A wa'adin mulkinsa na farko, shugaba Trump ya fi dogara da jami'an soja fiye da wata gwamnati da ta gabace shi tun zamanin shugaba Reagan. Hoto: AP       / Photo: AFP

Jimillar sansanonin soja 800 a kusan ƙasashe 90, haɗa da ɗaruruwa a cikin Amurka, a tarihi gaba ɗaya, Amurka ce ta mallaki cibiyoyin tsaro mafi yawa a ƙasashen ƙetare.

Yayin da yin amfani da matakan soja ya maye gurbin ɗaukar matakan siyasa, ko dai Amurka ta kasance ta faɗa yaƙi tsundum, ko ta shiga wani rikici, ko kuma ta jibge dakarunta a ƙasashen ƙetare, a tsawon fiye da shekaru 250 da ta kasance tana wanzuwa, in banda shekaru 11 kacal.

A wa'adin mulkinsa na farko, shugaba Trump ya fi dogara da jami'an soja fiye da wata gwamnati da ta gabace shi tun zamanin shugaba Reagan.

Amma Trump ya yi iƙirarin shi ba zai dinga tsoma baki cikin lamarin wasu ƙasashen ba, sannan kuma shi mai wanzar da zaman lafiya ne, wanda da ba zai taɓa bari rikicin Ukraine da yankin Gaza na Falasdinawa su zama yaƙi ba.

Saboda haka, Trump zai nuna shi shugaban ƙasa mai son zaman lafiya ne ko kuma ɗan ina-da-yaƙi ne a shekaru huɗu masu zuwa?

Amsa mafi sauƙi ita ce e kuma a'a.

Fuskoki biyu na Trump

Abin da ya fi bayyana shi ne Trump shugaban ƙasa ne "ɗan kasuwa" wanda ba ya taɓa barin dama ta kuɓuce masa. A wannan ra'ayin, abu mafi muhimmanci shi ne ƙulla hulɗar kasuwanci da shugabannin ƙasashen ƙetare.

Duniya na buƙatar wanzar da dimokuraɗiyya, amma wasu 'buwayayyun mutane' ne ke tafiyar da lamarin. Hakan ne ma ya sa shugabannin ƙasashen ƙetare kamar Vladimir Putin, Xi Jinping, Viktor Orban suke burge Trump, kamar yadda ake faɗa.

Amma kuma, manyan jami'an Trump kan harkokin ƙasashen waje an san su kan daɗaɗɗen ra'ayin ƴan mazan jiya da tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe, kamar sakataren harkokin waje,Marco Rubio, da ministan tsaro Pete Hegseth, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Michael Waltz, da shugaban hukumar leƙen asiri ta CIA John Ratcliffe, da jakadan Amurka a MDD Elise Stefanik da sauransu.

Waɗannan mutane maza da mata ƴan ra'ayin riƙau ne da suka yi imani da yin amfani da ƙarfi wajen tafiyar da manufofin ƙasashen waje.

Majalisar zartarwan Trump ta ƙunshi ƴan kasuwa ne, amma masu aƙidar ƴan mazan jiya tare da nuna tsauri na kawo musu cikas. Suna iya faɗa masa magana, amma ba yana nufin kullum yana sauraren su ba ne.

A wa'adin mulkinsa na farko, Trump ya fi dogara da mashawartan fadar shugaban ƙasa fiye da na ma'aikatar harkokin waje domin su ba shi shawara kan hulɗa da ƙasashen waje. Zai iya ci gaba da tafiya kan wannan ra'ayin..

Idan wa'adin mulkin Trump na farko zai ɗora alhakin tafiyar da maido da hulɗa tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa kan babban mai ba shi shawara kuma surukinsa Jared Kushner, mulkin Trump na biyu ya dogara ne a kan Steve Witkoff, hanshaƙin attajiri a harkar gine-gine, mai bayar da gudummawa a tafiyar kafa asalin ƙasar Yahudawa kuma mai sha'awar wasan golf wanda tuni ya ajiye Ma'aikatar Harkokin Waje a gefe.

Saɓanin mulkin Trump na farko,wanda ya ginu kan hayaniya da rashin tabbas yayin da ya warware ƴarjejeniyoyin da Amurka ta daɗe da ƙullawa da ƙasashen duniya, mulkin Trump na biyu ya yi wuf ya yunƙura, amma fa sai da ya samu matsala da ƙawayen Amurka.

Bisa la'akari da takensa na "Buƙatun Amurka su ne kan gaba", ya rungumi manufofin ƙasashen waje na ƴan kishin ƙasa, da hulɗar kasuwanci da ƙasashen duniya kan ƙulla ƴarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen duniya.

