Burin Nijeriya na ƙirƙiro sabbin jihohi 31.

Daga

Abdulwasiu Hassan

Majalisar wakilan tarayyar Nijeriya na nazarin shawarwarin da za su iya ƙara yawan jihohin kasar daga 36 zuwa 67, lamarin da ya sa masana da 'yan kasar ke yin hasashe kan illolin wannan mataki.

Idan har aka amince da shawarwarin da Majalisar Dokoki ta Kasa ta gabatar, hakan na iya zama daya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin mulki tun bayan komawar Nijeriya mulkin farar hula a 1999.

Yayin da jama’a ke ta cece-kuce kan hakikanin shawarwarin, kakakin majalisar wakilai, Akin Rotimi, ya yi karin haske a kwanakin baya cewa, rahotannin da ke nuni da cewa majalisar na ba da shawarar kafa sabbin jihohi ba gaskiya ba ne.

“Wadannan kudurori masu zaman kansu ba sa wakiltar matsayin majalisar,” in ji Rotimi, yana mai tabbatar da cewa za su bukaci a bi tsarin dokoki, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana.

Sassaucin tsarin gyaran kundin tsarin mulki na samar da sabbin jihohi yana cikin tsarin tarayyar Nijeriya.

Bayan amincewar majalisun tarayya da na jihohi, amincewar Shugaban Ƙasa ya zama tilas kafin kasar ta fadada adadin jihohi.

Wani babban lauya Barista Mainasara ya shaida wa TRT Afrika cewa, "Babban lamari ne a ce a samu 'yan majalisun jihohi 36 na tarayyar kasar su zauna su tattauna kan wannan batun."

"Ana bukatar kashi biyu bisa uku na yawansu, ko kuma jihohi 24, su goyi bayan shirin, sannan kuma ana bukatar kashi uku na Majalisar Dokoki ta ƙasa su don tabbatuwar hakan."

Wannan tsattsauran tsari yana taimakawa wajen bayyana dalilin da yasa yunƙurin ƙirƙirar ƙarin jihohi a baya bai tabbata ba duk da yawancin shawarwarin da aka gabatar a cikin shekaru 25 da suka gabata.

Tsare-tsare masu haɓaka

Rarraba harkokin mulki a Nijeriya ya samu cigaba sosai tun bayan mulkin mallaka.

Kasar ta fara ne da yankuna uku bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, inda sannu a hankali ya dinga ƙaruwa a karkashin gwamnatocin soja da na farar hula daban-daban.

Tsarin da ake da shi na jihohi 36 na yanzu an kafa shi ne a shekarar 1996 a lokacin Sani Abacha a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soja.

A cikin wannan cigaba da aka yi ta samu, waɗannan sassan gudanarwa sun yi aiki guda biyu, suna aiki a matsayin sassan gudanarwa yayin da suke tantance yadda ake rarraba albarkatun ƙasa da kudaden shiga a faɗin tarayyar ƙasa.

Shawarwarin da aka gabatar a yanzu sun sake haifar da doguwar muhawara game da batutuwan wakilci da rabon albarkatun ƙasa, da haƙƙin tsiraru a cikin tsarin Nijeriya daban-daban.

Masu fafutuka da yawa na sabbin jihohi da za a ƙirƙira daga cikin ƙungiyoyin da ake da su suna jayayya cewa shirye-shiryen da ake yi a halin yanzu sun bar wasu ƙabilun da wasu yankunan ba su da wakilci wajen rarraba albarkatu.

Dokta Mainasara Umar, wanda ya ƙware kan sani doka da tsaro da tattalin arziki da siyasa da diflomasiyya na kasa da kasa, yana ganin akwai fa'ida sosai a ƙara yawan jihohin.

"Akwai yiwuwar yin hakan ya sa a faɗaɗa rabon albarkatun ƙsa ta yadda ba za a bar kowa a baya ba. Ga wadanda ba su da damar samun gata na gwamnati a matakin tarayya, hakan zai sa tsarin ya matsa kusa da su," in ji shi.

Magoya bayan wannan matakin na ganin cewa samar da ƙarin ƙananan sassan gudanarwa na iya inganta wakilcin dimokuradiyya da tabbatar da samun ci gaba mai inganci.

Kaɗan mai amfani

Wasu masu sukar lamarin na cewa samar da sabbin jihohi za su biya bukatun masu ido da kwalli ne kawai maimakon inganta rayuwar sauran ‘yan kasa a gwamnatance.

Irin wannan damuwar ta samo asali ne daga yadda aka dinga ganin yadda tsarin mulki na jihohi ya fi amfanar manyan ‘yan siyasa fiye da talakawa.

Dokta Usman Bello na sashen nazarin tattalin arziki na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya yana da ra’ayin ci gaba da aiwatar da duk wani shiri mai tsauri.

"Ba mu daɗe da gama zazzafar muhawarar da ta kusan raba kasar nan kan batutuwan da suka shafi sake fasalin haraji da tsadar rayuwa.

Dama jihohi da dama ba sa taɓuka wani abin kirki wajen samar da kudaden shiga. To, wace madogara ake da ita ta fannin tattalin arziki na samar da jihohin da ba za su iya samar da isassun kudaden shiga don gudanar da ayyuka yadda ya kamata ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Hausa.

Dokta Bello ya nuna cewa kasar na fuskantar tabarbarewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki.

Yana kuma tababa idan Nijeriya za ta iya zuba jarin samar da ababen more rayuwa da ake bukata don kafa hukumomi masu aiki a cikin sabbin jihohi 31, wadanda suka hada da gine-ginen gwamnati, da tsarin ma’aikatan gwamnati, da muhimman ayyuka.

Damuwa game da ɗorewar tattalin arziƙin ta ta'allaka ne ga jihohin da ake da su, waɗanda yawancinsu ke fafutukar cim ma muhimman wajibai na kuɗi, da kuma biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati.

Babbar damuwar ita ce ƙara yawan jihohi a kan waɗanda da ma can ke fafutukar tsayawa da ƙafarsu zai ƙara zama wahala ga gwamnatin tarayya a ƙoƙarinta na rabon isassun kuɗaɗen shiga.

Ko tsarin majalisar zai magance wadannan abubuwan da suka shafi tattalin arziki da zamantakewar siyasa yadda ya kamata, yayin da shawarwarin ke ci gaba da tafiya ta hanyar dogon tsarin gyara tsarin mulkin Nieriya.

Muhawarar ta nuna irin fafutukar da Nijeriya ke ci gaba da yi na daidaita muradun yankin da samar da ci gaba mai inganci da dorewar kasafin kudi a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka.

TRT Afrika