A Disambar 2022, an fitar da kudin CFA samfurin “2020” a kasashen yankin tsakiyar Afirka wanda bankunan kasashen yankin suka fitar, hakan kuma ya zo daidai lokacin da kin jinin Faransa ke karuwa a yankin.
Akwai takaici sosai saboda ci gaba da amfani da nau’in kudin, inda ake kallon kudin a matsayin wata hanyar iko da tattalin arziki da ci da gumi da kuma karuwar fargaba tsakanin Faransa da kasashen da ta mulka a baya.
An samar da kudin a ranar 26 ga watan Disamabar 1945, inda kudin ke nufin “franc of French colonies of Africa”, wato kudin franc na kasashen da ke karkashin mulkin Faransa.
Duk da kawon karshen mulkin mallaka, ana ci gaba da amfani da kudin a kasashe 14 da suka hada da Benin da Burkina Faso da Ivory Coast da Guinea-Bissau da Mali da Nijar da Senegal da Togo da Kamaru da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Congo da Gabon da Equatorial Guinea da Chadi.
Ba Faransa ce ta yi wa Equatorial Guinea da Guinea Bissau mulkin mallaka ba amma suna amfani da kudin.
Akwai masana harkokin siyasa da tattalin arziki da dama na nahiyar Afirka da ke kallon wannan kudin a matsayin wani burbushi na mulkin mallaka.
Kokarin da aka yi ta yi na sauya wannan kudin ya gagara, har da matakin da kasashen Ecowas suka dauka na samar da kudin yankin a 2020 wanda ake kira Eco.
Tushen duka matsaloli
An baje duka wasu alamomi na tattalin arziki na akasarin kasashen da ke amfani da kudin Franc CFA, inda aka cimma matsaya kan cewa wannan kudin ne tushen duk wasu wahalhalu da suke fama da su.
Idan aka kwatanta da sauran kasashe da ke yankin bayan lura da wasu yanayi, kasashen da ba su amfani da CFA sun fi masu amfani da kudin na Faransa ci gaba da tazara mai yawa.
Misali, a kididdigar da Bankin Duniya yake fitarwa na kasashe mafi karfin tattalin arziki da kuma masu saurin habaka a Afirka, Cote D’Ivore da Benin ne kawai ke cikin kasashen da suke amfani da kudin Franc CFA suka tabuka abin a zo a gani ta fannin tattalin arziki.
Yadda aka samar da Franc CFA ne ake ganin yake jawo duk wasu ce-ce-ku-ce da ake yi kan amfani da kudin.
Da farko dai ana buga kudin ne a Faransa sa’annan a fitar da kudin zuwa kasashen da ke amfani da su; sa’annan rashin iko kan tsarin tattalin arziki sai kuma na uku, kudin Euro ta bangaren Faransa ke la’akari da darajar kudin.
Duk da cewa gwamnatin Faransa ta sha musanta wadannan zarge-zargen da kuma sake jaddada cewa ci gaba da amfani da kudin ya dogara ne kan shugabannin na Afirka, ana kara samun kin-jini da kuma tsana kan kasar Faransa a nahiyar saboda kudin da kuma wasu abubuwa.
Kin jinin Faransa
Masu rajin son kawo ci gaba a Afirka sun ta amfani da batun kudin na Franc CFA domin kara fito da yadda aka tsani Faransa a kasashe da dama da Faransar ta mulka a Afirka.
Masu rajin kare hakkin bil adama da kuma sharhin siyasa irin su Kemi Seba da Nathalie Yamb sun jawo hankali kan abin da suke ganin sabuwar hanya ce ta mulkin mallaka inda suka nuna cewa ci gaba da amfani da wadannan kudade za a iya alakanta shi da rashin ci gaban kasashe renon Faransa da kuma tuni kan iko da Faransar ke da shi kan kasashen da ta mulka.
