Afirka
'Yan bindiga masu alaƙa da Daesh sun kashe fararen hula 20 a arewa maso-gabashin Congo
An kama fararen hular a kauyuka da dama da aka kai wa hare-hare, sannan aka tara su waje guda a daji tare da kashe su, in ji Rams Malikidogo, wani mai kare hakkokin dan adam a Mambasa da ke Jumhuriyar Dimokradiyyar Kongo.Ra’ayi
Faransa na fuskantar ƙaruwar tashin hankali na ƙyamar Musulmai da shari'ar ta'addanci ba za ta magance ba
Da kyar shari'ar da za a gabatar a nan gaba ta yi wani tasiri wurin duba karuwar ƙyamar addinin musulunci a Faransa tare da fallasa yadda ƙasar ke jan jiki wurin tunkara rawar da take takawa wajen ba da damar al'amuran da suka shafi ƙiyayya.Afirka
Isa Muhammad Bawa: Kisan Sarkin Gobir na Gatawa ya tayar da hankulan 'yan Nijeriya
Shugaba Bola Tinubu ya nuna matuƙar kaɗuwarsa game da kisan da aka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Muhammad Bawa, wanda ya bayyana a matsayin "mummuna kuma wannan dabbancin ba zai wuce ba tare da kakkausan martani ba."Afirka
Sojojin Nijeriya sun kawar da kwamandojin Boko Haram biyar da mayaƙanta 35
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kawar da kwamandojin Boko Haram guda biyar da wasu mayaƙan ƙungiyar 35 a wasu hare-haren sama da rundunar Operation Hadin Kai ta gudanar a jihar Bornon da ke arewa maso gabashin ƙasar.Afirka
Sojojin Nijar sun ce an kashe fararen-hula 15 a hare-haren 'yan ta'adda a yammacin ƙasar
Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da ƙungiyar IS da Al-Qaeda.
Shahararru
Mashahuran makaloli