A shekarar 2020 ne Nijeriya ta kaddamar da shirin bunkasa amfani da iskar gas da ake kira CNG/:Hoto/Reuters

Tun bayan da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta cire tallafi kan man fetur ne farashin makamashi da sauran kayayyaki ya tashi lamarin da ya jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali.

Galibin 'yan kasar sun fi amfani da fetur don haka cire tallafin a kansa ya sa farashinsa ya tashi, abin da ya sa sayensa ya zama sai wane-da-wane.

Sai dai kuma masana sun ce Nijeriya na da wani makamashin da ya fi fetur araha wanda za a iya amfani da shi a mota maimakon man fetur.

Sunan wannan makamashi Compressed Natural Gas, wato CNG a takaice -- wata iskar gas ce da aka tsuke ta sosai har ta koma kasa da kashi daya na yawanta.

Iskar gasa ta CNG na da araha don haka ne Shugaba Tinubu ya ce za a raba wa jihohin kasar motocin bas 3,000 masu amfani da ita domin su rika yin jigilar mutane zuwa ofisoshi da sauran wurare.

A kasashe irin su Nijeriya masu arzikin iskar gas, masana na ganin za a iya amfani da iskar gas din maimakon man fetur da farashinsa ke hauhawa a kasuwar duniya.

Iskar gas ta CNG na da tarin yawa a rijiyoyin man Nijeriya, in ji masana.

Masana sun ce amfani da makamashin CNG zai rage hayakin da motoci ke fitarwa mai gurbata muhalli/:Hoto/Reuters

Injiniya Ali Gumel, wani masanin makamashin iskar gas da ke aiki Legas, ya ce masu motoci da ke amfani da fetur za su iya mayar da motocinsu zuwa masu amfani da iskar gas ta CNG domin samun sauki.

Sauki

A cewarsa amfani da iskar gas ta CNG a mota na bukutar sauya wasu abubuwa a jikin mota.

Kuma idan aka yi hakan, masu motar za su samu sauki sosai don kuwa kudin da za a kashe wajen sayen CNG bai kai kashi daya cikin hudu na kudin da ake kashewa kan man fetur ba a halin yanzu.

“Misali, idan za ka yi amfani da fetur na naira 400 don ka yi tafiyar kilomita goma, naira 100 za ka kashe a kan iskar gas din CNG,” in ji Ali Gumel.

Baya ga haka, masana sun ce amfani da wannan iskar gas din zai taimaka wa lafiyar injin mota saboda zai rage yawan hayaki saboda yawancin gas din yana da tsafta.

Rage gurbata muhalli

Baya ga rage hayaki daga injin mota, amfani da iskar gas ta CNG yana rage yawan hayaki mai guba da mota mai amfani da man fetur ke fitarwa wanda zai rage gurbata yanayi, in ji masana.

Sauya mota mai amfani da fetur zuwa mai amfani da iskar gas yana bukatar kashe kudi:Hoto/Reuters

Har ila yau masana sun ce rage yawan hayakin da ke fitowa daga mota zai inganta iskar da mutane ke shaka da kuma lafiyarsu.

Hatsari

Da yake CNG iskar gas ce da aka takure, mutane na fargaba game da hatsarin da ka iya kasancewa tattare da ita.

Amma masana sun ce amfani da iskar gas din CNG bai kai man fetur hatsari ba ganin yadda fetur ya fi CNG saurin kamawa da wuta a yanayi mai zafi.

Wadatattun wuraren sayar da iskar gas

Sai dai kuma wasu na ganin matsalar da za a iya samu kan amfani da iskar gas ta CNG ita ce karancin wuraren da ake sayar da iskar ga masu mota.

Amma tuni wasu dillalan man fetur a Nijeriya suka fara mayar da motocinsu na dakon man fetur motocin dakon iskar gas wadda aka tsuke.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya, Chinedu Okonkwo, ya ce mambobin kungiyarsa sun fara daukar matakin sayar da iskar gas din a gidajen mansu.

“Daya daga cikin manyan dillalan man fetur ya mayar da motocin dakon man fetur din shi sama da 500 zuwa motocin dakon iskar gas,” in ji shi a wata hirar da ya yi da jaridar Punch.

Tun shekarar 2020 ne gwamnatin Shugaba Buhari ta kaddamar da shirin bunkasa amfani da iskar gas ta CNG na Nijeriya domin tattalin arzikin kasar ya koma dogaro kan amfani da iskar gas din.

Masana na ganin idan gwamnati ta tallafa wajen bunkasa amfani da CNG din, makamashin tsukakken gas zai samu karbuwa, kuma mutane za su samu sauki.

TRT Afrika