.
Muhimmin batu da aka tattauna kan makamashi shi ne alakar sauyin yanayi da bukatar kudi don samar da hanyoyin samun makamashi mai dorewa.
Daga wannan mahangar, matasa sun jaddada muhimmancin ware kudi kan sauyin yanayi kuma ta haka ne za su taimaka wajen koma wa hanyoyin samar da makamashi mai dorewa da kuma bai wa matasa damar sarrafa kudin.
"Mun bukaci kasashen kungiyar BRICS da su hada kai kuma su ware wasu kudade a cikin gida da kuma a ketare don tallafa wa ayyukan samar da makamashi mai tsafta da abubuwan more rayuwa da kananan kamfanonin fasaha da rage tasirin sauyin yanayi," kamar yadda matasan suka bayyana.
Kwan-gaba kwan-baya
Kamar yadda aka zata sauya nau'in makamashi da ake amfani da shi ba abu ba ne mai sauki. Wannan abu ne da ake ci gaba da tafka muhawara a kansa a Afirka da kuma sauran sassan duniya.
Daga mahangar BRICS, matasa suna ganin ya kamata a tafiyar da tsarin cikin kwarewa ta yadda ba za a bar kowa a baya ba.
"Muna bayar da shawara yin amfani da tsari sauya nau'in makamashi wanda ba kawai zai mayar hankali kan cimma muradun sauyin yanayi ba, amma hatta warware matsalar karancin makamashi."
A matsayinta na mai masaukin baki Afirka ta Kudu ta bakin Bangaren Albarkatun Makamashi (DMRE) ya jaddada cewa ya kamata a fahimci sauya nau'in makamashin da ake amfani da shi abu da ake yi sannu-sannu inda za a rika la'akari da ci gaban tattalin arziki da bukatun ci gaba, kuma ba tare da yin kwan gaba kwan baya ba.
Ya kamata mu bai wa rayuwa da sana'o'in al'umma muhimmanci a daidai lokacin da ake tabbatar da adalci.
Marubucin, Makhosonke Buthelezi, shi ne Babban Darakta a kungiyar kasashe masu habbakar tattalin arziki kan babban taron makamashi wato BRICS Youth Energy Summit.
A kula: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin TRT Afrika ba ne.