Daga Yohannes Habteselassie Adhanom
Tashin hankali yana kaurewa yayin shagulgulan 'yan Eritriya a kasashen ketare, an samu haka a Kanada da Sweden da Jamus da kuma yanzu a Isra'ila.
Tashin hankalin yana da daure ka a ce mutum yana zanga-zanga kan kasarsa ta asali saboda dalilan siyasa a matsayinsa na dan gudun hijira, wanda hakan ba zai taba zama hujja ta karya dokar kasar da ta ba ka mafaka da 'yancin yin zanga-zangar lumana kan kasar ta asali ba.
Abin da ya fara a matsayin rikici ko ta da zaune tsaye, yanzu a shekarar 2023 ya zama abin da ke bukatar nazari da kula. An fara shagulgulan shekaru da dama da suka wuce, an fara ne lokacin da ake fafutikar neman 'yancin Eritriya daga mulkin Habasha.
Ko da yake, an sha ganin zanga-zanga yayin shagulgulan 'yan Eritriya da ke ketare tun shekarar 2001, wani martani ga gwamnatin Isayas wacce ba zababbiya ba ce.
Gwamnatin ta kasance a kan mulki ba tare da amincewar wadanda ake mulka ba har tsawon shekara 30. Wadannan zanga-zanga da na lumana ne wadanda a shekarar 2023 suka rikida zuwa zanga-zanga tashin hankali.
Tambayar da ake yi ita ce: me ya kawo wannan sauyin? Ga wadanda suke bibiyar al'amura a Kuryar Gabashin Afirka – abu ne mai sauki ka gane inda aka dosa.
Amma sanannen abu ne adadin masu neman mafaka da yawa da ke da shaidar katin Eritriya, 'yan Habasha ne daga Tigray. Jam'iyyar Neman 'Yancin Tigray (TPLF) ta mulki kasar Habasha har tsawon shekara 27 kafin hambarar da ita a shekarar 2018, abin da ya sa ta fara yaki da gwamnatin kasar.
Daukar wannan mataki ya hada har da takalar Eritriya, wanda hakan ya jawo wa jam'iyyar TPLF rashin nasara a bara.
Jam'iyyar TPLF da magoya bayanta sun fara kamfen din kawo baraka a tsakanin kungiyoyin 'yan hamayya a Eritriya, inda ake kokarin haddasa husuma tsakanin kasar Eritriya da jama'arta, duka a burin samar da kasar Tigray wato ‘Greater Tigray’.
Suna da wani tsari na maye gurbin ainihin 'yan hamayyan Eritriya da 'yan Tigray, ana amfani da wasu 'yan Eritriya da suka juya wa kasarsu baya wadanda ake boyewa da su, wannan ba abin mamaki ba ne.
A shekarun da 'yan Eritriya suke neman mafaka a Habasha don su kauce wa aikin yi wa kasarsu hidima, da yawansu sun kare ne a Tigray.
Ta hanyar amfani da wannan dama, gwamnatin TPLF wadda take mulki a gaba dayan Habasha, ta kwace katin shaidar 'yan Eritriya kuma sai ta bai wa jami'an Tigray wadannan takardu, abin da ke ba su damar neman mafaka a Kasashen Yamma da takardun wasu.
An assasa wannan dabara ta hanyar yi farfaganda a rediyo, inda ake jan hankalin matasan Eritriya da alkawura na samun saukin shiga Turai da Amurka da kuma Kanada idan suka isa Tigray.
Bugu da kari, gwamnatin ta jefa 'yan Eritriya cikin tsanani da azabtarwa da fyade da kashe-kashe, abin da ke jawo rarrabuwar kawuna da danniya a sansanin 'yan gudun hijira.
Yayin da ba za a iya kiyasta girman ta'asar da aka aikata ba, za a iya cewa sansanonin 'yan gudun hijira a Tigray ya zama bala'i ga 'yan Eritriya.
Duk da yadda al'amura suke ba duka mutanen da ke magana da harshen Tigrigna kuma suke ikirarin su 'yan Eritriya ne, aihinin 'yan Eritriya ba, da yawa daga ciki 'yan Habasha ne 'yan Tigray.
An kwashe shekaru 'yan Habasha 'yan Tigray suna shiga cikin 'yan Eritriya 'yan hamayya wadanda suke zaune a ketare.
