Gabon ce kasa ta baya-bayan nan da aka yi juyin mulki a Afirka.  Hoto: Others

Daga Nana Dwomoh-Doyen Benjamin

A tarihin siyasa, juyin mulki abu ne da aka fara gani babu zato babu tsammani wanda ya yi tasiri kan kasashe kuma ya sa aka sake shata taswirar siyasa.

Tsawon shekaru da suka wuce, nahiyar Afirka cike take da al'adu mabambanta da dimbin arziki a kwance a cikinta, kuma ta kasance wata nahiya mai samar da sauyi a siyasance.

Shugaba Sylvanus Olympio ya kasance babban mai ba da kwarin gwiwa a sabuwar kasar da ta samu 'yancin kai, kasar ta fuskanci juyin mulkin cikin gida, abin da ya aike da sako ga sassan nahiyar.

Rashin tabbas din siyasa ya biyo bayan fara hakan wanda ya karade nahiyar Afirka.

Ghana karkashin Nkrumah

Ghana wacce ita ce kasa ta farko da ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a yankin Kudu da Hamadar Sahara, tana da muhimmanci a tarihin nahiyar Afirka.

Mutum mafi muhimmanci shi ne Kwame Nkrumah, dan kishin kasa mai hangen nesa wanda burinsa shi ne ya nuna kwarewar bakar fata a fannin shugabancin kansu.

Kwame Nkrumah, dan kishin kasa ne mai hangen nesa wanda burinsa shi ne ya nuna kwarewar bakar fata a fannin shugabancin kansu. Hoto: Getty Images 

Saboda amannar da ya yi kan hadin kan gaba daya 'yan Afirka, Nkrumah ya mayar Ghana abin misali ga gaba daya nahiyar Afirka.

Ko da yake cikin manyan burukan da Nkrumah yake da su an samu baraka. Tsare-tsarensa don al'umma da wasu manufofinsa sun jawo rashin jituwa.

A shekarar 1966, wasu gamayyar hamayya da muradun kasashen waje sun kitsa juyin mulki, abin da ya tilasta wa Nkrumah yin hijira.

Burinsa na ganin an samar da nahiyar Afirka mai cin gashin kanta, wanda aka fara ganin haka a wajen yadda Ghana ta fara samun ci gaba, har yanzu bai kammalu ba. Kifar da Nkrumah ya canja yadda tarihin Ghana ya kasance sosai.

Wannan ya yi tasiri ga sauran sassan nahiyar Afirka. Ghana wacce ita ce a sahun gaba wajen samun 'yanci a Afirka, ta samu kanta a jerin juyin mulki soja iri-iri.

Halin da Ghana take ciki ya yi tasiri a gaba daya nahiyar Afirka, daga yakin Biafra a Nijeriya zuwa zamanin Idi Amin a Uganda.

Sojojin Tanzaniya sun hambarar da Shugaba Idi Amin a shekarar 1979. Hoto: Reuters

Kowane juyin mulki yana da sarkakiya da tsoma bakin kasashen ketare da kokarin samun iko.

An shirya tsaf don fafutikar wanzar da akidoji da manufofin siyasa a Angola da Mozambique da kuma wasu kasashe da dama, inda aka bar wasu kasashe a tarwatse kuma al'umma suka yi hijira.

Mummunan tasirin Yakin Cacar Baki

Yakin cacar baka, wani abu da ya yi tarihi kan tarihi, ya yi mummunan tasiri kan Afirka. Manyan kasashen duniya suna kokarin samun iko, suna kallon kasashe a matsayin karnukan farauta a fagen siyasar duniya.

Ana yaki da manufofin juna ta hanyar yaki a kaikaice inda ake amfaninda karfin soji a boye, kuma ana amfani da juyin mulki a matsayin babban makami.

Angola da Mozambique sun kasance a tsakiyar rikicin yayin da bangarori biyu da ba sa ga maciji suke samun goyon baya daga Amurka da kuma Tarayyar Soviet.

Nahiyar ta zama bakin daga, kuma ana amfani da juyin mulki a lokacin da aka so.

Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore ya tattauna da Shugaban Rasha Vladmir Putin a taron kasuwanci na Rasha da Afirka a watan Yuli. Hoto: Reuters

Tasirin amfanin da karfin sojin yana nan har tsawon lokaci, kuma ya bar tabanni da za su ci gaba da yin tasiri a siyasar Afirka har zuwa yanzu.

Albarkatun da Afirka take da su, kama daga man fefur din Nijeriya zuwa lu'u lu'un Saliyo da sinadarin Cobalt da zinare na Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo, sun dade da kasancewa alheri kuma a lokaci guda bala'i.

Wannan arzikin yana da karfin canja kasashe, sai dai kuma yana da karfin haifar da cin hanci da rashawa da jawo rikici da kuma yunkurin juyin mulki.

Tarihin Nijeriya cike yake da juyin mulki wanda hakan ke da nasaba da yadda ake kokarin kwace iko da kudin man fetur. Haka zalika karbe iko da kudin man fetur ya jawo rashin tabbas a siyasance a kasashe kamar Equatorial Guinea da Sudan.

Kokarin karbe iko kan wadannan albarkatu yana jawo cikas ga mulkin dimokradiyya da kwanciyar hankali.

Gazawar shugabanci

Raunin cibiyoyin dimokradiyya da shugabanci ya jawo matsalolin siyasa da yunkurin juyin mulki akai-akai a kasashen Afirka da dama.

Shugabanni da suke matukar kwadayin mulki suna gyara kundin tsarin mulki don su ci gaba da kasancewa a kan mulki, abin da ke jawo fushin al'umma kuma ake bukatar agaji.

Shugaban juyin mulki na Mali Assimi Goita ya yi juyin mulki a 2021. Hoto: Reuters

Mali kasa ce da take fama da rashin kwanciyar hankali, an yi juyin mulki a shekarar 2012 da 2020 da kuma 2021.

A duka misalan, al'umma ce ta gaji da cin hanci da rashawa da shugabanci mara kyau saboda haka take goyon bayan juyin mulkin soja don samun canji.

Yaduwar matsalar

Karuwar juyin mulki a fadin Afirka ya yi mummunan tasiri har gaban nahiyar Afirka.

Gibin shugabanci da rikicin da ya biyo baya ya yi barazana ga zaman lafiya a yankin, abin da ya jawo mutane fada wa matsanancin hali da raba su da muhallinsu.

Dimokradiyya ce ta fi cutuwa, inda aka hambarar da zababbun shugabanni, kuma ake maye gurbinsu da gwamnatin soji wadda a lokaci da dama take gallaza da muzgunawa fararen hula.

Bugu da kari wannan rikita-rikitar siyasar tana da tasiri sosai kan siyasar duniya.

Manyan kasashe na ci gaba da kokarin karbe iko a Afirka, inda kasashe kamar China suke kokarin taka muhimmiyar rawa. Tsarin siyasar nahiyar yana sauyawa, inda yake sake fasalin rawar da Afirka take taka wa a duniya.

Hulda da Faransa

A shekarun da suka wuce, kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka sun fuskanci juyin mulki ciki har da Burkina Faso da Mali da Guinea da Chadi da Nijar da kuma Gabo, inda aka danganta hakan da 'yancin cin gashin kai da rashin samun gagarumin ci gaba a wadannan kasashe.

Masu zanga-zanga a Nijar sun nemi a janye dakarun Faransa daga kasarsu bayan juyin mulkin watan Yuli. Hoto: AFP 

An alakanta juyin mulkin da aka yi a kasashen Afirka wadanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka saboda hulda ta kut-da-kut da Faransa don tarihin tsare-tsaren mulkin mallaka.

Tasirin manyan kasashe da suka yi mulkin mallaka musamman Faransa ya jawo damuwa kan take 'yancin cin gashin kai a kasashen Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

Ana kallon ci gaba da tsoma baki da Faransa take yi a al'amuran siyasan kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a matsayin take 'yancinsu na cin gashin kai.

Za a iya ganin hakan a kiraye-kirayen da magoya bayan juyin mulki da canjin tsare-tsare da hadakar sabbin gwamnatocin a kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

Sabbin shugabannin da suka yi juyin mulki a kasashen da Faransa ta yi musu mulkin mallaka sun yanke huldar siyasa da tattalin arziki da Faransar.

Sauyi cikin gaggawa

Dangantaka ta kut-da-kut tsakanin Faransa da kasashen Afirka da ta yi wa mulkin mallaka ya jawo cikas ta fuskar tattalin arziki da zama cikas ga ci gaba.

Tsare-tsaren tattalin arziki da Faransa ta kakaba a kan kasashen da ta yi wa mulkin mallaka kamar amfani da kudin bai daya na CFA franc da kayyade alherin da za su samu ta fuskar kasuwanci da iko kan arzikin kasa, wadannan sun jawo cikas ga tattalin arzikin kasashen da bambance-bambance ta fuskar zamantakewa.

Matasan Gabon sun yi murna da juyin mulkin da aka yi a kasar. Hoto: Reuters 

Rashin ci gaba da rashin wadatacciyar damar neman ilimi da kiwon lafiya da samar da guraben aikin yi da kuma rikicin 'yan bindiga masu dauke da makamai da sauransu.

Juyin mulkin da ake yi a kasashen Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka martani ne ga halin rashin ci gaba da kasashen ke ciki da kuma bukatar kawo sauyi.

Karuwar samun juyin mulki a Afirka abu ne mai sarkakiya da ke da dadden tarihi, ciki har da fafutikar siyasa da arzikin kasa da rashin kyakkyawan shugabanci da gibi ta fuskar dimokradiyya.

Yayin da ake samun ci gaba ta fuskar dimokradiyya da 'yancin, kalubalen da ke faruwa suna barazana ga wadannan nasarori da aka sha wahala wajen samu.

Magance tushen matsalar yana bukatar hada hannu waje guda wajen kare cibiyoyin dimokradiyya da assasa shugabanci nagari da dakile tsoma bakin kasashen ketare masu kokarin juya akalar alkiblar siyasar Afirka.

Ta wannan hanyar ce kawai Afirka za ta samu makoma wadda ba za ta rika ganin juyin mulkin soji ba, kuma ta iya cimma duka burinta a idon duniya.

TRT Afrika