A wannan, mataimakin shugaban ƙasa JD Vance na taimaka masa, yayin da naɗa Tulsi Gabbard a matsayin shugabar hukumar leƙen asiri ke nuna takatsantsan matuƙa ainun, a yadda Amurka ke tunkarar hulɗa da ƙasashen duniya.

Sai dai, akwai abu guda da mulkin Trump guda biyun suka yi tarayya a kai - maƙudan kuɗi.

Karanta ƙarin wasu

Suka kan masu goyon baya: Mutane biyar da suka fi kowa kuɗi da suka rusuna wa Trump Manufofin da buloniyoyi da manyan masana'antu ke aiwatarwa.

Kuɗi ne jigon tafiyar da siyasar Amurka. Ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓen Trump babban misali ne.

A shekarar 2020, ya samu goyon baya daga Robert Mercer mai jawo ce-ce-ku-ce (ƙiyasin dukiyarsa ta kai dala biliyan$1)da ƴarsa Rebekah, waɗanda da dukiyarsu aka yi wa yaƙin neman zaben Trump hidima, da kuma aikace aikace mai tsatssuran ra'ayin,Steve Bannon, har ma Boris Johnson da kuma Brexit na Birtaniya.

A shekarar 2020, ya samu goyon baya daga Robert Mercer mai jawo ce-ce-ku-ce (ƙiyasin dukiyarsa ta kai dala biliyan$1)da ƴarsa Rebekah, waɗanda da dukiyarsu aka yi wa yaƙin neman zaben Trump hidima, da kuma aikace aikace mai tsatssuran ra'ayin,Steve Bannon, har ma Boris Johnson da kuma Brexit na Birtaniya.

Yanzu iyalan Mercer sun ɗauki nauyin wasu jami'an Trump da kuma kwamitin Heritage, wanda shi ya assasa project 2025, yunƙurin durƙusar da harkokin gwamnati a Amurka.

Wannan karon, attajirai masu goyon bayan Trump sun ƙaru. Waɗannan manyan waɗanda suka bayar da gudummawa Space X - karanta: Elon Musk (ƙiyasin dukiyarsa ya kai dala biliyan$400); mai ra'ayin mazan jiya,buloniya mai zuba jari Timothy Mellon (ƙiyasin dukiyarsa ta kai dala biliyan$14); da kuma Miriam Adelson (dala biliyan $32), buloniya Ba'amurkiya ƴar Isra'ila matar marigayi attajiri mai sana'ar caca,Sheldon Adolson.

Kowannensu ya bayar da gudummawa daga dala miliyan $100 zuwa miliyan $300 a yaƙin neman zaben Trump.

An samu sauyin goyon baya daga shekarar 2020 zuwa 2024. Waɗanda suka bayar da gudummawa mai tsoka yanzu sun fi yawa a kashi biyu cikin uku na jimillar adadin, a kan waɗanda suka bayar da gudummawa kaɗan.

A cikin masana'antu kuwa, sashen kuɗi da na sufurin jiragen sama da sufuri su ke cin karensu babu babbaka, bisa samun goyon bayan ƴan a-mutun Trump, Amurkawa da suka manyanta da kuma ƴan jam'iyyar Republican masu ra'ayin mazan jiya.

A cikin gida, Musk shi ne mai kawo wa Trump sauye sauye. Amma a manufofin ƙasashen waje,shi ne mai daidaita al'amurra, a batun haraji da batun China.

Shekaru hudu da suka gabata, yaƙin neman zaɓen Trump sai da ya samu sama da dala miliyan $300 ta bayan fage. Akasin haka, hankalin manyan masana'antu bai kwanta da Trump da magoya bayansa ba.

Wannan a baya kenan. A yanzu, cibiyoyin kuɗi suna nan daram a bayan Trump. Sun yi imanin za su yi amfani da shi, yayin da shi kuma yake ganin yana amfani da su.

Galibin masu tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashen, ko ƴan jam'iyyar Republican ko jam'iyyar Democrat sun dogara da kuɗi ne daga ma'aikatar tsaro ko ta makamashi. Trump bai dogara da su ba.

Yana so maganganunsa da ayyukansa su rinƙa tsoratarwa, kuma yana son tirsasawar tattalin arziƙi. Sai dai akwai gargaɗi. Idan ka ƙalubakance shi don ka ga gudun ruwansa, zai iya yin amfani da ƙarfi.

Faɗaɗa da mamaya

A wa'adinsa na farko, Trump ya sauya fasalin tsaro da kariya na ƙasa na Amurka ya mayar da hankali kan gogayyar neman iko da China da Rasha sannan ya harzuƙa ƙawayen Amurka na Turai ta hanyar yin barazanar yin watsi da ƙawancen zamanin yaƙin cacar baka.

Yanzu kamar Trump yana hasashen tsaron ƙasa kan tsarin aikin-tare tsakanin ƙasashen yanki kan tsaron da ya danganci faɗaɗa da mamayar Amurka.

