Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya  jaddada buƙatar inganta yin aiki tare wajen magance matsalar ƙarancin abinci, da tashin farashin kayayyaki, da kawo tsaiko a hanyar safarar kayayyaki. /Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Tukiyya Hakan Fidan ya ce ba za a taɓa samun dawwamammne zaman zaman lafiya ba tare da tallafin ci-gaban tattalin arziki da wadata ba.

Da yake magana a taron ministocin ƙasashen waje na G20 ranar Juma’a a birnin Johannesburg na Airka ta Kudu, Fidan ya ce “Zaman lafiya na tangal-tangal a Siriya da Gaza da yankuna da dama na duniya. Farfaɗowar tattalin arziki da yunƙurin ci-gaba ga waɗannan yankunan ba sa ɗorewa har sai mun tsara su ta haya mai ɗorewa.”

Da yake jaddada cewa ya kamata G20 “ta ci gaba da kasancewa taro mafi muhimmanci ga haɗakar tattalin arziki na duniya,” Fidan ya ce ya kamata a ɗauki jerin matakai da sababbin ƙudurori don wanzar da jajircewar G20 da muhimmancinta.

Jami’in na Turkiyya ya bayyana cewa waɗannan matakan sun haɗa da “yunƙuri don ƙara shigarwa tare da wakiltar tsare-tsaren shugabanci na duniya, musamman ma wajen wanzar da zaman lafiya da tsaron duniya,” da “ƙara rawar da ƙasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa da ƙasashen da ke da faɗa a ji a yankuna a wajen ɗaukan matakai da yanke hukunci.”

Ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa alaƙa tsakanin G20 da wasu ƙungiyoyin, irin su Ƙungiyar Ƙasashe Musulmai (OIC), da Ƙungiyar Ƙasashen Kudu Maso Gabashin Asia (ASEAN), da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).

"Musamman ma a Tsakiyar Asia, da Gabashin Turai da Yammacin Asia, da Gabas ta Tsakiya, da bunƙasa haɗaka ta hanyar sadar da damammakin tattalin arziki na hanyanr sufurin cinikayya ta ruwa da ta tashi tun daga Turkiyya zuwa China da Gabas ta Tsakiya da aikin Bunƙasa Hanyoyin Mota, duka suna da muhimmanci wajen cim ma wannan fata,” a cewarsa.

Fidan ya jaddada muhimmancin bunƙasa ɗaukan nauyi bisa daidaito wajen tunkarar matsalar ‘yan ci-rani da masu ƙaura da kuma tallafa wa ƙasashen da suke karɓar baƙuncin ‘yan ci-rani, da wani tsari mai dorewa.

Ya kuma jaddada buƙatar inganta yin aiki tare wajen magance matsalar ƙarancin abinci, da tashin farashin kayayyaki, da kawo tsaiko a hanyar safarar kayayyaki.

TRT World