Sanannen abu ne yadda tawagar kwallon kafar kasar ta kunshi 'yan wasa da dama wadanda asalinsu ba 'yan kasar Faransa ba ne. Hoto: AFP

Daga Yahya Habil

Tawagar kwallon kafar kasar ta samu nasarori da dama, ta lashe Gasar Kofin Duniya har sau biyu, kuma ta ci gaba da fafata a gasanni ba kakkautawa kuma ta samar da manyan zaratan 'yan wasa da duniya ke ji da su.

Ko da yake sanannen abu ne yadda tawagar kwallon kafar kasar ta kunshi 'yan wasa da dama wadanda asalinsu ba 'yan kasar Faransa ba ne.

Yawancin 'yan wasan suna buga wa tawagar kasar Faransa duk da cewa galibinsu 'yan asalin Afirka ne wanda hakan yake nuna tasirin mulkin mallakar da Faransa ta yi wa kasashensu.

Misali kamar yadda kafar yada labarai ta Sportskeeda ta bayyana kaso 87 cikin 100 na 'yan wasan da suka ciyo wa kasar Kofin Duniya a shekarar 2018 asalinsu baki ne.

Wannan zubin bai tsaya ga babbar tawagar kwallon kafa ba kawai hatta sauran tawagogin ciki har da kungiyoyin da ke wasa a matakin lig-lig din kasar – galibinsu 'yan asalin nahiyar Afirka ne.

Abin ya jawo ce-ce-ku-ce da muhawara, inda mutane da yawa a Faransa ba sa goyon bayan tsarin zubin 'yan wasan kwallon kafar kasar.

Wannan yanayin na tawagar kwallon kafar Faransa yana nuni ga yadda zamantakewa take a kasar wadda ta kunshi al'adu iri-iri da nuna wariya.

Kashi 87% na 'yan wasan tawagar kwallon Faransa 'yan ci rani ne 'yan asalin Afirka. Hoto AFP

Game da tawagar kwallon kafar Faransa, ana wannan korafin ne kawai ranar da tawagar ba ta yi nasara ba, daga nan sai a fara nuna wa 'yan wasa 'yan asalin Afirka wariyar launin fata.

Idan ana so a fahimci abin sosai, akwai lokacin da shahararren dan wasan Faransa Karim Benzema wanda dan asalin Afirka ne, ya ce: "Idan na ci kwallo ni Bafaranshe ne, idan kuma ban ci ba, ni Balarabe ne".

Batun nuna wariyar launin fata da tsangwama da ake nuna wa 'yan wasa 'yan asalin Afirka a Faransa hakan yana nuna akwai dimbin irin wadannan 'yan wasan.

Kamar yadda Quartz ta bayyana akwai 'yan wasa 'yan Afirka 107 da ke wasa a Gasar Ligue 1 (babbar gasar lig ta Faransa), hakan ya sa Lig din shi ne wanda ya fi yawan 'yan wasa 'yan asalin Afirka a nahiyar Turai.

Wadannan 'yan wasa 107 ba su zama 'yan Faransa tukuna ba, wato ba su da fasfo din zama 'yan Faransa. Wannan yana nufin adadin ya fi haka idan aka hada da 'yan wasan 'yan asalin Afirka da suke rike da fasfo din Faransa.

Wannan bai zo da mamaki ba ganin yadda tawagar kwallon kafar kasar Faransa ta dogara ne kacokan kan 'yan wasa 'yan asalin Afirka.

Bugu da kari, ana yi wa tawagar kwallon kafar kasar Faransa inkiyar “Black, Blanc, Beur” abin da nuni da yawan bakaken fata 'yan Afirka da ke wasa a Faransa.

Inkiyar ta samo asali ne daga launin fata daban-daban da ake samu a tawagar kwallon kafar Faransa, kalmar "Beur" tana nufin 'yan wasa 'yan asalin arewacin Afirka.

An haifi Zinedine Zidane ne a ranar 23 ga watan Yunin 1972, a Marseille da ke Faransa bayan da iyayensa suka yi kaura daga Aljeriya. Hoto: Others

Ko da yake kwallon kafa abu ne da yake a cakude a Faransa, sai dai abu ne da ke kunshe da nuna wariyar launin fata, amma kuma ba za a ce ya samo asali daga wasan ba ne kansa, ya samo asali ne daga masu ruwa da tsaki kan wasan kamar kafafen yada labarai da 'yan siyasa da magoya baya da hatta wasu 'yan wasa da kuma masu horar da su.

Har ila yau akwai nau'in nuna wariyar launin fata da ya samo asali daga hukumar kwallon kafar kanta.

