Umar Yunus daga Jos
Damina wani yanayi ne da ake yin ruwa sama a-kai-a-kai. A irin wannan lokaci, kasa na jikewa ta yi shakaf, abin da ke haifar da yanayi mai sanyi.
Akwai fa'idoji masu yawa tattare da lokacin damina da suka hada da saukaka hanyoyin samar da abinci kamar noma da kiwo. Manoma suna zagewa su yi aiki tukuru a wannan lokacin saboda ƙasa ta yi laushi kuma ba su da matsalar ban-ruwa.
Suma makiyaya a nasu bangaren, suna ribatar lokacin damina sosai saboda wadatar ciyayi da sauran tsirran da dabbobi ke bukata.
Fa'ida ta biyu da damina ke haifarwa ita ce bai wa tsirrai da bishiyoyi sukunin rayuwa a sake domin ba sa samun ƙarancin ruwa.
Har ila yau, damina na samar da wadataccen ruwa a rafuka da koguna da koramu da tafkuna da rijiyoyi da madatsun ruwa da karkashin kasa da kuma sauran wuraren da ruwa ke taruwa don amfanin bil adama da dabbobi da ma sauran halittu kamar kududdufi da gulbi.
A daya bangaren kuma, damina na zuwa tare da wasu abubuwa da ke da mummunan tasiri ga rayuwar bil adama ta yau da kullum, kamar ambaliya, da zaftarewar ƙasa, da hana dabbobi da tsuntsaye da kwari sukuni da kuma uwa uba, haifar da wasu cututtuka, musamman masu nasaba da sanyi.
Yayin da daminar bana ke ci gaba da faɗuwa a sassan Duniya dabam dabam (yanayin wasu yankunan sun bambanta da juna), masana kiwon lafiya a Najeriya suna shawartar mutane, musamman mazauna yankuna masu sanyi, game da hatsarin da ke tattare da sakankancewa ba tare da sun dauki matakan kariya daga sanyi da sauran cututtukan damina ba.
Dakta Sabo Ahmad Muhammad, Farfesan Ilimin Kiwon Lafiya a Kwalejin Koyon Aikin Lafiya ta Jami'ar Jos ne, kuma ya kasa nau'in cututtukan da ke addabar mutane lokacin damina gida biyu.
A cewar Dakta Sabo, a farko farkon damina, lokacin da ruwan sama bai yi karfi ba, cututtuka masu nasaba da kazanta suna yawaita. Wadannan cututtukan sun hada da zazzabin cizon sauro, da amai da gudawa, da kurajen damina da kuma zazzabin hanji wato Typhoid a turance.
"A farko-farkon damina, ruwa na ɗebo kazanta ya kai ta inda za ta gurbata ruwan da ake sha da ke rijiyoyi da famfuna. Ga kuma shara da najasa da mutane ke zubawa a kwatami da kuma bola a cikin unguwanni da ba a kwashe ba," in ji shi.
"Duk wannan ƙazantar, idan ba a ɗauki mataki ba, ita ce ke haifar da wadannan cututtukan idan sauro da sauran kwari suka yada ta a tsakanin mutane," a fadar Dakta Sabo.
Likitan ya ce cututtukan damina kashi na biyun su ne masu nasaba da sanyi kamar sarkewar numfashi da asma da ciwon zuciya. A cewarsa, sanyi na ta'azzara waɗannan cututtukan ya jefa mutanen da ke fama da su cikin mawuyacin yanayi.
Ya ce irin sanyin da ake magana a kai, shi ne wanda idan mutum ya shake shi, zai yi ta atishawa, hancinsa ya toshe, manumfasa ta takure, ta ki budewa, don mutum ya yi numfashi cikin walwala.
Malamin jami'ar ya ci gaba da cewa, "sanyi yana yi wa mai ciwon asma illa sosai. Yana sa numfashinsa ya yi ta ziza, ya shide, har ta kan kai ga rasa rai, idan bai samu kulawar gaggawa ba."
Likitan ya ci gaba da bayyana cewa hatta masu ciwon zuciya, musamman tsofaffi, ba su kubuta daga sharrin farmakin sanyi ba; domin idan suka shaki iska mai sanyi da ta wuce misali, za su iya samun bugun zuciya.
Sai dai kuma ya ce sanyi ya fi yin illa ga rukunin mutanen da jikinsu ke da rauni bisa halitta ta yadda ba zai iya bijire wa sanyin ba. Ya bayar da misali da yadda jikin mai fama da asma ke kasa bijire wa kura duk da jikin nasa ba ya son ta.
Dakta Sabo ya jaddada cewa yawan shekaru ma yana taimaka wa sanyi wajen ta'azzara cututtukan da ke jikin mutane.
"Idan girma ya zo wa mutum, to fa wajen da ya fiye sanyi ba wajen zamansa ba ne, saboda da sanyin zai iya sa wa jikinsa ya yi rauni, har ta kai ba zai iya bijire wa wasu cututtuka ba," a cewarsa.
Wannan matsala ce da ta zama ruwan dare a kasashe masu tasowa kamar Nijeriya. Saboda haka, malamin jami'ar ya ce, idan ana so a ga bayan ta, wajibi ne a ɗauki matakai kamar haka:
Da farko, ya kamata mutane su kauce wa zama a muhalli da ke da alaƙa da sanyi kai-tsaye, kamar bakin rafi da fadama da lambu da sauransu. Gidajen da aka gina a irin wadannan wuraren suna fama da rima da danshi, alama da ke nuna wanzuwar sanyi da ke shiga jikin bil'adama a hankali.
Abu na biyu, shi ne mutane su dinga saka suturu masu kauri da za su saka jikinsu ya kasance cikin dumi a kodayaushe. Kuma idan so samu ne, su dinga shan ruwan dumi fiye da na sanyi.
Da farko, ya kamata mutane su kauce wa zama a muhalli da ke da alaƙa da sanyi kai-tsaye, kamar bakin rafi da fadama da lambu da sauransu.
Har ila yau, mutane su muhimmantar da cin cimaka mai gina jiki tare da sinadaran gargajiya masu bayar da kariya daga sanyi kamar citta da tafarnuwa da sauransu.
A cewar likitan, ya kamata mutane su dawo da dadaddiyar al'adar nan ta yi kwalema akai akai domin kawar da tarkace da shirgi masu rike sanyi a cikin gida. Kuma su tabbatar sun hana danshi da rima zama a dakunan kwanansu.
Ya kara da cewa, mutane su lazimci shafa mayukan gargajiya kamar man shanu, da man kade, da man alaidi da kuma mayuka na zamani masu inganci domin bai wa fatarsu kariya daga ƙurajen damina.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga hukumomin da ke da alhakin tsara gari, da duba gari da kuma kula da tsaftar muhalli da su tashi tsaye wajen tabbatarwa mutane sun dena taka dokar gine gine da kuma ta kula da muhalli. Duk wanda aka kama yana zuba kashi da shara a magudanan ruwa a hukunta shi, domin hakan ya zama izina ga wasu.