Daga Abdulwasiu Hassan
Taham Adamu Abubakar, magidanci ne mai ‘ya’ya hudu, kuma yana iya tuna yadda ya ji a matsayinsa na mahaifi, yayin da dansa yake kallonsa cike da ihu lokacin da wanzami ke kokarin cire masa beli daga makogoronsa.
“Idan suka rike yaron, sai su rinka masa kamar ba sa son sa. Yaron sai ya soma kuka, inda za ka fara tunanin za su ji masa ciwo,” kamar yadda Taham, wani dan garin Giade a jihar Bauchin Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika.
“Suna kokarin cire wa danka beli. Ka san dole ne amma ba abu ba ne mai sauki ka zauna kana tunani,” kamar yadda ya bayyana a matsayinsa na uba wanda aka cire wa ‘ya’yansa hudu beli.
A arewacin Nijeriya, cire beli ga jarirai ba wani sabon abu ba ne. Akasari wanzamai ne suke aikin cirewar. A al’adar Bahaushe, wanzami na ayyuka wadanda suka hada da kaciya da yin kaho da kuma cire beli.
“Cikin duka abubuwan da muke yi a aikinmu, cire beli shi ne abu mafi wahala,” kamar yadda Baffa Aliyu Zindiri wanda aka fi sani da Baffa Wanzam ya shaida wa TRT Afrika.
“Saboda abin da za a cire yana kusa da makogoro,” in ji shi.
Baffa Wanzam na ganin mayar da hankali kwarai da gaske na daga cikin muhimmin abin da ake bukata wurin cire beli.
Dauke numfashi
Wanzamin yana amfani da wani tsinke wanda ake kira mataki domin danne harshen jariri da kuma wani karfe mai lankwasa domin cire belin.
Dole sai an bi a hankali domin kada a girgiza ko a yi motsi da kayan aikin saboda ka da a yi wa makogoron rauni.
“Idan jaririn ya bude bakinsa domin ya yi kuka, ana amfani da hakan domin danne masa harshe. “Idan aka danne harshen kafin bakin ya rufe,” in ji shi.
Da zarar belin ya hau kan karfen, akwai bukatar wanzamin ya dauke numfashinsa kafin ya cire belin. “Idan ka yi numfashi, hannun ka zai motsa.
Da zarar hannunka ya motsa, karfe zai iya taba makogoro ko ya taba can kasan harshen,” kamar yadda Baffa Wanzam ya yi gargadi.
Ya bayyana cewa lakantar cire beli shi ne babban ginshikin aikin wanzamai. D zarar mai koyon aikin wanzanci ya iya cire beli, ya cancanci zama wanzami.
Yana tattare da hatsari
An samo batun cire beli ne kan maganar da ake yi kan cewa idan aka bari belin ya girma, ko ruwan nono yaro ba zai iya sha ba sai dai ya zubar da shi.
Taham, wanda aka yi wa wannan cire belin a lokacin yana jariri kamar nasa jaririn, haka kuma shi ma ya yarda cewa cire belin yana taimaka wa yara kauce wa matsalar da ke tattare da matsalar ta beli har su girma.
Sai dai likitoci na zamani na ganin bai kamata a rinka cire beli ba sai da wata matsala wadda ta taso wadda ta bukaci a cire shi.
“Cire beli a gargajiyance ba shi da amfani kuma yana da illa a mahangar likitoci,” kamar yadda Dakta Fatima Damagum, wadda likita ce a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bayero da ke Kano ta fada.
“A wasu kauyuka na Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, wasu na ganin cire beli na taimakawa wurin magance ko kuma kiyaye wasu ciwuka da suka hada da zubar da yawu da matsalar magana da mashago da kumburin beli da wasu matsaloli na numfashi,” in ji ta.
A zahiri, babban amfanin beli shi ne hana ruwa ko abinci tafiya saman hanci idan mutum ya yi hadiya.
Masana kiwon lafiya sun ce cire beli ta hanyar gargajiya na tattare da hatsari.
“Hatsarin da ke tattare da cire belin ya hada da zubar da jini da kamuwa da cuta da jin ciwo a makogoro da kawo matsala wurin magana da matsalar hadiya da ta numfashi. A wani lokacin ma har mutuwa ake yi,” in ji Dakta Damagum.
“Daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta da cire beli shi ne zubar da jini. A wani lokacin zubar da jinin na faruwa ne ta cikin jiki, inda yaro zai ci gaba da hadiye jini sakamakon iyayen ba lallai su lura ba har sai jinin ya yi yawa ya jawo mutuwa.”
Har yanzu ana yi
Wata matsala kuma da ake samu sakamakon cire belin ita ce ta kamuwa da cuta sakamakon amfani da aska wurin cire beli.
Cutuka da suka hada da HIV da ciwon hanta da sauran cututtuka da ake kamuwa da su abubuwa ne na lura, in ji Dakta Damagum.
Sai dai wadanda suke gudanar da wannan aikin suna tababa da gargadin na likitoci. A gare su, babu matsala idan aka yi aikin lafiya kalau.
“Wannan shekarar ce aka cika shekara 35 tun da na fara cire beli. Babu wanda na taba cire wa beli da ya taba fuskantar matsala,” in ji Baffa Wanzam.
Taham ya amince da batun na wanzaman, “Ni ko yarana ba mu taba fuskantar matsala da cire beli ba,” in ji shi.
Baffa Wanzam ba zai iya lissafa adadin mutanen da ya yi wa aikin ba. “Na gudanar da aikin cire belin mutum sai na yi na dansa bayan shekaru. Na yi wa uwa na yi wa ‘yarta.
"A rana guda, mutum zai iya zuwa gidaje biyar zuwa shida yana zuwa cire beli wani lokacin kuma mutum zai iya yin kwanaki uku ko hudu ba tare da na yi aikin cire belin ba,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Haka kuma ya ce soma barin masu koyon aiki a wurinsa yin aikin cire beli. Baffa Wanzam ya ce a bana kadai, ya yi aikin cire beli kusan sau 50 zuwa 60.
Akwai bukatar karin taka-tsan-tsan
Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarar cewa wadanda aka yi wa wannan aikin na gargajiya akwai bukatar su je asibiti domin kwararru su duba su.
“Babban dalilin shi ne a gane wane irin cire belin aka yi, duka ne aka cire ko kuma rabi da kuma irin raunin da aka ji. Za kuma a lura da wasu alamomi, za kuma a yi gwajin jini,” in ji Dakta Damagum.
“Za a yi sikanin domin ganin cewa idan akwai zubar da jini, sannan akwai bukatar a bayar da maganin kashe kwayoyin cuta domin kauce wa kamuwa da cuta,”
Idan aka ga alamar zubar da jini, za a iya yi wa yaron karin jini ko na ruwa. “Akwai matukar bukatar a yi allurar tetanos,” in ji Dakta Damagum.
Likitan ta bayar da shawara ga wadanda aka yi wa cire beli da su rinka tsaftace bakinsu da kuma goge baki da kuskure baki da shan ruwa mai yawa, da tsotsar alewa ko cin cingam, da kuma nesantar masu tari ko mura da cin abinci mai ruwa.