Shugaban kasar Amurka Joe Biden na rikici da majalisar wakilai kan ciyo bashi. Photo: Reuters

Daga Dayo Yusuf

Idan ana maganar tattalin arzikin duniya, tsawon gomman shekaru Amurka na kan gaba a duniya.

Muna tunani da kallon kasar a matsayin mafi karfi a duniya, saboda abubuwan da take da su.

Tabbas, shin ba shi ne dalilin da yake sanya mutane da yawa suke tattara kayansu, su sayar da kadarorinsu su yi bankwana da iyalai da dangi da abokai – su koma can da zama? Zuwa kasar da ake wa kallon aljannar duniya?

Amma watakila wannan abu a baya ne yake haka. Ba ka bukatar yin dogon kallo da tunani don fahimtar lallai akwai matsaloli a wannan aljanna ta duniya.

Majalisar dokokin Amurka ta tafka zazzafar muhawara kan ko za a iya bai wa gwamnatin Biden damar kara yawan bashin da za ta iya ci.

Ranar kin dillanci ce ke matsowa?

Tun 2001, Amurka ba ta iya takaita kudaden da take kashewa ba, saboda ba ta samun yawan kudin da take kashewa. Kuma wannan lokaci ya ga yadda kashe kudi da kasar ke yi ya karu sosai.

Ko tana daukar nauyin habaka fasahar kere-kere da yake-yake ko magance sauyin yanayi, kasar dai ta dinga gwagwarmayar tsayawa a kan kafafunta.

Sanata Rick Scott a tsakiya a yayin taaron manema labarai inda suke kira ga shugaba Biden da ya tattauna da majalisar wakilai kan ciyo bashi. May 3, 2023. Photo: Reuters.

Tsawon shekaru gwamnatoci sun dinga ciyo bashin kudade don tabbatar da kasar ta ci gaba da motsawa kamar ko yaushe.

Amma akwai takaita ciyo basussuka, wanda a ilimin kasafin kudi ake kira da “Iyakance bashi”. Idan ba a kara yawan wannan iyaka ko dakatar da ita a kan lokaci ba, ko kuma kafin kasar ta rasa kudin gudanarwa, hakan zai sanya ta gaza biyan basussukanta a kan lokaci sannan ta kasa tafiyar da al’amuranta.

Wannan wa’adi na gabatowa cikin sauri. Da fari dai, lalitar Amurka ta yi tsammanin ci gaba da bai wa kasar kudaden kashewa da suka yi saura har nan da watan Agusta.

Amma bayan sake nazari da aka yi, sai lalitar ta sanar da ba za ta iya bayar da kudi ba bayan 1 ga Yuni.

Daga ina Amurka ke cin bashi?

Kamar yadda aka dauke ta kasa ‘mai arziki’, da wahala a iya hasashen wai Amurka na ranto kudade daga wani waje. Amma kuma tana rantowar.

Kuma abun ban mamakin shi ne kasar da Amurka ke yawan suka da kalubalanta ce ke kubutar da ita: China.

"A yanzu haka babbar barazanar Amurka ba Rasha ba ce, China ce” in ji Dr. Anthony Francis Mveyange, masanin tattalin arzikin kawo cigaba da ke Kenya.

“Kuma Amurka za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ba ta gaza biyan China bashinta a kan lokaci ba,” in ji shi.

Tun 2011, iyakance bashin da Amurka kan iya ciyowa yake ta karuwa daga dala biliyan $11.9 zuwa dala tiriliyan $31.4.

Amma saboda yadda kasar ba ta da isassun kudaden da za ta rike kanta da kanta wajen kashe kudade, hakan ya sanya dole a dinga ranto kudade daga wurare sama da guda.

Manyan masu bai wa Amurka bashi:

Japan – Dala tiriliyan $1.1

China -- Dala biliyan $859

Birtaniya - Dala biliyan $668

Duk wannan kaso 31 ne na bashin da ake bin Amurka. Kasar na kuma ranto kudade daga cikin gida, wanda shi ne yake kaso 69 da ya rage.

Wannan bashin na zuwa daga ‘yan kasuwar cikin gida da bankunan Amurka da kudaden fansho da kudaden hadin gwiwa da gidajen mutane.

Shugaban kasar Amurka Biden na daga hannu ga shugaban China Xi Jinoing a yayin ganawa ta yanar gizo a ranar 15 ga Nuwamba 2021. Photo: Reuters

Masana tattalin arziki na cewa ya kamata a kalli rikicin bashin da ake bin Amurka ta sigar da ta bambanta da basussukan sauran kasashe.

“Amurka ba za ta taba gaza biyan bashinta ba kamar yadda ya faru ga Girka, ko Ajantina, ko Zambia ba. Saboda rikicin bashin na Amurka bai faru sakamakon matsalar tattalin arziki ba, sai don matsalolin da dan adam ya janyo’, in ji Mveyange.

