Daga Karya Naz Balkiz
‘Yan shekarun da suka wuce ba a samu zubar kankara a Istanbul ba. Baya ga rashin zubar kankarar, ga dimbin cunkoson ababen hawa da sauyin yanayi da ya addabi birnin, amma a ranar Larabar nan lamarin ya sauya.
Iyaye da dama irin su Gul Ece Cakmak sun ji daɗin zubar dusar kankarar, inda mahaifiyar yara biyu ta yi gaggawar zuwa dauko ‘yarta daga makarantar reno don ta yi wasa a dusar kankara.
“Suna shewar farin ciki a lokacin da suke tafiya gida, suna kallon dusar kankarar na zuba a jikin tagar motarsu,” in ji ta.
A wajen ‘yarta Duru mai shekaru 6, hada mutum-mutumi da dusar kankarar shi ne cinyewa a lokacin sanyi.
“Idan kankarar ta taba fuskata akwai sanyi. Amma na hada mutum-mutumi da ita, ba na jin sanyin sosai,” ta fada aa TRT Afrika.
A wajen Bade mai shekaru biyu kuma, wannan dusar kankarar lamari ne mai girma a rayuwarta saboda ita ce ta farko da ta gani.
"Dusar kankarar da ta zuba a makon da ya gabata ba ta da yawa, shi ya sa ba mu ga wani bambanci ba.
"Amma a wannan karon, na ji dadin ganin dan hancinta ya yi ja saboda daga kanta sama tana kallon yadda fale-falen dusar kankara ke zuba a kan fuskarta,” Cakmak ta fadi haka game da Bade.
Duk da Bade ba za ta iya bayyana me take ji ba, kawai tana ta maimaita kalma daya ne “Kar” dusar kankara kenan a harshen Turkanci.
An soke tashi da saukar jiragen sama, an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa
A yayin da yara ke murna da farin ciki kan “hutun makaranta saboda dusar kankara”, an samu tsananin cunkoson ababan hawa a Istanbul a yammacin Laraba. Inda matafiya suka dauki awanni kafin su je inda suke son zuwa.
A yayin da aka rufe hanyoyi tare da jinkirta motsawar motocin bas, mutane sun yi dogayen layuka suna jiran zuwan motocin, wasu kuma sun taka da kafa zuwa gida.
Haka kuma, manyan filayen jiragen saman Istanbul guda biyu sun rage yawan jiragen da za su kula da su. Kamfanin jiragen saman Turkiyya, ya soke tashin jiragen sama 200.
A yayin da dusar kankarar ta dinga sauka a mashigar tekun Istanbul, Ma’aikatar Sufuri da Gina Kasa ta sanar da dakatar da kai komon jiragen ruwa a mashigar.
Fatma Korunoglu, wata mazauniyar Istanbul ta ce dusar kankarar ta yi yawa ta yadda ba ta iya ganin gadar shahidai ta Istanbul.
A wajenta, saukar dusar kankarar ya zo da makararren farin ciki saboda yadda aka dade ba a ga hakan ba. Ta ce dusar kankarar ta karfafa gwiwar mutane, inda ta sanya su mantawa da matsalolinsu na yau.
“A yayin tafiya a Istanbul, na ga wani abu… alamun farin ciki a fuskokin mutane, har ma a ababan hawa na haya,” ta fada wa TRT World, tana mai kara wa da cewa wasu iyalan ma tuni suka fita waje don tattara dusar kankarar a yammacin Laraba.
Hukumar Kula da Yanayi ta ce dusar kankarar za ta ci gaba a ranar Alhamis a fadin Istanbul har zuwa ranar Litinin din mako mai zuwa.

Gwamnan Istanbul, Davut Gul ya bukaci mazauna birnin da su kaurace wa tafiyar da ba ta dole ba, su hakura da amfani da ababan hawansu ba tare da tayoyin lokacin sanyi ba, kuma su dogara kan ababan hawa na haya masu daukar mutane da yawa.
Ana sa ran yankunan da ke gabar teku za su samu zubar dusar kankara har ta kai tudun santimita 5 zuwa 10, inda yankunan da babu teku kuma za su fuskanci mai yawan santimita 10 zuwa 20 ko ma sama da haka a ranakun Juma’a da Asabar.
A wurare masu tsananin tudu ma za ta iya kai santimita 40.
Ana sa ran yanayi zai sauka zuwa daraja 0 zuwa 2 har nan da 22 ga Fabrairu, kai har za a iya samun saukarta zuwa -1 ko -2, in ji masanan yanayi.
Dusar kankarar na kuma sauka a yankin Tekun Bahar Maliya, inda ake sa ran sanyi zai yi yawa a garuruwa da dama. Babban birnin Ankara da wasu garuruwa da dama na tsakiyar Anatolia na fuskantar sanyi da kankarar.
Lokutan sanyi da ba a saba gani ba
Lokutan da aka fi samun zubar dusar kankara sosai a Istanbul su ne 1987, 2004, 2017, da 2022.
Korunoglu da ta zo daga garin Mersin na yankin Tekin Bahar Rum da ba a samun zubar dusar kankara sosai, ta ji dadin yadda yanayin sanyi ya kasance a Istanbul.
“A Mersin, iyaye na kai yaransu Taaunukan Taurus don su ga dusar kankara,” in ji ta. A zaman da ta yi a Istanbul, ta fahimci yadda dusar kankara ke hada mutane waje guda suna wasanni tare.
“Idan dusar na zuba, kowa na son fita waje, komai irin sanyin da ake yi. Ko karfe 1 na dare ne, za ka ga mutane a waje, na jin dadin zubar ta.”
A ranakun da dusar kankara ke zuba, tana tabbatar da ta tsaya a mashigar tekun Istanbul don shaida yadda ‘yan Istanbul suke.
“Tekun na sauya kala zuwa kore shar tare da rangaji idan dusar kankara na zuba.”