An karbi noman zogale da hannun bibbiyu a halin yanzu a Nijeriya maimakon yadda a baya ake barinsa yana tsirowa da kansa a daji./Hoto:Eden Moringa

Idan ana neman wani abu da ke inganta lafiya da kare duniya daga halaka a cikin tsirrai, to lallai za a yi magana a kan zogale saboda amfaninsa.

Bushasshen ganyen bishiyar zogale mai saurin girma da kuma iya jure fari na cike da sinadarin bitamin C fiye da lemo sau bakwai, da sinadari mai gina jiki fiye da kindirmo sau 9 da sinadarin calcium fiye da madara sau 17.

Kazalika yana da sinadarin iron fiye da alayyahu sau 25 da sinadarin bitamin A sau 10 sama da karas da kuma sinadarin potassium sau 15 sama da ayaba.

An bayyana irin amfanin da zogale ke yi wa jiki cikin bincike-bincike da aka wallafa a mujallun kimiyya da dama ciki har da wani rahoton da aka wallafa a mujallar kimiyya ta kasa da kasa ta Phytotherapy Research, a shekarar 2013.

Wadanda suka shiga harkar noman zogalai sun ce akwai  riba sosai a cikinta :Hoto/Eden Moringa

Yayin da karin sassan duniya ke kallon zogale a matsayin wani ganye na sha-yanzu-magani-yanzu, Afirka, inda bishiyar ke tsirowa a daji ba tare da shuka ta ba, ta fara kokarin cin gajiyar harkar kasuwancin ganyen bishiyar.

A baya dai ana yi wa zogaye kallon abin da ake ci ne kawai a arewacin Nijeriya, amma a halin yanzu ya zama wata hanyar da mutane da yawa ke kokarin bi domin neman kudi.

"Noman zogale na da riba sosai," in ji Dr Shehu O. Adamu, wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ya zama manomin zogale a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.

Adamu, wanda ya yi karatu kan aikin gona, na da kadada biyar ta gonar zogale inda yake iya samun naira miliyan biyu a duk lokacin da ya ciri zogalen a kakarsa.

Abin da ya fi burgewa a nan shi ne zai iya samun wannan kudi sau goma a shekara daya.

Bayaga ganyen zogalai, ana amfani da irinsa bayan an cire shi daga bishiyar:Hoto/Eden Moringa

Hakan ne ya sa ba Adamu kadai ne ya habaka noman zogale zuwa matakin neman kudi ba.

"Mutane na mayar da hankali kan noman zogale a Nijeriya," in ji Dr Michael Ashimashiga, shugaban kungiyar hadin kan manoma zogale a Nijeriya.

Zogale a matsayin magani

Ana alakanta ganyen zogale da kuma irinsa da wasu fa’idoji na magani da ke dakile ayyukan kwayoyin cuta da kuma karfafa garkuwar jiki ta hanyar bitamin da kuma wasu sinadirai.

Duk da cewa mutane sun dade suna amfani da ganyen zogale a matsayin maganin nau'ukan rashin lafiya, har yanzu ana dakon binciken kimiyyar da zai tabbatar da hakan.

Ana tatsar mai daga cikin irin zogalai domin masu bukata :Hoto/Eden Moringa

Kayayyakin da aka sarrafa da zogale sun riga sun shiga kasuwa a kasashen duniya da dama, lamarin da ya sa ‘yan kasuwa suka saka jari kan yiwuwar samun kudi a harkar.

Kamfanin Eden Moringa Productions Ltd da ke Abuja daya ne daga cikin irin wadannan kamfanoni wadanda suka mayar da hankali kan sarrafa zogale zuwa abubuwan iri-iri da ake amfani da su.

Abubuwan da ake sarrafawa daga ganye da irin bishiyar sun hada da shayin zogale da garin zogale da mai, wadanda mutane ke amfani da su don biyan bukatu daban-daban.

“Muna cikin mutanen da ke sayar da zogale ga kamfanoni irin su Eden. Bayan ka cire ganyayyakin tare da busar da su, za ka samu N500,000 a kowace cira," in ji Adamu.

"Idan aka bi ta nauyi kuma, ina ganin a da suna biyan N2,500 ($3.1) a kan kowane kilo na bushasshen ganyen zogale.

Saboda haka, idan kana da gona mai cike da bishiyoyi da yawa, za ka iya samun N500,000 a ko wace cira."

Saboda yadda ake nemansa, farashin kilon ganyen zogale ya karu matuka kwanan nan inda ake sayarwa kan N3,500 ($4.3). Manoma irin su Adamu suna da yakinin cewa wannan abu ne mai dorewa.

"Za ka iya samun N1,000,000 ($1,250) a kadada daya ko fiye da haka a lokaci daya. Kuma za ka iya ci gaba da samun amfani tsawon shekaru masu yawa," in ji shi.

A cewar Adamu, duk wanda yake da sha’awar noman zogale zai iya tsunduma cikin harkar domin bishiyar ba ta bukatar kulawa da yawa kuma zai iya fitowa da kyau a yankunan da ke da fari idan ana ban-ruwa.

Matsaloli

Daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a noma zogale ita ce rashin ruwa. Masana sun ce zogale na bukatar a ba shi ruwa sau daya a mako, ko kuma akalla sau uku a wata.

Masu sayar da abinci na zamani na kawata sana'ar sayar da zogale:Hoto/Habibty's kitchen

Adamu ya shawarci manoman da ke son shiga harkar zogale a inda ba ruwa su tabbatar da wata hanyar samun ruwa irin su rijiyar burtsatse.

"Har ila yau, zogale ba ya son ruwa da yawa; saboda haka mutum na bukatar tabbatar da cewar gonar ba ta wurin da ruwa ke iya taruwa," in ji shi.

A da cirewa da kuma busar da ganyen zogale na tattare da kalubale ga manoma a Abuja, amma wasu daga cikinsu suna da injinan busar da ganye da za su iya gaggauta aikin busar da shi.

Kayan kwalama

Da alama yadda mutane ke kara sanin amfanin zogale a fadin duniya ya yi tasiri a kan rinjayen da yake da shi a cikin kayayyakin kwalama na arewacin Nijeriya.

A da sayar da kwadon zogale aiki ne na tsoffi wadanda suke tallarsa a kan tituna a yankin arewacin Nijeriya. Amma a halin yanzu ana tallan zogale har a shafin sada zumunta na Instagram.

Ummiti Muhammad, mai kamfanin sayar da abinci na Habibty's Kitchen, daya ce daga cikin masu samun kudi ta hanyar sayar da ganyen zogale.

Tana samun buhunhunan ganyen zogale daga manoma a kauyuka sannan ta mayar da su abinci da yawan mutane ke nema.

Habibty's Kitchen na sayar da ‘takeway’ din zogale kan N2, 000 ($2.5).

"Kasuwanci na kyau," kamar yadda Ummita ta shaida wa TRT Afrika.

TRT Afrika