Kololuwar bayyanar wannan kutsen ya yi arashi da takalar da jam'iyyar TPLF ke yi wa Eritriya, abin da ya jawo 'yan hamayyar Eritriya da masu goyon bayan gwamnatin kasar suke nuna goyon baya ga sojojin kasar, wadanda suke kare kasarsu ta haihuwa.
Dakarun kasar sun dakile tasirin TPLF, abin da ya kawo 'yan hamayyar Eritriya da masu goyon gwamnatin kasar kusa da juna.
An dauki wannan matakin ne don kare kasarsu ta haihuwa yayin lokacin yaki, ba wai goyon bayan yadda ake tafiyar da kasar ba.
Halartattun kungiyoyin 'yan hamayya, wadanda ra'ayinsu ya bambanta da gwamnatin kasar, suna goyon bayan daukar matakan kishin kasa a ko da yaushe, inda suke kira da sauyin gwamnatin cikin lumana a cikin Eritriya, ba tare da tsoma baki daga waje ba.
An kafa wata kungiya a Eritriya da ke da alhakin warware matsalolin cikin gida ta hanyar lumana, ba tare da sa hannun kasashen waje ba saboda gudun ta da zaune tsaye ko kuma husuma.
Saboda yadda rikicin ya sha karfin 'yan sandan Isra'ila, hakan ya jawo asibitoci a birnin ayyana aikin gaggawa, wannan babban tashin hankali da aka dade ba a ga irinsa ba, tun bayan rikicin da ya barke yayin intifada Falasdinawa a karo na biyu a watan Satumbar shekarar 2000.
Yana da wuya a kalli wannan "rikici" a matsayin sahihiyar fafutikar kwato hakkin 'yan Eritriya. Ainihin 'yan Eritriya za su so su ja hankalin jama'ar kasarsu ne ta hanyar neman sauyi cikin lumana, maimakon su jefa su cikin tashin hankali kamar irin wanda aka gani a sassan duniya.
Abin da ya fito fili shi ne TPLF, wadda ba ta yi nasara ba, ta kitsa wasu ayyuka da jami'an 'yan Tigray na bogi, wanda suke da takardar shaidar 'yan Eritriya da ba nasu ba ne, saboda su kawo cikas ga hadin kan Eritriya, don su nuna cewa 'yan Eritriya suna da matsala a zamantakewarsu a siyasance a wajen kasarsu.
Batun gaskiya kan 'yan Eritriya shi ne su masu son bin doka da oda ne saboda sun gaji tsarin hakan tun iyaye da kakanni.
Daga tuta mai launin shudi yana da tarihi, saboda yana ishara ne ga wani zamani da ya wuce, yanzu ana yin haka ne don tuna wa da lokacin mulkin mallakar Habasha, wani lokaci da Eritriya ta fuskanci danniya da kuma ya sa ta fara fafutikar neman 'yancin tsawon shekara 30.
Nuna wannan tutar da wasu 'yan Tigray suke yi da tayar da zaune tsaye duka ayyuka ne na jam'iyyar TPLF da masu goya mata baya, wanda suke son wannan tashin hankalin ya ci gaba.
Sabanin shagulgulan da suka gabata, shagulgulan 'yan Eritriya da ke zaune a ketare na 2023, ya fuskanci tashin hankali.
Tambayar ita ce: mene ne abin da ya canja? Fatanmu ne a fayyace ainihin dalilin da ke sa a yi shagulgulan da kuma majiyar da aka samu bayanai, a fade su yadda suke – wato jam'iyyar TPLF wadda take kokarin ba ta sunan mutanen Eritriya.
Wadanda aka sa musu shakku a rai suna tunanin cewa 'yan Eritriya ne ke kai wa juna hari, zai fi kyau su samu bayanansu daga majiya mai tushe maimakon daga rahotanni marasa zurfi na kafafen yada labaran Kasashen Yamma, wadanda suke yawan kuskure-kuskure idan aka zo batun Afirka da 'yan Afirka.
Yohannes Habteselassie Adhanom, tsohon malami ne a Jami'ar Asmara. Mai bincke da nazari kan kan yadda dokokin al'adun kasar Eritrea suka rika sauyawa a tarihi.
Togaciya: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin TRT Afrika ba.