Kasar na dab da samun babban sauyi da ci gaban tattalin arziki mai ban sha'awa, in ji shi, inda ya kara da cewa "abubuwan ci gaba a yankinmu za su gaggauta wannan tsarin," in ji Erdogan. / Hoto: AA

Turkiyya ta zama jagora a duniya wurin ƙera jirage marasa matuƙa haka kuma ita ce ta 11 wurin fitar da kayayyakin tsaro a duniya, kamar yadda shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana, Ya bayyana haka ne a wurin babban taron Jam’iyyar AK karo na 8 a Ankara.

Kasar na dab da samun babban sauyi da ci gaban tattalin arziki mai ban sha'awa, in ji shi, inda ya kara da cewa "abubuwan ci gaba a yankinmu za su gaggauta wannan tsarin.”

Erdogan ya ce gwamnati ta shirya wani shirin kawo sauyi ga "karni na Turkiyya," wanda ya bayyana a matsayin "mai faɗi", wanda zai "samar da ci gaban kasarmu da ƙaruwar abubuwan da ake samarwa."

Turkiyya na dab da kawar da ta’addanci

Erdogan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa, Turkiyya da yankinta na dab da kawar da ta'addanci, inda ya yi kira da a hada kai a tsakanin Turkawa, Kurdawa, da Larabawa domin kawar da dakarun da suka haddasa tashin hankali shekaru da dama.

"Insha Allahu, kwanakin da aka shafe ana fama da ta’addanci, tashin hankali, da amfani da makamai za su kau daga kasarmu da yankinmu gaba daya."

"Za mu hadu a matsayin Turkawa, Kurdawa da Larabawa, mu rusa bangon ta'addancin da ya addabi mu da ‘ya’yanmu fiye da shekara 40.”

TRT World