Daga Kalonji Bilolo Trésor
Kwanan nan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta cika shekara 63 da samun 'yancin kai wato a ranar 30 ga watan Yuni kenan, wani lokaci na nazari kan tafiyar da aka yi da kuma yadda za a tunkari shekaru masu zuwa.
Samun 'yancin kai abu ne mai tattare da kalubale. Yakin cacar baka da tsoma baki ya shafi dangantaka tsakanin manyan 'yan siyasar kasar da Belgium wanda hakan yake da nasaba da samun iko kan albarkatun kasar.
Yayin taron Berlin da manyan kasashen duniya suka zaba wa nahiyar Afirka makoma ba tare da jin bakin 'yan Afirkan ba, ba sa mana kallon matsayinmu na kasashe, sai dai ayari-ayarin kabilu da ake tafiyar da su bisa tsarin ilimi da al'adu.
Daga nan ne sai tsarin mulkin mallaka ya zo ya sauya komai, yanzu an raba nahiyar zuwa kasashe.
Yayin mulkin mallakar Turawan Belgium, an take hakkin kakanninmu kuma an mulke su ba tsari, a wani yanayi karkasa al'umma da take hakkokinsu na 'yan Adam.
Korafe-korafen da aka yi ta yi game da dacewar kawo karshen mulkin mallaka wanda a wasu lokuta ya kunshi yake hakkin dan Adam kisan 'yan Kongo da Turawan mulkin mallakar suka yi.
Kuskuren manyan kasa
Yawancin ta'asar da aka aikata an aikata ne tsakanin 1885 zuwa 1908 daga jagororin mulkin mallakar lokacin mulkin Sarki Leopold II na Belgium.
Miliyoyin 'yan Kongo ne aka kashe ko kuma aka azabtar saboda tsananin aikin bauta da tsare-tsaren kasuwanci da ke da alaka da shigowa da fitar da danyar roba wadda aka yi wa lakabi da 'Robar Jini' saboda tashin hankalin da ke tattare da aikinta.
Bayan shekaru masu yawa na bauta, 'yancin kai sai ya zama wani abu da wuce batun cin gashin kai, ya zama wata hanya sake daidaita al'amura da kuma dawo da asalinmu na 'yan Kongo.
Yayin jerin tattaunawar da ta gabaci samun 'yancin kai, akwai wani kuskure da 'yan siyasa suka tafka wato shi ne yarda cewa samun 'yancinmu a siyasance shi ne kadai hanyar fitar da mu daga kangin bauta.
Bayan wannan akwai wasu matsaloli da ana sane aka ki magance su don su kawo rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Kongo kuma su rika haddasa tashin hankali.
Makomar kowa da kowa
Bore bayan bore, asali da tushen 'yan Kongo ya shiga matsaloli wadanda suka rusa kasar mai albarkatu da yawa da abubuwa na musamman, tana kabilu 250 kuma tana da harsuna 100.
Wasu suna cewa kasar ta yi girma sosai kuma ta wuce a kalle ta kasa daya mara bambance-bambance.
Amma gwarzon samun 'yancin kan Kongo kuma Firaiminista Patrice Lumumba, ya rika mayar da martani da wannan sananniyar jumla: "Kongo babbar kasa ce, kuma tana bukatar babbar gudunmuwa daga gare mu."
An kwashe tsawon shekaru ana munanan ayyuka, 'yan Kongo sun koma rayuwa da son arziki cikin sauki. Wani wuri ne da mutane ba su fiye damuwa da manyan batutuwa ba ko kuma makomar kasar ba.
Wane bayani za ka yi wa mutum ya fahimta kan cewa Kongo tana da hekta miliyan 80 na kasar noma, amma kuma ta kasa ciyar da jama'arta miliyan 100?
Kusan kaso 62 cikin 100 na 'yan Kongo suna rayuwa ne a kasa da dala biyu a rana a cewar Bankin Duniya, kuma cin hanci da rashawa sun yi kasar kakagida. Akwai kuma wasu kalubale masu yawa.
Ba komai da komai ba ne ya lalace
A shekarar 1977, jumlar ‘’Yiba ndambu, tika ndambu’’ jumla ce da ta karade fagen siyasa. Za a iya fassara jumlar da "Ka da ka sace komai da komai, ka rage wani abu." Ana cin dukiyar al'umma da karkatar da su.
Sai dai ba komai ba ne yake a lalace a Kongo. Mun nuna kwarin gwiwarmu duk da wadannan kalubale. Kongo ita ce kasa ta 10 a Afirka ta fuskar tattalin arziki a shekarar 2022, inda da take da dala biliyan 69 na ma'aunin GDP.
Kasar tana da mutum miliyan 45 masu amfani da wayoyin salula da masu amfani da intanet miliyan 22, kasa ce da ta samar kyakkyawan yanayi don ci gaban intanet da fasaha da kirkirarriyar basira (AI).
Kusan 'yan Kongo miliyan 10 ne suke amafani da tsarin bankin na zamani ta waya kuma fannin yawon bude ido da bangaren masana'antu na bunkasa.
Makomar Kongo tana da muhimmanci kan makomar gaba daya Afirka, saboda idan Kongo ta samu zaman lafiya da ci gaba, to hakan zai yi tasiri ga kasahen yankin.
Muna bikin cika shekara 63 da samun 'yancin kai ba tare da yin farin ciki ba. Wajibi ne mu fada wa kanmu gaskiya cewa har yanzu ba mu samu wani bangare na 'yan kanmu ba tukunna.
Sauya halayyarmu da rungumar akidunmu na asali kuma mu yi watsi da akidun Turawan mulkin mallaka, abu ne da ya kamata mu fahimta.
A kawo karshen ci da guminmu
Maimakon mika wuya, kamata ya yi Kongo ta fahimci matsalolinta da abin da ya jawo su kuma ta kara daukar saiti don samun ci gaba a Afirka da duniya musamman a dangartakarta da sauran manyan kasashen duniya ta fuskar albarkatun kasa.
'Yancin kan da kasar ta samu a siyance ta samu a madadin kudurorinta na tattalin arziki da cin gashin kai, abin da ya jawo kashe mu raban ma'adanai kamar lu'u lu'u da zinare da kuma copper.
Ya zama wajibi huldar Kongo take da sauran kasashen duniya ta zama don ci gaban duka bangarorin biyu ne.
Shekara 63 bayan samun 'yancin kai, ya kamata Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta samu ci gaban da ya fi wanda take da shi musamman ganin cewa tana daya daga cikin kasashen duniya masu arzikin albarkatun kasa.
Sai dai kasashen yamma wadanda suka mamaye bangaren hakar ma'adanai na kasar sun ci gaba ci da gumin 'yan kasar kuma cin hanci da rashawa ya yi kasar kakagida. Dole sai wannan ya zo karshe kafin Kongo ta fara cin amfanin arzikinta da cin gashin kanta.
Bai kamata albarkatun Kongo su ci gaba da jawo wa jama'ar kasar matsala ba, amma ya kamata ya zama sanadin da 'yan kasar maza da mata za su cika burinsu. Mun cancanci abin da ya fi haka.
Marubucin, Kalonji Bilolo Trésor, wani mai fafutikar ne kuma mataimakin shugaban wata kungiya mai suna Junior Chamber International a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.
A kula: Wannan ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba ne.