Canada/Tsibirin Greenland/Yankin Arctic. Wannan muhimmin hadafin ne ya bai wa Trump sha'awar ya da ƙasar Canada ta zama jihar Amurka ta 51.

Mafi ƙaranci, an yi amfani da yunƙurin wajen samar wa Amurka ƙarin ƙarfin faɗa a ji a Amurka ta Arewa.

Irin wannan hadafin ne ya haifar da yunkurinsa na sayen tsibirin Greenland, abin da yake ganin wata ɗamba ce ta mamayar yankin Arctic.

Iyaka da Mexico/Amurka ta Tsakiya/Mashigar Ruwan Panama. Irin wancan ƙudurin ne ya sa ya jibge dakaru a kan iyakar Kudancin Amurka da Mexico, ya dakatar da kwararar ƴan cirani daga Amurka ta Tsakiya sannan ya karɓi iko da mashigar ruwa ta Panama da sunan tsaron ƙasa, domin kassara ƙawance tattalin arziƙin China a yankin Latin Amurka.

A wajen yankin Amurka, Trump yana neman samun ƙarfin faɗa a ji da zafi zafi kamar yadda gwaninsa, shugaban ƙasa William Mckinley ya yi, sama da shekaru ɗari da suka gabata.

A wannan gagarumin wasa, ya dogara da manyan ƙawayen Amurka da ba sa ƙungiyar NATO a matsayin wasu ƙarin-sansanonin sojin Amurka.

Isra'ila/Yankin Gabas ta Tsakiya. Manufar Trump kan yankin Gabas ta Tsakiya ta bayyana ne bisa gagarumin goyon baya da yake bai wa Isra'ila, wanda ake amfani da shi wajen muhimmantar da matakin soji a yankin, da Saudiyya, wacce ake yi wa kallon ƙusa wajen kawo zaman lafiya a yankin, da kuma ɗaukar matakin ba-sani-sabo kan Iran.

Kuskuren lissafi zai iya dawo da yaƙin Gaza ya dawo sabo kuma ya haddasa bazuwar rikici a yankin ta wajen Iran.

Ukraine/Rasha. Trump ya yi imani biyan buƙatar Amurka ne a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ba tare da ɓata lokaci ba, amma yana son ƙulla sahihiyar yarjejeniya da Putin.

Kamar yadda waɗanda suka gabace shi suka yi tare da marigayi tsohon shugaban Rasha, shugaba Gorbachev, yana fatan ya sa Rasha ƙarƙashin Putin ta juya wa China baya, abin da ba zai yiwu ba.

Taiwan/Asia ta Gabas. A shekarar 2016, ya zama shugaban Amurka na farko tun shekarar 1979 da ya tattauna kai tsaye da takwaransa na Taiwan.

Ya ƙara yawan sintirin sojin ruwan Amurka a Tekun Taiwan sannan ya buƙaci a sayar wa Taiwan ƙarin makamai amma kuma yana don Taipei ta biya ƙarin kuɗi domin samun kariyar Amurka.

Duk wani kuskuren lissafi a kan China zai iya haddasa mummunan tashin hankali a yankin da zai haifar wa duniya babban bala'i.

Philippines/Kudu Maso Gabashin Asia. A watan Yuli na shekarar 2020, gwamnatinsa ta sanar cewa za ta yi watsi da kusan duk wani iƙirarin China kan mallakar wani yanki a Tekun Kudancin China. Taku ne na ci gaba da samun gindin zama a Taiwan. Yiwuwar tafka irin wancan kuskuren lissafin babba ne.

Najeriya/Afrika. A yankin Afirka kudu da Sahara, Trump ya bayar da umurnin ƙaddamar da hare hare kan mayaƙan jahadi a Somalia da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Hakan ya biyo bayan wani harin ne a Arewa maso yammacin Nijeriya, wata ƙawar Amurka ta kusa a yankin kuma babbar mai sayen makaman Amurka.

Ta hannun rundunarta ta Afrika, da ke da hedkwatar a Stuggart, ƙasar Jamus, rundunar sojojin Amurka na tafiyar da sansanonin soja guda 30 a nahiyar mai ɗimbin ma'adanai amma kuma mai fama da talauci.

Gwamnatin Trump na neman faɗaɗa a yankin Amurka ta Arewa, tsaron haɗin gwiwa a faɗin yankunan Amurka da kuma gagarumin ƙarfin faɗa a ji a wasu muhimman yankunan duniya.

Waɗannan muhimman manufofin za su ƙara ta'azzara kasadar tattalin arziƙi da barazana a yankunan duniya - kar ma a yi batun kuskuren lissafi da zai haifar da mummunan bala'i a duniya.

TRT World