Nijar ta zama kasa ta karshe da ta fada karkashin mulkin soji. Abin ya fara ne daga yunkurin juyin mulki bayan rufe hanyar da ke danganawa ga fadar Shugaba Mohamed Bazoum da dakarun fadar suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023, sai daga baya ya koma cikakken juyin mulki.
An sanar cewa Shugaban Dakarun Fadar Shugaban Kasar Janar Abdourahamane Tchiani shi ne sabon shugaban kasar a ranar 28 ga watan Yulin 2023, bayan juyin mulkin.
Wannan ne juyin mulki na takwas da ya yi nasara a Afirka tun watan Afrilun 2020.
Ban da juyin mulkin da aka yi a Sudan da Chadi, sauran an fi yinsu ne a yankin Yammacin Afirka wanda aka yi a Mali sau biyu (a watan Agustan 2020 da kuma a watan Mayun 2021).
Sai Burkina Faso (a watan Janairun 2022 da kuma a watan Satumbar 2022), sai Guinea (a watan Satumbar 2021), sai kuma yanzu a Nijar.
Duka juyin mulkin da aka yi ban da wanda aka yi a Sudan sun faru ne a kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Nijar kasa ta karshe ce a yankin Sahel da aka yi juyin mulkin kuma hakan ya samar da wani jerin kasashe a yankin Sahel da ya fara daga Guinea a gabar Tekun Atalantika a yankin Yammacin Afirka har zuwa Sudan a gabar Tekun Bahar Maliya, kamar yadda aka bayyana a taswirar da ke kasa.
Duk da cewa Nijar ce ta karshe a jerin a kasashen yankin Sahel, juyin mulkin Nijar ya kasance wata babbar gaba. Saboda kasar tana da tasiri da muhimmanci sosai a yankin fiye da sauran kasashen da aka yi juyin mulkin a baya.
Kafin mu tattauna tasiri da matsalolin da juyin mulkin zai jawo, yana da muhimmanci mu duba abubuwan da suka sa juyin mulkin ya yi nasara.
Da farko, lokacin da aka yi juyin mulkin ya nuna cewa babbar dama ce aka yi amfani da ita. Juyin mulkin ya yi tasiri nan take saboda ya dakatar da rahoton shirin maye gurbin shugaban dakarun fadar shugaban kasa.
Dimokuradiyya ba ta zauna ba sosai
Abu na biyu, kamar yadda aka nuna lokacin zanga-zanga a farkon wannan shekarar, Nijar ba ta tsira daga nuna kin jinin Faransa kamar yadda aka gani a sauran kasashe da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Wannan bai hana gwamnatin Nijar karkashin jagorancin hambararren Shugaba Bazoum kara karfafa dangantaka da kasashen Yammacin Duniya ba musamman Faransa.
Nijar ta kasance cibiyar dakarun sojin Faransa da kuma yaki da ta'addanci a yankin Sahel, ba tare da la'akari da ra'ayoyin galibin 'yan Nijar ba.
Rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin Shugaba Bazoum da 'yan Nijar ya fito fili ne bayan da ba a ga adawa a zahiri daga 'yan Nijar kan hambarar da zababben shugabansu ba.
Abu na uku, juyin mulkin ya nuna rashin kafuwar dimokradiyya a Nijar. Wannan ya nuna cewa cibiyoyin wanzar da mulkin dimokuradiyya na duniya sun mayar da hankali ne kan zabe da tafiyar da al'amura tsakanin manyan a kasar da kuma hadin gwiwa kan tsaro.
Rushewar manyan cibiyoyin kasa
Wannan ya sa aka kasa magance matsalolin zamantakewa da na tattalin arziki da na kyakkyawan shugabanci da kuma matsalolin tsaro da ke ci wa talakawa tuwo a kwarya, juyin mulkin Nijar ya kasance wata manuniya ce ga nakasun dimokuradiyya da ci gaba da hadin gwiwar tsaro a yankin Sahel.
Bugu da kari, za ka iya kawo abubuwa shida kan tasiri da matsalolin da juyin mulkin Nijar ya jawo, wannan ya sa juyin mulkin ya zama abin musamman.
