Sojojin Saman Nijeriya sun kai hare-hare a maɓoyar 'yan Boko Haram a Degbewa da Chikide a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno inda suka kashe gomman mayaƙan ƙungiyar da kuma lalata muhimman kayayyakin aikinsu, kamar yadda jami’ai suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya (AA) ranar Laraba.
An kai hare-hare ta sama ne da zummar halaka wasu shugabannin ‘yan ta’adda kuma an yi nasarar kawar da 'yan ta'adda aƙalla 30.
Da yake tabbatar da lamarin, mai magana da yawun sojin saman ƙasar, Olusola Akinboyewa, ya ce an ƙaddamar da hare-haren ne domin tabbatar da doka da oda da kuma wanzuwar zaman lafiya a arewa maso gabashin ƙasar.
“Har yanzu ana bincike bayan hare-haren. Kuma za a fitar da ƙarin bayanai idan sun samu,” in ji shi.
Hare-haren na zuwa ne kwanaki biyar bayan ‘yan ta’adda na ƙungiyar ISWAP sun kashe sojoji aƙalla 22 a Borno. Rundunar sojin ƙasar ta ce an kashe ‘yan ta’adda 70 a wancan lokacin.
An kashe sojojin Nijeriya 35 a kan aiki daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa yanzu, lamarin da ke nuna babban ƙalubalen da sojin ke fuskanta wajen yaƙar masu tayar da ƙayar baya.
Kazalika sama da ‘yan ta’adda 100 ne aka kashe a faɗin Nijeriya tun daga farkon wannan shekarar.