Filin hakar ma'adanan uranium a Tamgak, karkashin kamfanin hakar ma'adanai na Areva's Somair a Arlit, Nijar. / Hoto: Reuters Archive

Daga Mahaman Laouan Gaya

Tsarin jari-hujja na kasashen Yamma yana fuskantar rikici, wanda ya janyo kamfanonin ke tururuwa zuwa kasashen Afirka don hakar ma'adanai, musamman kasashen da ke yankin Sahel wanda ake wa lakabi da "boda-uku".

Idan ana magana kan hakar arziki (ma'adanai da mai da gas) a yankin Sahel na Afirka, za a duba batun matsayin ma'adanai a kasar yankin, da tattalin arzikinsa, da kuma duba siyasar yankin, sannan a kalli inda batutuwan biyu suka hadu.

Tabbas, ana amfani da sunan aikin 'jin-kai' da yakar 'yan ta'adda, inda har yankinmu na Afirka ya zamo inda manyan kasashe suke kutsowa, ta hanyoyi da yawa, da karfin soji a wuraren da ake da arzikin ma'adanai (karafan da ba a samu a ko ina) da albarkatun makamashi (mai, gas, uranium, da hydrogen).

Wannan salon mulkin mallaka ne da kasashen Yamma suka shirya kuma suka aiwatar da shi a Libya (inda suka kashe shugaban Libya Muammar Gaddafi suka haifar da rikici a kasar) a 2011, karkashin Shugaba Sarkozy na Faransa, ta amfani da NATO.

Dole a fahimci cewa takamaimar manufar katsalandan din da sojin Faransa suka yi ba ta da alaka da tsaron al'ummar Libya, ko assasa dimokuradiyya, sun zo ne don tabbatar da kamfanonin Yamma sun yi kaka-gida kan arzikin ma'adanai da makamashi na Libya. Kuma abin ya zo ya shafi Yammacin Afirka.

Makarkashiyar shirya rikici?

Tun wannan lokacin, yankin Afirka ta Yamma bai kara samun dauwamammen zaman lafiya ba. An hambarar da gwamnati a Mali, da Guinea, da Burkina Faso, sannan ga rashin zaman lafiya a Nijar, da Burkina Faso, da yunkurin wargaza Mali.

Kananan rikice-rikice suna yaduwa a yankin, kuma suna watsuwa a kasashen bakin teku (Benin, da Kwadibuwa da Togo), yayin da ake fuskantar barazanar harin soji daga kasashen waje.

Wadannan rikice-rikice a Yammacin Afirka, idan aka hada su da yakin Rasha da Yukiren (wanda ya janyo katsewar safarar makamashi daga Rasha zuwa Yammacin Turai), sun janyo bukatar makamashi da ake hakowa, musamman ma'adanan karafa a kasashen da suka ci gaba.

A 2010, bayan sabanin kan-iyaka tsakanin China da Japan game da tsibiran Senkaku, China, wadda ke samar da ma'adanan karfe masu wuyar samu, sun saka takunkumin kai kaya zuwa Japan. Kuma sun takaita kayan da ake kai wa wasu kasashen, musamman a Yammacin Turai.

Wannan ya janyo wa masana'antun fasaha matsala, inda ya haifar da tashin farashin wadannan ma'adanai masu kima a duniya.

A daidai wannan lokacin ne Tarayyar Turai ta karfafa shirinta na saka tsaro kan muhimman ma'adanai wanda ya kunshi jerin da kasashen Turai suka zayyana, na albarkatun da ake hakowa masu matukar muhimmanci.

Kalubalen shi ne saka tsaro kan harkar samar da kaya, ta hanyar sayen hannun jari a mahakar ma'adanai, da kirkirar jari, da nemowa da kare ma'adanan a kasashe wadanda ba su san ma suna da arzikin ba.

A duk fadin Yammacin Afirka, da kuma a yankin Sahel, wanda ya yi kaurin suna da yanki mafi talauci a duniya, akwai tarin arzikin karkashin kasa. Arzikin yankin na makamashi da ma'adanai suna daya daga cikin dalilan da yankin ke da farin jini.

Kamar yadda aka rubuta a jaridar "l'Humanité", arzikin yankunan "yana saka wa manyan kamfanonin duniya su tara yawu a baka".

Mamayar arzikin karkashin kasa

Ganin dumbin arzikin hakar ma'adanan, masana suna kiran yankin mai ‘badakalar kasa’. A yau, kamar yadda ya faru a baya, wuraren hakar ma'adanai a Yammacin Afirka yawanci manyan kamfanonin kasashen waje ne suka mallake su.

Kamfanonin Faransa sun hada da Orano da TotalEnergy. Sai manyan kamfanonin Amurka kamar ConocoPhilips, da AngloAmerican, da AngloGold Ashanti, da BHP Billiton, da Rio Tinto, da kuma kamfanin China na CNCP.

Sannan akwai kananan kamfanonin hakar ma'adanai daga wadannan kasashe, wadanda suke yi suna da badakalar hada-hadar kudi.

