Shugaban 'yan ta'addar PKK Abdullah Ocalan, ya yi kira da a rusa dukkanin kungiyoyin da ke karkashin kungiyar ta'addancin, ya kuma bukaci kawo karshen ta'addancin da ta shafe sama da shekaru 40 tana yi.
A wata wasika da ya aike daga gidan yari, Ocalan ya ce: "Dukkan kungiyoyi su ajiye makamansu, kuma PKK ta rusa kanta."
Shugaban kungiyar ta'addanci ta PKK da ke ɗaure Ocalan, a cikin sanarwar ya ce "kiran da Mista Devlet Bahceli ya yi, tare da wasiyyar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi, da kuma kyakkyawar amsa da sauran jam'iyyun siyasa suka yi game da kiran da aka sani, ya haifar da yanayin da nake yin kira na a ajiye makamai, kuma na dauki nauyin tarihi na wannan kira."
"...Dole ne dukkan kungiyoyi su ajiye makamansu sannan PKK ta wargaza kanta."
Efkan Ala, mataimakin shugaban jam'iyyar Justice and Development Party (AK) mai mulkin kasar Turkiyya, ya amince da wannan sanarwa amma ya jaddada bukatar a jira a dauki ƙwararan matakai.
"Za mu kalli sakamakon," in ji Ala lokacin da aka tambaye shi game da kiran Ocalan.
Ya kara da cewa idan 'yan ta'addar PKK suka bi ta, to za a kubutar da Turkiyya daga ƙangin da take ciki.
A cikin yaƙin ta'addanci na shekaru 40, kungiyar ta'addanci ta PKK - wadda Turkiyya da Amurka, da EU suka amince da ita a matsayin kungiyar ta'addanci - ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutum 40,000, ciki har da mata, yara, da tsofaffi.