Kisan zaluncin da wani dan sanda ya yi wa matashi Nahel Merzouk, Musulmi dan asalin Aljeriya da Morokko, ya janyo rikici sosai a fadin kasar Faransa.
Wannan rashin adalci da zalunci ya faru a jajiberen Babbar Sallah – hakan ya bakanta wa Musulmai sosai. Musulmai sun harzuka tare da fara kai hare-hare kan gine-gine da kadarorin gwamnati, makarantu, shaguna da wuraren sana’a, abin da ke da ma’ana ta siyasa.
Masu zanga-zangar sun nuna adawa da nuna kyama ga Musulunci da wariyar launin fata da suka yi katutu a Faransa.
Wannan abu ya fito da kazantar da kasar Faransa ke ciki.
Masu goyon bayan kasar da masu fada a ji a shafukan sada zumunta sun goyi bayan zaluncin ‘yan sandan ga Musulmai, inda suka dora alhakin lamarin kan ‘bata-gari’ daga cikin Musulman, ba wai wani tsari da aka kafa dadadde da ya shafi kasar ba.
Domin bankadowa tare da bayyana wannan ta’ada, kisan gilla ga Merzouk da zaluncin da ‘yan sanda ke yi na bukatar a duba su da idanuwan basira ta fuskar tarihi da zamantakewa.
Tun daga mulkin mallaka
Emmanuel Blanchard, masanin harkokin siyasa yana ganin cewa ‘yan sandan ‘sun zama inuwar ‘yan mulkin mallaka’ ne, inda wannan matsala ta samo asali daga lokacin bautar da mutane a Faransa.
Bayan mamayar da ‘yan mulkin mallaka suka yi a karni na 19, an kirkiri sabbin hukumomin tsaro don fuskantar boren da ka iya tasowa a yankunan da aka mamaya, da ladabtar da mutane.
'Yan sandan suna aiki ne tare da sojoji domin bayar da kariya ga ‘yan mulkin mallaka, inda suke kashe Musulmai da suke gudanar da tarukan karya dokokin Jamhuriyar Faransa.
Daga nan ‘yan sandan mulkin mallaka suka zama masu nuna kyama ga Musulmai da zaluntar su. Manufarsu ta farko ita ce hana Musulmi sakewa da karbe ragamar siyasa a yankunan da suka kwace musu.
Shigar Musulmai biranen Faransa ta sa Jamhuriyar Nuna Wariya ta samar da wasu ‘yan sanda da aka saka wa sunan Dakarun Arewacin Afirka a 1930.
Suna amfani da dabarun da suka aiwatar a Aljeriya a birnin - babban aikin dakarun shi ne su sanya idanu kan Musulmai da ke wajen birane.
Bayan yakin duniya na biyu, an samu raguwar wannan nuna kyama ga Musulmai da wariyar launin fata na wani dan lokaci, sai dai kuma abin ya dawo a shekarun 1950, da wata siga ta daban amma kuma da yanayi iri guda.
A lokacin yakin kwatar ‘yancin kai na Aljeriya, an kai wadannan dakaru don yakar Musulman Aljeriya.
Daya daga cikin sojojinsu Roger Le Taillantier ya bayyana yadda wadannan dakaru suka dinga cin karensu babu babbaka.
Jami’in ya rubuta a wani littafinsa da aka wallafa a 1995 cewa ‘A bangarenmu, tare da bindiga a bangare daya, sannan ga littafin hukunta manyan laifuka a daya hannun, muka dinga yaki a Aljeriya.”
Bayan yakin, an samar da runduna ta musamman don yaki da manyan laifuka a Arewacin Afirka.
Duk da cewa an sauya mata suna, amma aikinsu gida daya ne da na bayan. Sun dinga kokarin murkushe Musulmai a yankunan wajen biranen Faransa. Har zuwa yau suna nan suna wannan aiki.
A lokacin gwagwarmayar ‘yantar da Aljeriya, ‘yan sanda da sojojin Faransa sun fadada ayyukan yaki da masu tayar da zaune tsaye.
Dakarun Faransa sun yi wa Musulmai kawanya.
Domin kare manufofin mulkin mallaka, kasar ta yi amfani da hanyoyi da dama don cutar da Musulmai da magance tawayensu.
Daga cikin hanyoyin da suka bi har da bincikensu da neman su nuna katunan shaidar zama dan kasa, sannan suna harba musu hayaki mai sanya hawaye da jiragen sama masu saukar ungulu don sanya musu ido.
Wadanna tsauraran dokoki har yanzu suna tasiri kan yadda Faransa ke ayyukan tabbatar da tsaro a yankunan Musulmai.
Dalilan da suka sanya ‘yan sanda ke zalunci a Faransa
Bincike na baya-bayan nan da aka gudanar ya bayyana yadda wasu maza 13 manyan ‘yan asalin Afirka suka mutu a hannun ‘yan sandan Faransa a 2022 kadai a lokacin duba ababen hawa.
Har yanzu babu kwakkwaran bincike game da zaluncin da ‘yan sanda ke yi a Faransa. Duk da haka, rashin wadannan alkaluma ba zai hana mu bincikar tsarin da ake nuna kyamar Musulunci da nuna wariya ba.
A zahiri bai kamata 'yan sanda su hada siyasa ko nuna bambaci da kyama a aikinsu ba. Amma an tsara shi ne don ya kalubalanci Musulmai, tare da murkushe siyasarsu.
Kamar yadda farar-fatar Amurka suke tsoron samar da daidaito tsakaninsu da bakar-fata, Faransa da fararen-fatar kasar na da babbar barazana guda daya: karfin siyasar Musulmai.
A zamanin mulkin mallaka, gwagwarmayar neman ‘yancin Musulmi na kassara wa da raunata Jamhuriya. Shi ya sa Dhoruba Bin Wahad ya ce dalilan da suka sanya ‘yan sandan Amurka ke zaluntar bakaken-fata shi ne ya sanya ‘yan sandan Faransa suke zaluntar Musulmai.
Wannan bore ya sake bude sabon shafin siyasa ga Musulmai a Faransa.