Kananan kamfanonin hakar ma'adanai suna sayar da kayan bogi ga gwamnatocin Afirka marasa kan-gado, da hannun-jari-guda daga kasashen da suka cigaba (hannun-jari-guda na nufin hannun jari a kananan kamfanonin hakar ma'adanai da ake siyan su a kasa da dala guda, a kasuwar hannun jari ta Toronto).

Abin lura a nan shi ne, kasuwannin hada-hadar hannun jari na Toronto, da Vancouver da Calgary a Canada, suna kau da kai daga batun shigar da kananan kamfanonin hakar ma'adanai cikin kasuwar, wadanda suka fara ayyukan hakar ma'adanai a Afirka kudu da Sahara.

Wadannan kananan kamfanonin da ba su da jari sosai, wani lokacin ma ba su da ma'aikata ko ofis, wadanda mamallakansu boyayyu ne kuma an kafa su ne a kasashen da ba a biyan haraji, suna iya cin nasarar samun amincewar gwamnatocin Afirka su ba su kwangilar kula da wuraren hakar ma'adanai masu muhimmanci.

Da zarar kwangilar ta shigo hannu, wadannan kamfanoni sai su koma kasuwar hannun jarin, daidai lokacin da jarinsu zai yi sama, kuma su kaucewa biyan haraji, da bin doka, da kare muhalli, da kare mutane, da lafiyar jama'a.

Suna tattara dumbin jari tun kafin aikin hako ma'adanan ya fara. A karshe ba sa saka ko kwabo na jarinsu, ban da watakila dala miliyan daya ko biyu na cin-hancin da sukan bayar don hanzarta sanya hannu kan yarjejeniyar.

A harkar hakar ma'adanai, kasar Canada (tare da kasuwanninta na hannun jari a Toronto da Vancouver) ita ce tamkar yadda Geneva da Zurich suke zaman matattarar masu harkar halatta kudin haram da masu gujewa haraji.

Cikin shekaru 30 da suka shude, Canada ta zamo babbar maboyar masu gudun bin doka, da bin tsari, da biyan haraji a duniya.

Da yawa daga wadannan kamfanoni suna bibiyar nahiyar Afirka ne. Muna iya tuna lasisi sama da 150 na hakar ma'adanai da aka raba cikin gaggawa a yankunan Sahel na Liptako-Gourma, da Sud Maradi, da Air, Djado da Tim Mersoi Basin.

An bai wa kamfanoni 42 (wasunsu na bogi) daga kasashe 12 a shekarar 1995-96, amma a karshe ba a kara jin duriyarsu ba. Me ya faru da lasisan hakar ma'adanan da gwamnatin Nijar ta bayar har 154 a lokacin, kuma ina labarin kamfanonin da suka ci gajiyar lasisan?

Akwai abin lura kan batun wadannan kananan kamfanonin hakar ma'adanai, wadanda suka rage: kamar Savannah Energy PLC, wanda a 'yan kwanaki da suke wuce ya tsinci kansa a rikicin da ya illata diflomasiyya tsakanin Kamaru da Chadi.

A wata sanarwar yada labarai da ta fito ranar 23 na Afrilun 2023, fadar shugaban Chadi ta nuna bacin-ranta game da sabanin da ya barke tsakanin Kamaru da Chadi, bayan zargin saye kadarorin kamfanin ex-ESSO-Tchad da kamfanin Savannah Energy ya yi.

Gwamnatin Chadi ta zargi gwamnatin Kamaru da tallafawa wajen saye kadarorinta a cikin kasarta.

Hadarin canji

Cikin shekaru goma na baya, adadin kamfanoni hakar ma'adanai daga Arewacin Amurka da Turai wadanda suke aiki a Afirka sun kara yawa sosai.

Wannan yanayin ya fito da gasar da ke tsakanin kasar Faransa da Amurka, a yankin Sahel. Yankin na fama da tarin matsaloli da aka kitsa kuma aka raina, wadanda kuama ake fakewa da su don halatta amfani da sojoji da kafa sansanin soji.

Lokaci ya yi da 'yan kasar Burkina Faso, da Mali da Nijar za su fahimci cewa matsalar tsaro tana ci gaba a yankinsu, da yawaitar rundunonin sojin kasashen waje, a kasarsu da ba komai ya kawo su ba face kwadayin albarkatun kasa da makamashi.

Akwai albarkatun da a yanzu ake kwasa daga kasashen, (uranium a Nijar, zinare a Mali da Burkina Faso), da kuma yunkurin manyan kasashen waje na fara kwasar wasu muhimman ma'adanai da ba a fara diba ba (an kula yarjejeniyar fara hakar ma'adanin leonine a wasu daga cikin kasashen).

Matakin ci gaba fasaha a lokacin mulkin mallaka da bayan lokacin bai ba da dama an fara hakar wadannan ma'adanai ba. Amma a yau ci gaban duniya ya janyo bukatar farawa. Kuma kasashen Yamma suna bin duka matakan ganin sun kai ga albarkatun.

Da alama yanayin wayewa da kuma fafutukar matasan Afirka yana ruguza aniyar mulkin mallakar kasashen Yamma. A yanzu alamu suna nuna cewa ana daf da rufe shafin kasashen Yammacin duniya masu karfi, da suke wawason albarkatun yankin Sahel, kowa ya huta.

TRT World