Za a ci gaba da jerin Tarukan a cikin Fabrairu inda za a gudanar da su a Birtaniya da Poland da Belgium da Faransa. /Hoto: AA

Ofisihin Sadarwa na Fadar Shugaban Turkiyya ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin gudanar da taruka na ƙasa da ƙasa a ƙasashe 20, don haɓaka tattaunawa kan sauye-sauyen jagoranci a duniya.

Shirin, wanda aka yi masa taken “Zai Yi Wu a Samar da Duniya Cike da Adalci”, na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na shirin Taron Ƙasa da Ƙasa kan Sadarwa da aka fi sani da Stratcom a taƙaice.

Bayan tarukan da aka gudanar a baya-bayannan a Austria, da Switzerland, da Hungary, da Netherlands da kuma Jamus, tarukan za su ci gaba a birnin Rum ranar Talata, yayin da ake shirin gudanar da wasu tarukan a manyan biranen ƙasashen Turai.

“Kalaman Shugaba Erdogan da ya ce ‘duniya ta fi girman ƙasashe biyar’ na wakiltar wani kira mai girma na gina wani tsari na duniya kan ginshiƙin adalci,” a cewar Fahrettin Altun, Daraktan Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasa, a cikin wani jawabi da ya gabatar ta bidiyo.

“Biyar” na nufin ƙasashe biyar masu kujerun din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya - Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma China.

Shirin na nuna yadda yunƙurin Turkiyya ke ƙara haɓaka don yin tasiri kan tattaunawar diflomasiyya, musamman sauye-sauye a Majalisar Ɗinkin Duniya. A ƙarkashin jagorancin Erdogan, a kowane lokaci Turkiyya na neman sauye-sauye a cibiyoyin ƙasa da ƙasa don su ƙunshi kowa da kowa.

Me zai faru gaba?

Za a ci gaba da jerin Tarukan a Fabrairu inda za a gudanar da wasu a Birtaniya da Poland da Belgium da Faransa.

Altun ya jaddada cewa maufar tarukan ita ce tsara tattaunawa tsakanin gwamnatoci da ƙungiyoyin al’umma, da kafafen watsa labarai da masu tsare-tsare.

“Ba wai kawai muna fito da matsaloli ba ne, muna mayar da hankali kan mafita,” kamar yadda ya faɗa, yana mai ƙarawa da cewa Turkiyya “tana da ƙaƙƙarfan imanin yiwuwar samun duniya mai adalci ta hanyar yunƙuri na duniya.”

Shirin ya zo ne a daidai lokacin da cibiyoyin ƙasa da ƙasa suke fuskantar saka ido kan yadda suke iya warware matsalolin duniya.

TRT World