Mali

Wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai kan sojojin Mali da sojojin hayar Rasha na Wagner ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 32 a arewacin ƙasar, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Asabar.

An kai harin ne a ranar Juma'a tsakanin garuruwan Gao da Ansongo da ke arewacin kasar, in ji su.

An bayyana adadin wadanda suka mutu da farko ya kai 10 amma daga baya adadin ya kai 32.

"Muna da gawawwaki fiye da 30 daga wurin," in ji wata majiyar asibiti a Gao.

Wani jami’in yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, masu iƙirarin jihadi sun yi wa ayarin motocin fararen hula da sojoji ke rakiya kwanton-ɓauna.

"Akwai fararen hula da sojoji a cikin wadanda suka mutu."

Wata majiyar lafiya ta ce an kai da dama daga cikin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa birnin Gao.

Wata majiya daga ƙungiyar masu jigilar kayayyaki ta ce: "A cewar wani dan jigilar kayayyaki da ya yi nasarar tserewa, mayakan masu iƙirarin jihadi sun yi wa ayarin motocin kwanton-ɓauna tare da buɗe wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadin shafar mutane da yawa."

Wani jami'in yankin ya shaida wa AFP cewa: "Sojojin Mali da Wagner na cikin motoci kusan 10 da ke kare ayarin ƙananan motocin bas guda 22 waɗanda ke ɗauke da fasinjoji fararen hula da manyan bas shida da motocin ɗaukar kaya takwas."

AFP