A yau ne aka fara tantance mutum 14 daga cikin mutum 28 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya mika wa majalisar dattawan kasar domin nada su mukamin ministoci.
A makon jiya ne dai fadar shugaban kasar ta Nijeriya ta mika sunayen mutanen ga majalisar dattawan kasar don tantancewa.
Jihohi 25 na kasar sun samu wakilcin akalla mutum daya, yayin da kawo yanzu fadar shugaban kasar ba ta mika sunayen wadanda za su yi minista daga jihohin Adamawa, Bayelsa, Gombe, Kano, Kebbi, Kogi, Filato, Legas, Osun, Yobe da Zamfara ba.
Ga abu biyar da suka ja hankali a yayin zaman tantance ministocin da majalisar dattawa ta yi a yau:
‘Mutanena sun raka ni gida’
Tsohon gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shaida wa 'yan majalisar dattawan cewa zai taka muhimmiyar rawa ci gaban Nijeriya idan aka tabbatar da shi a mukamin minista yana mai cewa Shugaba Tinubu ba zai yi da-na-sanin nada shi ba.
Ya ce don tsabar aikin da ya yi a jiharsa a lokacin da ya kammala wa’adinsa na biyu mutane sun raka shi gida kuma mata suka shimfida zannuwansu domin ya taka ya wuce.
Nyesom Wike ya ce shi bai taba barin jiharsa ya je ya kwana a waje ba a yayin wa’adinsa na biyu domin yadda yake son jiharsa.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa BarauJibrin ya ce ya yi tsammani yana kasar waje ne da ya je jihar Ribas domin ganin aikin da Wike ya yi a jihar.
Daga nan sai mataimakin shugaban majalisar ya ce wa Wike ya yi gaisuwa ya wuce.
Daga baya shugaban majalisar, Sanata Godswil Akpabio, ya ce dalilin da ya sa ba su yi wa Wike tambayoyi ba shi ne ya taba aiki a matsayin minista kuma majalisar dattawan ta tantance shi a wancan lokacin kafin ya samu damar zama minista.
‘Na gama makarantar Firamari a shekara tara’
Sanatoci sun yi ta mamakin yadda Farfesa Joseph Utsev, da aka gabatar daga jihar Binuwai ya kammala karatun firamare a shekarar 1989 bayan an haife shi a shekarar 1980.
Bayan Sanata Tokumbo Abiru na jihar Legas ya yi tambaya game da yadda farfesan ya gama makarantar firamare yana dan shekara tara da haihuwa, farfesan ya ce ba abin mamaki ba ne.
Farfesa Utsev ya yi bayanin cewar shi ya shiga makarantar firamare kuma ya kammala karatun a shekarar 1989.
Amma wasu sanatocin ba su gamsu ba, sai dai kuma shugaban majalisar ya ce shi ba zai sake sauraron tambaya game da lokacin da farfesan ya fara ko gama makaranta ba bayan Sanata Abba Moro ya yi masa wani bayani a asirce.
Sai dai kuma Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa ya kai wa farfesan dauki a lokacin da ya ce “Na yi jarrabarawar kammala karatun a lokacin da nake aji uku a makarantar Firamare, kuma na yi nasara saboda irin basirar da nake da ita.”
‘Ka kawo sauran takardunka’
Shugaban majalisar dattawa, Godswil Akpabio, ya ce wa Bello Goronyo ya dauko sauran takardun shaidar kammala makarantar sakandarensa a lokacin da tsohon kwamishina a jihar Sokoto din ya bayyana a gaban majalisar dattawa don tantancewa.
Wannan ya biyo bayan tambayar da wani sanata ya yi wa mutumin da ake son a nada ministan ne kan ta yaya ya shiga jami’a da takardar shaidar kammala sakandare mai kiredit biyu.
Bello Goronyo dai ya ce shi yana da wata takardar shaidar kammala makarantar sakandaren, amma bai dauko ta ba domin ba ya son ya takura wa majalisar kuma takardar shaidar kammala karatun sakandare kawai tsarin mulki ke bukata.
Sai dai kuma, ‘yan majalisar ba su yarda da wannan bayanin na sa ba, dalilin da ya sa shugaban majalisar ya ce ya dauko sauran takardun shaidar kammala karatun sakandarensa.
‘Abin da ya sa ake ce mini mai kalkulata’
A lokacin da ya bayyana a gaban majalisa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru, ya ce abin da ya sa ake ce masa mai kalkulata shi ne irin dagewar da yake yi wajen tabbatar da cewa an yi aikin gwamnati yadda ya dace kuma ko nawa za a kashe ya dace a lissafa shi .
Wannan ya sa ‘yan majalisa suka sheke da dariya, kuma shi ma Badarun ya kyalkyale da dariya.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawan ya ce shi yana da wani dan uwa kuma a majalisar wanda ake ce wa kalkulata, yana mai cewa tsohon gwamnan Ebonyin Dave Umahi ne.
Babu hukuncin kotu da ya hana ni rike mukamin gwamnati
Mutumin da ake son a nada minista daga jihar Taraba, Sanata Danladi Sani, ya ce ba gaskiya ba ne rahoton da ake cewa a shekarar 2019 Kotun Kolin Nijeriya ta hana shi rike mukamin gwamnati tsawon shekara 10.
Da ya bayyana a gaban majalisar, tsohon gwamnan na jihar Taraba ya ce Kotun Kolin Nijeriya ba ta hana shi rike mukamin gwamnati ba.