Babban Taron MDD karo na 78 a birnin New York/ Hoto: Reuters

Daga Andebrhan Welde Giorgis

An kafa Majalisar Dinkin Duniya a 1945 bayan Yakin Duniya Na Biyu don dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, samar da kyakkyawar alaka tsakanin kasashe, habaka cigaban zamantakewa, inganta halin rayuwar dan adam da kare hakkokinsu.

Kwanan nan an kara yaki da sauyin yanayi a matsayin daya daga cikin manufofin kafa MDD.

Sai dai kuma, kalubalen siyasa, tsanantar hamayya tsakanin kasashe musamman ma manyan kasashen biyu da suke daga kasashe biyar mambobiin dindindin na Kwamitin Tsaron Majalisar, na hana ruwa gudu a ayyukan sauke nauyi da take yi.

Rashin ikon cimma manufofinta ne yake hana ta taka rawar da ta kama a duniya musamman ma ga Afirka.

Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin da ke karkashinta sun dauki matakan cimma sakamakon mai kyau wajen warware rikici, tabbatar da zaman lafiya, tsaro, kare hakkokin dan adam, daidaiton jinsi, cigaba mai dorewa, taimakon jin kai, hana yaduwar nukiliya, kwance bama-bamai, kwace makamai, tsare muhalli da sauran su.

A yayin da nasarar da aka cimma ba ta kai yadda ake bukata ba, duba da manufofin kafa Majalisar, amma MDD na ci gaba da zama mai taka rawa sosai wajen tabbatar da tsaro a duniya.

Mamayar Yammacin Duniya

Samar da Majalisar Dinkin Duniya ya baiwa wadanda suka yi nasara a yaki damar zama mambobin dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar. Kasashen P5 su ne China, Faransa, Rasha, Ingila da Amurka.

Yakin Cacar Baki ya ga yadda aka rabu gida biyu, Gabashin Duniya da Soviet ke jagoranta da Yamma da Amurka ke ma jagoranci. Bangarorin biyu na gasar samun karfin fada a ji a kasashe masu tasowa da ba su shiga rikicin ba.

Faransa, Ingila da kawayensu da Amurka ke goya wa baya na daga cikin kasashe 10 da ba mambobin dindindin ba ne a Kwamitin Tsaro, inda suke da babban iko kan hukumomi da cibiyoyin majalisar, ciki da har da Babban Zaurenta, Sakatariyarta, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya.

Maye gurbin Taiwan da Jumhuriyar Al'ummar China ta yi a 1971 da kuma kokari nuna 'yanci da Faransa ta dinga yi, bai sauya wani abu game da mamayar Yammacin Duniya a Kwamitin Tsaro da Tsarin ayyukan Majalisar.

Rushewar Tarayyar Soviet da kacalcala Yarjejeniyar Warsaw ne suka sanya Francis Fukuyama rubuta litattafan “end of history” a duniyar da bangare dayan da Amurka ke jagoranci ke juya wa.

Tare da hakan, tasowar Rasha a hankali da kuma durkushewar Amurka na ni da samar da wani sabon karfi a duniya, tare da samun daidaiton karfin soji saboda yadda Nukiliya ta yadu.

Tsarin tafiyar da duniya mai rassa da yawa

Saboda haka, wanzuwar zaman lafiya da tsaro a duniya, kyakkyawar alaka tsakanin kasashe, ci gaba mai dore wa, yaki da gurbatar yanayi da tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, na bukatar tsarin kasa da kasa mai kyau da za a iya tafiyar da shi karkashin MDD da ke bukatar garambawul.

Wannan na da muhimmanci ga ci gaba da rayuwar dan adam a ban kasa da kuma walwalarsa.

A saboda haka, ya zama dole a yi garambawul ga tsarin ayyukan Majalisar Dinkin Duniya - musamman ma Kwamitin Tsaro da Zauren Majalisar - a mayar da su yadda za su dinga aiki da karfin ikon bangarori da dama.

Wannan garambawul zai samar da yanayin da z a asamu wakilci bisa adalci, ya kuma kawo muhimmancin kasashe da yankuna.

Game da karfin tattalin arziki, karfin soji da yawan jama'a, misali Indiya na daya daga kasashe biyar na duniya, tana gama da Faransa da Ingila, Afirka ta candanci kujera a Kwamitin Tsaro na Majalisar DInkin Duniya.

Gazawar MDD a Afirka

Zubi da tsarin ayyukan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da aka kafa shekaru 78 da suka gabata don ci gaba da aiki da tsarin da kasashen da suka yi nasara a Yakin Duniya II suka assasa, na bukatar kwaskwarima da garambawul don samar da yanayi na adalci da zai kara karfi ga wasu bangarori.

Babban Zauren Majalisar dake da wakilcin kasashe 193, na bukatar a karfafe shi da ya zama murya daya tilo ta dukkan kasashen duniya, sannan ya samu damar yanke hukunci da daukar matakan da suka kamata, maimakon kawai sanar da abun da yake so.

Idan ba haka ba kuma, to MDD za ta dinga rasa kima da karfin fada a ji a duniya da ma Afirka.

Garambawul din da za a yi zai bayar da dama MDD ta shawo kan matsalar gaza aikata katabus sakamakon gogayya da manyan kasashen duniya ke yi wanda hakan ne ke durkusar da yunkurin sauke nauyin ta.

Yake-Yaken da aka dinga yi a shekaru kusan tamanin da suka gabata a Afirka tare da illata jama'ar nahiyar na bayyana irin gazar da MDD ke da shi a fannin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duniya.

Gazawar da ta yi na kas ashawo kan dadadden rikici a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Eritrea-Itopiya, Itopiya, Libiya, Mali, Nijar da kisan kiyashi a Rwanda, na bayyanawa karara irin rashin nasarar da MDD ke da ita, wanda ke janyo rasa karfin fada a ji a Afirka.

Jakada Andebrhan Welde Giorgis ne marubucin “Eritrea at a Crossroads: A Narrative of Triumph, Betrayal and Hope.” Shi ne tsohon Babban Jami'in Ayyukan MDD a Eritrea da Itopiya. Ya kuma taba zama Jakadan Eritrea a Tarayyar Turai. Shi tsohon Jakadan Musamman a Yankunan Manyan Tafkunan Afirka.

Togaciya: Ba lallai ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi, mahanga da manufofin dab'i na TRT Afirka ba.

TRT Afrika