Tun dawowar shugaba Donald Trump mulki aka saka idanu kan ayyukan USAID. / Hoto: AA Archive

Daga Mazhun Idris

Wani jawabi na ɗan majalisar Amurka Scott Perry mai cewa hukumar Amurka ta Bunƙasa Ƙasashen Duniya, USAID ta kasance tana bai wa ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram a Nijeriya kuɗaɗe, ya janyo martani daga ofisoshin diflomasiyya.

Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya faɗa a shafin X ranar 18 ga Fabrairu cewa suna yin tir da Boko Haram saboda "tsabar rashin daraja rai da take", kuma ya tabbatar wa Nijeriya cewa suna "cikakken saka-ido da kula da tsare-tsare don taimakawa wajen tabbatar da tallafin Amurka yana isa ga waɗanda suka dace".

Dalilin wannan sanarwar shi ne wani taron Kwamitin Majalisar Amurka, inda ɗan majalisa daga Pennsylvania ɗan jam'iyyar Republican, Perry ya zargi USAID da ayyukan da ya kira "almubazzaranci da dukiyar al'umma da kuma ƙoƙarin mamaye duniya".

Zarge-zargen Perry sun taɓo wani batu mai hatsari a Nijeriya, inda Boko Haram ta halaka fiye da mutane 50,000 kuma ta tilasta wa miliyan 2.5 barin gidajensu, wasunsu suka tafi Nijar, Chadi, da Kamaru gudun hijira.

Ɓaɓatu a majalisa

Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta ɗauki mataki nan-take kan "gagarumar" matsalar zargin USAID tana bai wa 'yan-ta'adda kuɗi a ƙasar. A makon jiya, Majalisar ta sanar da shirin kiran shugannin tsaro, ciki har da Mashawarcin Tsaro na Ƙasar, don tattaunawar ƙoli.

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno, inda Boko Haram ta aikata ta'annati tun 2009, ya nemi yin binciken ciki-da-bai. Ya alaƙanta zargin Perry da irin daɗaɗɗen zato kan ƙungiyoyin jin-ƙai suna taimaka wa 'yan-ta'adda a yankin, ciki har da samar da horo kan makamai.

"Hukumomin tsaron [Nijeriya] sun kawo wannan batun a lokuta da dama. Gwamnatin Jihar Borno tana yawan zargin ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu," cewar Ndume, yana nuni kan jihar da ta fi cutuwa daga rikicin Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya halaka dubban mutane a Nijeriya, Nijar, Kamaru, da Chadi. / Hoto: AFP

"Mun yi shekaru muna mamaki — baya ga hare-hare da garkuwa da mutane — ina 'yan ta'addar nan ke samun kuɗaɗe? Abin ban-kaye ne. Yanzu da ɗan majalisar Amurka ya fito da abin fili, ba za mu iya watsi da batun a matsayin zargi ba kawai."

Murɗaɗɗiyar matsala

A wata tattaunawa a watan Janairu da Al Jazeera, babban kwamandan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya koka kan yadda Boko Haram ke samun tallafi daga waje cikin shekaru fiye da 20.

Ya koka kan yadda ƙoƙarin sojojin Nijeriya na daƙile Boko Haram yake samun tasgaro daga "ƙasashen waje da ke taimaka musu da kuɗi da makamai".

Janar Musa ya ba da misalin mayaƙan Boko Haram da "ake kamawa suna ɗauke da kuɗaɗen manyan ƙasashen waje, wande ke nuni da akwai 'yan ƙasar waje da ka tallafa musu".

Tsohon ministan harkokin wajen Nijeriya, Prof Bolaji Akinyemi ya ƙarfafa wannan zargi na kwamandan sojojin ƙasar, yayin da yake wata hira da gidan talabijin na Arise TV ranar 17 ga Fabrairu.

Ya ce, "Na shiga wani kwamiti kan Boko Haram, inda mazauna karkara ke yawan gaya mana suna ganin jiragen helikwafta da baƙin haure ke sauka a Borno tare da makamai, alburusai, da maƙudan kuɗaɗe".

Prof Akinyemi, wanda ya yi minista zamanin ƙarshen yaƙin Cacar-baki, ya kuma ƙarfafa tunanin cewa wasu gwamnatocin Yamma suna aiki don tarwatsa Nijeriya, inda ya ce abin ya faro tun lokacin mulkin mallakar Burtaniya.

Tono batu

Martanin Amurka kan maganar Perry ya ƙunshi jawabi kan ayyukanta na diflomasiyya, inda ta ce Sakataren Harkokin Waje na Amurka ya ayyana Boko Haram a matsayin "ƙungiyar waje ta ta'addanci" tun 14 ga Nuwamban 2013, "don toshe kadarorin ƙungiyar da hanyoyin samun kuɗinta, da hukunta mambobinta, da saka takunkumin tafiye-tafiye zuwa Amurka".

"Amurka za ta ci gaba da aiki tare da Nijeriya da abokanta na yankin don yaƙi da ta'addanci," cewar sanarwar.

Yayin da masana tsaro a Nijeriya ke muhawara kan ko wannan batu zai kawo ƙarshen hanyar samun kuɗin Boko Haram, aƙalla dai abin ɓoye ya fito fili.

"Zarge-zargen ɗan majalisar na siyasa ne, duk da ba za a musa cewa wasu ƙasashe a tarihi suna goyon bayan 'yan-ta'adda a duniya ba," inji Kabiru Adamu, wanda shugaba ne na cibiyar al'amuran tsaro ta Beacon Consulting, a zantawarsa da TRT Afrika.

Wani mai sharhi kuma tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya, Adamu Garba yana kallon wannan tonon silili a matsayin "abin ci gaba ga Afirka".

"Idan ka duba jerin ƙasashe 10 da USAID ta fi aiki — daga Ukraine zuwa Sudan ta Kudu — za ka ga kusan waɗannan ƙasashe suna cikin ruɗani duk da yawan kuɗin da suka zuba," in ji shi, a wata zantawa da gidan talabijin.

"Nijeriya tana samun tallafin Amurka da dama da ya kai dala biliyan $1.02 a 2023, da yawansa ta hanyar cibiyoyi kamar USAID. Sannan, akan yi tambaya kan dala miliyan $824 da suke bai wa Nijeriya a 2023. Ina kuɗaɗen ke zuwa? Muna da tabbacin wannan kuɗin ba a amfani da su kan yaƙe-yaƙe ta bayan-fage?"

TRT Afrika