A shekarar 2011, Kocin Tawagar Kwallon Kafar Faransa na lokacin Laurent Blanc ya bayar da shawara ga Hukumar Kwallon Kafar Faransa yayin wata ganawa kan yin wani tsari na takaita yawan 'yan wasa matasa 'yan asalin Afirka a tawagar kwallon kafar Faransa.

Ya ce ya kamata rika daukar 'yan wasan a tawagar kaso 30 cikin 100 ne kawai, inda ya ce Faransa tana son 'yan wasa da suka dace da al'adunta.

Ya ci gaba da magana, inda ya bayar da misali da tawagar kwallon kafar Spain, wacce yake "ba ta cikin matsala" saboda ba ta "bakaken fata".

Ana yawan samun irin wadannan kalaman nuna wariya daga kafafen yada labarai a Faransa da kuma fagen siyasar kasar. Kalaman da suka ja hankali sosai kafin kalaman Koci Blanc shi ne na tsohuwar Shugabar jam'iyyar National Front Party Jean-Marie Le Pen.

Kamar Blanc, Le Pen ta yi magana ne kan batun asali da kuma batun "kasancewar mutum Bafaranshe."

Ta taba ikirarin cewa 'yan wasa 'yan asalin Afirka ba su iya rera taken kasar ba, inda ta buga misali da shahararren dan wasan Faransa Zinedine Zidane, wanda kamar yadda Le Pen ta ce "yana motsa baki ne" idan ana taken kasar.

Kalaman Blanc da na Le Pen wanda suka yi musu fiye da shekara 10 da suka wuce, suna nuna yadda kalaman wariyar launin fata a tawagar kwallon kafar Faransa ya zama babban batu.

Batun ya ci gaba babu kakkautawa. An taba bukatar Kocin kungiyar OGC Nice ta Lig 1 Christophe Galtier ya bayyana a gaban wata kotu dangane da kalaman da ya yi a kakar shekarar 2020-2021.

Ya taba cewa kungiyar "cike take da kazanta" kuma "akwai bakaken fata zalla wadanda suka kunshi rabin 'yan wasan kungiyar da suke kasancewa a masallaci duk ranar Juma'a da rana."

Dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe dan asalin Kamaru ne mai kuma alaka da Aljeriya. Hoto: AFP

Har ila yau wani misali da ke nuna yadda batun nuna wariyar launin fata ya ki ci, ya ki cinyewa a fagen kwallon kafar Faransa shi ne kalaman shahararren dan wasan kasar Kylian Mbappé.

Mbappé, wanda yake da asali a Kamaru da Aljeriya, ya ce ya kusan barin tawagar kwallon kafar Faransa a shekarar 2021, bayan ya fuskanci rashin samun goyon baya bayan da ya barar da bugun fanariti a wasan da aka doke su a Gasar Cin Kofin nahiyar Turai. Abin da ya faru ya yi kama da kalaman da Karim Benzema ya yi a baya.

Ko ba komai an gurfanar da Galtier kan kalaman da ya yi kuma hakan manuniya ce kan yadda aka fara samun ci gaba dangane da batun yaki da nuna wariyar launin fata a fagen kwallon kafar Faransa, kodayake Koci Blanc da ya yi irin kalamansa ba a gurfanar da shi ba.

Haka zalika hakan ba yana nufin an yi nasarar gano yadda za a magance matsalar ba ne.

Ya kamata a magance matsalar daga tushe ne. Me ya sa 'yan wasa 'yan asalin Afirka kadai ne ke fuskantar wannan matsala ta nuna wariyar launin fata?

Idan ana haka ne saboda su baki, to su waye 'yan asalin Faransa, to me ya sa ba a taba nuna wa 'yan wasa kamar Raymond Kopa da Michel Platini da Youri Djorkaeff da kuma Robert Pires wariyar launin fata ba?

Ko saboda su baki ne daga kasashen Turai fararen fata? Ko saboda su ba bakaken fata ba ne ko kuma wankan tarwada ba?

Ya aka yi Platini, wanda bako ne, ya zama Bafaranshe fiye da Zidane, wanda shi ma bako ne?

Babbar matsalar kwallon kafa a Faransa wanda kuma shi ne yake damun Faransa a matsayin kasa, shi ne yadda mahukunta suke kokarin "nakar" da kowa ya zama cikakken Bafaranshe.

Kasancewar mutane masu al'adu iri daban-daban yana zuwa da kalubale, wato dole ne a karbi mutane yadda suke kuma ya kamata kada Faransa ta manta da tarihin mulkin mallakar da ta yi.

Marubucin, Yahya Habi, dan jarida ne dan kasar Libya wanda yake nazarin kan al'amura a Afirka.

TRT Afrika