Abubuwa na kara zafafa idan aka yi la’akari da batun wulakanta ‘yan ci-ranin da ke zuwa Turai a kasashe kamar Faransa da sojojin Faransa da suka je da sunan wanzar da zaman lafiya a Mali da Burkina Faso da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da kuma irin tarihin Faransa a nahiyar Afirka.
Bugu da kari za a iya cewa kin jinin Faransar ya karu ne bayan jerin juyin mulkin da aka yi a kasashen Yammacin Afirka, musamman Mali da Guinea Bissau da Burkina Faso.
A lokacin wani taro na Majalisar Dokokin Faransa, wani dan majalisar Faransa ya ce ya lura da cewa jagororin juyin mulkin Mali sun samu goyon baya daga jama’ar kasar da kuma nuna rashin jin dadi dangane da sojojin Faransa da ke kasarsu.
Za a iya cewa fargabar ta kara karuwa tsakanin Faransa da kasashen Yammacin Afirka bayan da aka bukaci sojojin na Faransa su bar Mali, inda kuma dangantaka ta kara tsami tsakanin Paris da Bamako bayan da aka kori jakadan Faransa din da ke Mali a karshen 2022.
Illar Faransa
Wani lamari da ke kara nuna yadda tasirin Faransa ke raguwa a Afirka shi ne lamarin da ya faru a ranar 4 ga watan Maris din 2023 inda Shugaba Felix Tshisekedi ya karbi bakoncin Shugaba Macron na Faransa inda ya jaddada masa dole ne Faransa da sauran kasashen yamma su sauya yanayin da suke mu’amala da Afirka da kuma daina yi musu katsalandan.
Wannan batun wanda aka yi ta tunaninsa a fadin Afirka ya zama wata alama da ke nuna cewa shugabannin Afirka da dama za su daina yarda da katsalandan daga Faransa da sauran kasashen yamma.
Masu sharhi kan siyasa da dama na ganin Macron bai ci nasara ba a tafiyarsa zuwa Afirka, wadda tafiya ce domin kaddamar da sabbin tsare-tsaren tattalin arzikin Faransa da tsare-tsaren soji da na muhalli da kuma ceto darajar Faransa da kuma raguwar karfinta kan kasashen Afirka.
Hakan kuma ya nuna yadda Faransar yunwarta ta fito fili wajen ganin ta ci gaba da iko da Afirka da kuma fada a ji a idon duniya.
Rasha da China sun fito a matsayin wadanda suke son maye gurbin Faransa a nahiyar.
Ganin irin rashin jituwar da ke tsakanin Faransa da Rasha sakamakon yakin Ukraine, ana ganin Moscow na daukar kin jinin Faransa a matsayin wata dama a nahiyar ta bata dangantakar Faransar da kuma saka sojojinta a nahiyar, ta hanyar sojojin hayarta na Wagner wadanda yanzu haka suke a Mali da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka inda suke aikin tsaro.
Mai magana da yawun gwamnatin riko ta Mali ya yi wata magana a lokacin hira da gidan rediyon RFI kan cewa Rasha ta taimaka wa kasar da kayayyakin soji masu muhimmanci da suka hada da jirgi mai saukar ungulu da makamai domin yakar masu tayar da kayar baya a arewacin Mali.
Shi ma shugaban Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka ya ce Rasha ta taimaka wa sojojin kasarsa da makamai ganin cewa makaman da Faransa ta yi alkawari ba su iso masa ba.
Ana ganin Faransa tana ci gaba da amfani da hanyoyin mulkin mallaka inda tana mu’amala da kasashen Afirka duk da kawo karshen mulkin mallakar a shekarun 1960.
Marubucin, Niying Roger Mbihbiih, malami ne a tsangayar nazarin harkokin mata da jinsi a Jami’ar Buea ta Kamaru.
Togaciya: Ra’ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai ne su zama ra’ayi ko mahanga ta TRT Afrika ba/