Ba a cika damuwa da rikice-rikicen da kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da Najeriya suke fama da su ba idan ana tattauna batun ta’addanci hoto: AP      

Daga Mubarak Aliyu

Fararen-hula da suke rayuwa a kananan garuruwa a yankin na Afirka, da rikici biyu suke fama.

A bangaren soji, ana samun cin zarafin fararen-hula a duk lokacin da sojoji suke gudanar da harkokinsu, sannan a daya bangaren, tabarbarewar tattalin arziki da rashin aikin yi da rashin ababen more rayuwa sun sa mutanen yankin da dama suna cikin kangin talauci, wanda hakan ya sa suka tsani gwamnatoci.

Matasa da dama a yankin suna rububin shiga kungiyoyin ta’addanci ne domin samun kudi, ba wai domin imani da ra’ayoyin kungiyoyin ba.

Amma duk da haka, ba a cika tattauna yadda gwamnatoci suka gaza ba wajen kawo karshen ta’addancin ta hanyar amfani da karfin soji a kasashe irin su Burkina Faso da Mali da Nijar da Nijeriya wajen magance matsalar, duk da muna ganin yadda ake cigaba da kara wa sojojin kudade a kasafin kasashen, kuma suke samun tallafi daga waje.

Wani lamari ma da ba a cika tattauna shi ba shi ne yadda cibiyoyin tattalin arziki na duniya wadanda ake kira Bretton Woods Institution wato irin su Bankin Duniya da Bankin Lamuni na Duniya suke taimakawa wajen lalata tattalin arziki, wanda shi kuma yake sa matasa shiga ta’addanci.

Tun gomman shekaru da suka gabata ne aka fara gina tubalin wannan tabarbarewar tattalin da muke gani a yanzu a lokacin da cibiyoyin kudin na duniya suka kirkiri shirin gyara tattalin arziki na Structural Adjustment Programmes da ake kira SAPS.

Daga cikin ka’idojin shirin na karbar bashi manya akwai wasu garambawul da ake yi wa tattalin arziki kamar karya darajar kudi da rage kasashe kudade da kara hanyoyin samun kudin shiga.

Da sannu sai wadannan ka’idojjin suka jefa mutane cikin talauci, da kara fadada bambanci tsakanin talaka da mai kudi, sannan mutane da dama suka rasa aikin yi.

Kungiyoyin ’yan ta’adda sun yi amfani da rashin aikin yi da talauci a yankin na Afrika wajen samun mayaka Hoto: Reuters

Bincike ya nuna cewa gazawar tsare-tsaren na mayar da tattalin arziki hannun ‘yan kasuwa sun haifar da matsaloli sosai a rayuwar mutane da siyasa.

Sakamakon wadannan matsalolin ne muke gani yanzu a yankin Sahel din, inda kungiyoyin ‘yan ta’adda suke amfani da rashin aikin yi da talaucin da suka fi yawa a yankin wajen samun wajen zama a harkokin kananan kasuwanci da sana’o’i.

Duk da hare-haren da ake kai wa a kan fararen hula masu hakar ma’adinai a Burkina Faso, akwai rahotanni da suka nuna cewa masu hakar ma’adinan sun fi son kariyar ‘yan bindiga domin samun amincin cigaba da harkokinsu.

An kiyasta cewa bangaren ma’adinan Burkina Faso da Mali da Nijeriya zai kai kimar akalla Dala biliyan biyu, kuma akwai sama da mutum miliyan biyu da suke cin abinci a harkar ko dai kai tsaya ko ta karkashin ma’aikatan.

A Arewacin Nijeriya, bincike ya nuna cewa tun a gomman shekarun baya da masana’natu suka fara lalacewa da rashin ingantaccen ilimi da karancin ababen more rayuwa, sai yanzu aka samu wata matsala ta yadda yanzu wadanda suka kammala jami’a suka fara fin wadanda ba su samu damar zuwa jami’ar ba yawa a harkokin kananan sana’o’i da kasuwanci.

Sojojin Nijar sun dade suna fama da yawaitar kungiyoyin ta’addanci. Hoto: Reuters

Wadanda suka kammala karatun ba su samu aiki ba, sun fi wadanda ba su yi karatun ba jari da sanin mutane, wanda hakan ya sa suke danne wadanda ba su yi karatun ba a harkokin idan sun shigo.

’Yan ta’adda Boko Haram ma suna amfani me da tabarbarewar tattalin arziki wajen daukar matasa marasa aikin yi ta hanyar lasa musu zumar samun kudi da ba su kariya.

Duk da sunan Boko Haram ya nuna kiyayya ga ilimin boko, tsarin kungiyar na jawo hankalin matasa ya fi karfi ta bangaren amfani da rashin aikin yi da tsame masu ilimi, ba batun addini ba.

Wadanda suke fama da talauci sun yi saurin amincewa da kiran kungiyoyin na shiga cikinsu. A yankin Tafkin Chadi, kungiyar ISWAP suna da tsari kamar na gwamnati, inda suka mamaye wasu tsibarai da kauyukan kamun kifi a yankin, sannan suke ‘amintar’ da mazauna yankin suna cigaba da harkokinsu na yau da kullum, suna karbar haraji a hannun mutanen.

Wannan tsarin na ‘yan ta’addan ya samu nasara ne saboda gazawar gwamnati, wanda alamar hakan na kara bayyana a rashin ababen more rayuwa a yankin, wanda bai rasa nasaba da tsare-tsaren gwamnati na rage kashe kudi.

A garuruwa da dama, suna sanin akwai gwamnati ne kawai idan ayarin sojoji suka zo wucewa, ko kuma jirage yaki na jefa bama-bamai a yankinsu.

Kungiyoyin ‘yan ta’adda sun fahimci cewa akwai alaka tsakanin tabarbarewar tattalin arziki da saukin sauya tunanin mutane, kuma suna amfani da hakan.

A yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, kungiyoyin agaji suna aiki wajen inganta ababen more rayuwa ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.Horo Reuters

Daga kungiyar ISWAP zuwa JNIM da Boko Haram, dukan wadannan kungiyoyin sun sauya salo yanzu, inda suke da tsarin mulki da tattalin arziki da suke gudanarwa, sannan sun samu damar kwace wasu yankunan baki daya.

Magance matsalar bambancin da ke tsakanin talaka da mai kudi yana cikin manyan hanyoyin da za a bi domin yaki da ta’addanci a yankin.

Idan ana so a samu nasara, dole gwamnati ta farka daga muhimmantar da tsarin nan da’yan kasuwa suke juya tattalin arziki, ta koma muhimmantar da jin dadin al’umma.

Haka suma cibiyoyin bayar da tallafi akwai bukatar su yi gyara, musamman wajen gudanar da tsarin tattalin arzikin da zai tafi da kowa wanda kuma zai taimaki gwamnatin kasashen wajen samar da ababen jin dadin al’umma irin su asibitoci da inganta ilimi da sana’o’i.

Haka kuma yana da matukar muhimmanci kasashen Sahel su yi watsi da duk wani tsarin tattalin cibiyoyin na duniya da za su taimaki mutanensu ba.

Mubarak Aliyu mai sharhi ne a kan harkokin siyasa da tsaro wanda ya fi mayar da hankali a kan Afirka ta Yamma da yankin Sahel.

Togaciya: Ra’ayin marubucin ba dole ba ne ya yi daidai da ra’ayoyi da ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika