Talata, 25 ga Fabrairun, 2025
1330 GMT — Akalla Falasdinawa 59 da ake tsare da su ne suka mutu a gidajen yarin Isra’ila tun farkon yakin Gaza a watan Oktoban 2023, in ji wata kungiyar kula da harkokin fursunoni.
Kungiyar fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce wadanda abin ya shafa sun hada da fursunoni 38 daga Gaza.
Ta zargi mahukuntan Isra'ila da boye mutuwar fursunonin Falasdinawa da dama da ake tsare da su.
Hukumar da ke kula da fursunonin ta ce wani fursuna dan kasar Falasdinu Musab Hani Haniyeh ya mutu a hannun Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun kama Haniyeh, mai shekaru 35, daga kudancin birnin Khan Younis, a ranar 3 ga Maris, 2024. A cewar iyalansa, Haniyeh na cikin koshin lafiya kafin a tsare shi.
Alkaluman Falasdinawa sun ce akalla fursunonin Falasdinawa 296 ne suka mutu a tsare Isra’ila tun bayan mamayar da Tel Aviv ta yi wa Yammacin Kogin Jordan da Gaza a shekarar 1967.
1000 GMT — Jarirai da dama na mutuwa a Gaza saboda tsananin sanyi
Tsananin sanyi ya kashe jarirai biyar a Gaza yayin da yankin ke cigaba da kasancewa cikin ƙawanyar Isra'ila, a cewar wani likita.
"An kwantar da yara tara a asibiti cikin mako biyun da suka wuce sakamakon tsananin sanyin da ya kama su," kamar yadda Saeed Salah, daraktan asibitin Friends Benevolent Society a Gaza ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu.
"Biyar daga cikin jariran tara da aka kwantar 'yan tsakanin kwana daya zuwa sati biyu sun mutu," ya ƙara da cewa.
Salah ya ce har yanzu akwai jaririn da yake kan na'urar da take taimaka masa shaƙar iska, yayin da aka sallami wasu ukun daga asibiti.
Ƙarin labarai 👇
0941 GMT — Tsohon ministan Isra'ila 'yana alfahari' da hotunan zalincin da aka yi wa Falasdinawa fursunoni
Tsohon Shugaban Tsaro na Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir ya cika baki tare da yin alfahari a kan yadda aka tursasa wa Falasɗinawa fursunoni durƙusawa a kan gwiwarsu yayin da ake nuna su da bakin bindiga da kuma shafe fentin da suka yi a kan bangwayen gidan yarin da suka hada da "Birnin Ƙudus na Larabawa."
"Ina alfahari da Hukumar Gidan Yarin Isra'ila na Ktzi'ot da ke yankin Negev, an gano yadda aka rubuta wasu kalamai masu alaƙa da addini a jikin bangwayen gidan a bangaren ma'aikatan tsaro, " kamar yadda Ben-Gvir ya rubuta a shafin X ranar Litinin.
Fursunonin Falasdinawa sun rubuta kalmomi kamar "Ba za mu manta ba, ba za mu yafe ba, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba, Kudus ta Larabawa ce," in ji tsohon ministan, wanda kuma ke jagorantar jam'iyyar siyasa ta Yahudanci mai tsattsauran ra'ayi (Otzma Yehudit).
0855 GMT — Masar ta ƙi amincewa da ƙaurar Falasdinawa ta ce barazana ne ga tsaron kasa na kasashe
Masar ta yi watsi da shawarwarin raba al'ummar Falasdinu saboda kar a "rusa" fafutukar Falasdinawa da kuma kauce wa barazana ga tsaron kasa na kasashen yankin, a cewar wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasar Masar ta fitar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya harzuƙa kasashen Larabawa da wani shiri na korar Falasdinawa sama da miliyan 2 daga Gaza, yana mai cewa Amurka za ta karbe yankin da kuma mayar da shi wajen shaƙatawa na Gabas ta Tsakiya