Me zai faru idan ta gaza biyan bashin?

A mafu munin yanayi, idan nan da 1 ga Yuni ba a cimma matsaya ba, kasar za ta fuskanci mummunan sakamako.

Na farko dai shi ne rashin aminta, wanda bai taba faruwa a baya ba, duk da wasu lokutan an kusa fuskantar hakan.

“Kamar yadda yake ga bashin da ka ci ne, gaza biya zai zama ka kasance wanda ba za a iya dogaro a kan sa ba kenan. Masu bayar da bashi ba za su sake yarda da gasgata Amurka ba kan batun biyan bashi", a fadin Mveyange.

Sannan sai tsadar ranto kudaden, wanda shi ne tasirin sake tattauna sharuddan bayar da bashin.

“Babu wanda yake son saka kudadensa cikin hatsarin bayar da bashi ga wanda ba zai iya biya ba. Shi ya sa ko ka yarda ka ba shi bashin, dole sai ka kara yawan kudin ruwa don kar ta kwana. Mun ga yadda hakan ke faruwa ga kasashen Afirka,” in ji Mveyange.

Yau da gobe ne batu na uku da lamarin zai shafa. Ga gwamnatin da ta dogara kan bashi don gudanar da ayyukanta na yau da kullum, ba za ta taba samun hanyar matsawa gaba ba.

Masu fafutuka na Amurka sun bukaci kara aadin bashin ba tare da yanke albashin ma'aikata ba. Photo: AA

Za a rufe ayyukan gwamnati da dama, ba za a iya biyan albashi ba, haka ma ba za a iya biyan ‘yan fansho ba, za a dakatar da samar da kayayyaki.

Haka zalika, kamfanoni za su takura ta yadda dole su rage yawan ma’aikata, rashin aikin yi zai jefa kasa cikin matsin tattalin arziki, sannan kuma idan ba a dauki mataki nan da nan ba, hakan zai janyo asarar tattalin arzikin da ba za ta mayarwa ba.

Idan aka kai ga yanayin da gwamnati ba za ta iya baiwa bankuna kudade ba, mutanen da suka ajiye kudade a bankuna za su yi kokarin janye ajiyarsu.

Wannan na nufin bankunan za su durkushe. Kenan ba makawa za a shiga matsalar durkushewar tattalin arziki.

Bata suna a siyasance

Mveyange ya bayyana cewa, sa-toka-sa-katsi tsakanin ‘yan Democrat da ‘yan Republican ta dade tana faruwa.

“Mun ga haka a 2011, lokacin Barack Obama. “Yan Republican sun yi yunkurin gurgunta gwamnatin, sai suka yi amfani da kayyade cin bashi a matsayin makaminsu,” in ji masanin tattalin arzikin.

Za a iya dora laifi kan ‘yan Democrat da ‘yan Republican idan ana maganar wannan batu na rikicin bashi.

Mambobin majalisa da aka zaba a ginin Capitol na Amurka da ke ashington a ranar 22 ga Nuwamba 2022  Photo: Reuters

A yayin muhawara a majalisar dokoki, mafi yawa na neman masu adawa da su amince da bukatar da aka kawo, ya dogara kan waye a kan mulki a lokacin. Wannan ba ya nufin shugaban kasa ba zai samu mafita ba.

A yanayi mafi mauni, kamar yadda ya faru ga Obama, shugaban kasa na iya yin barazanar amfani da sashe na 14 na kundin tsarin mulkin Amurka wanda ya bai wa shugaban kasa damar tsallake majalisar dokokin don daukar irin wannan mataki.

Amma masu nazari na cewa wannan zai kara rura wutar rikicin ne tare da shigar da kara kotu.

Mveyange ya kuma ce “A yanzu, gwamnatin Biden na dogaro ne kan yadda mafi yawan ‘yan Republican da ke majalisar wakilai mamallakan manyan kasuwanci ne, kuma ba za su so a fada matsalar durkushewar tattalin arziki ba.”

Da yawan masu nazari sun aminta da cewar akwai hadin kai da cimma matsaya tsakanin ‘yan majalisar dokokin, kan kar a kyale Amurka ta gaza biyan bashin da ake bin ta, wanda hakan zai sanya Amurka rasa darajarta a duniya.

Mveyange ya yi hasashen cewar “ba za su taba bayar da dama ga tattalin arzikin kasar ya durkushe ba, sai dai idan suna son su rasa matsayinsu na kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya”.

Ya ci gaba da cewa “Idan har suka bar hakan ta faru, tabbas jama’ar Amurka ba za su yafe musu ba.”

TRT Afrika