Da farko, kamar yadda juyin mulkin ya hambarar da zababben shugaban kasa ya samar da wani yanayi da idan ba a dawo da Bazoum ba, to babu wata gwamnati a Yammacin Afirka da sauran wurare da za ta iya tsira daga juyin mulki.
Abu na biyu, juyin mulkin Nijar ya jefa shakku sosai dangane da makomar kungiyar kasashe biyar na yankin Sahel (G5 Sahel), wadda ta kasance babbar mai yaki da ta'addanci a yankin Sahel, wadda da ma ta yi rauni bayan da Mali ta fice daga cikinta.
Abu na uku, Kungiyar Tarayyar Afirka da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) wadanda suke yaki da juyin mulki, faruwar juyin mulkin Nijar ya sa an zuba ido a ga yadda za su magance matsalar.
Alamu na nuna cewa al'adar yaki da juyin mulki na wadannan kungiyoyi na fuskantar barazanar rushewa.
Koma-baya ga Kasashen Yamma
Abu na hudu, ci gaba da hamayya tsakanin Kasashen Yamma da Rasha da China a bangare daya a yankin Sahel, juyin mulkin ya sa Nijar ta karkata a bangaren Rasha ciki har da kungiyar sojojin haya ta Wagner Group.
Abu na biyar, Nijar tana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ta'addanci a yankin Sahel.
Faransa ta mayar da sansanin sojinta Nijar bayan da Mali ta fada hannun sojoji. Haka zalika Amurka ta kafa sansaninta na jirage marasa matuka a Nijar. Akwai kimanin sojojin Amurka 1,000 da aka girke a kasar.
Idan ba a dawo da gwamnatin da aka hambarar ba, wanda hakan zai yi wuya, Faransa za ta rasa sansaninta, hakan zai zama koma baya ga shirye-shiryen Faransa a yankin Sahel.
Haka zalika ga Amurka, juyin mulkin zai tilasta mata dakatar da aikace-aikacen sojinta da sauran huldar tattalin arziki da take da kasar.
Gaba daya, ba Faransa da Amurka kawai juyin mulkin zai jawowa asara ba, har ma da sauran Kasashen Yamma wadanda suke amfani da Nijar a matsayin sansanin wasu ayyukan tsaron hadin gwiwa da sauran aikace-aikacen a yankin Sahel.
Cikas din da juyin mulkin zai jawo
Abu na shida, juyin mulkin zai yi tasiri sosai kan samar da makamashi a nahiyar Turai, musamman ga kasar Faransa.
Faransa tana samun kaso mai yawa na sinadarin Uranium (wanda tashar lantarkin nukiliyarta ke amfani da shi) daga kasar Nijar ne.
Bayan jagoran juyin mulkin ya sanar da dakatar hako sanadarin Uranium a Nijar, hakan zai yi tasiri kai-tsaye kuma nan take.
Ko da yake duba da tsare-tsarenta da huldarta, juyin mulkin Nijar ya kasance wata dama ce ta sake tunani kan nahiyar da kasashen duniya kan yadda za a wanzar da dimokuradiyya da ci gaba da hadin gwiwar tsaro a Afirka.
Kamar yadda wani nazarin cibiyar Amani Africa kan yaki da ta'addanci ya ce sauyin manufofi suna "bukatar a mayar da hankali kada a bayar da wata kafa na bazuwar ayyukan ta'addanci" da sake faruwar juyin mulki.
Bayan batun mayar da hankali kan tsaro da ci gaba da hadin gwiwar tsaro da suka kamata su kasance yadda suke ko ma ya karu, akwai bukatar hadin gwiwa da hada albarkatu wuri guda da bai wa fararen hula horo da sauransu."
Marubucin, Dokta Solomon Dersso, tsohon Kwamishina a hukumar kare hakkin dan Adam ta Tarayyar Afirka mai suna African Commission on Human and Peoples’ Rights.
Kuma yana daya daga cikin daraktocin da suka kafa Cibiyar Nazari kan Afirka, wato Amani Africa.
A kula: Wannan makalar ta bayyana ra'ayin marubucin ne, amma ba ra'ayin kafar yada labarai TRT Afrika ba ne.