Turkiyya ta caccaki Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa bisa wallafa wani zane na Shugaba Recep Tayyip Erdogan bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki na ranar 14 ga watan Mayu.
Ranar Laraba Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun ya ce "zane na rashin mutunci da Mujallar Charlie Hebdo ta yi na shugaban kasarmu" wani yunkuri ne na cin zarafi da batanci ga kafafen watsa labaran duniya.
"Wannan mummunan labari na Charlie Hebdo ya sake jaddada wa duniya irin kyamar da wannan mujalla take wa shugaban kasarmu, inda ta wallafa zanen rashin mutunci nasa," in ji shi.
Altun ya kara da cewa ga dukkan alamu "gagarumar nasarar" Erdogan a zabukan 14 ga watan Mayu "ta hana wadannan marasa darajar bacci, inda suke amayar da bakin ciki da kiyayyar da suka dasa wa zukatansu."
Altun ya gaya wa mujallar cewa: “Duk abin da za ku yi, ba za ku iya yi wa Recep Tayyip Erdogan barazana ba. Ba za ku iya kawar da mu daga kan turbarmu ba."
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da Mujallar Charlie Hebdo ta yi wani zanen barkwanci a bangonta da ke nuna Erdogan a cikin kwamin wanka, tana alakanta hakan da mutuwar wani fitaccen mawaki Claude François (Cloclo) a shekarar 1978, wanda ya rasa ransa sakamakon jan sa da lantarki ya yi yana wanka a baho.
Da take alakanta Erdogan da sakon, mujallar ta rubuta: "Tamkar dai abin da ya faru da Cloclo, kaddara ce kawai za ta raba mu da shi".
Mai magana da yawun shugaban kasar Ibrahim Kalin wanda ya kira mujallar da "tsumma", ya caccake ta da cewa "abin da take yi hauka ne, kuma zanen nasu na nufin Turkiyya tana kan madaidaiciyar turba."
"Masifa a wasu lokutan haka take. Takan kai mutum ga kyakkyawan abu", in ji Kalin.
A shafin Twitter ya kara da cewa: "Kar ku damu CH (Charlie Hebdo). Kasarmu za ta ba ku amsar da ta dace da ku da babbar murya ranar 28 ga watan Mayu," yana mai alakanta batun da zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za a yi.
"Ko da yake dai E bai samu adadin kason da ake bukata don cin zaben shugaban kasa a zagaye na farko ba, alamu sun nuna karara cewa shi ne kan gaba a zagaye na biyun da za a je saboda nasararsa a zagayen farkon.
Miliyoyin masu kada kuri'a ne suka fita zabe a ranar 14 ga watan Mayu don zabar sabon shugaban kasar da 'yan majalisar dokoki 600.
Jam'iyyar Kawancen Erdogan ta People’s Alliance ta samu gagarumin rinjaye a majalisa, yayin da za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa ranar 28 ga watan Mayu, duk da cewa dai Erdogan ne ke kan gaba a zagayen farkon.
Erdogan da babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu, kuma shugaban babbar jam'iyyar adawa ta (CHP) da kuma dan takarar kawancen jam'iyyu shida na Nation Alliance, za su fafata a zagaye na biyu na zaben.
A shekarun bayam Mujallar Charlie Hebdo ta sha jawo ce-ce-ku-ce da shan suka saboda zana hotunan Annabi Muhammad, sannan a bana ma ta yi wani zanen barkwanci kan girgizar kasar da ta afkawa kasar Turkiyya ranar 6 ga watan fabrairu, inda mutum sama da 50,000 suka mutu.