Daga Abdulwasiu Hassan
Ghana na daya daga cikin kasashen Afirka da ke bakin ruwa da kuma ke da dumbin arzikin ruwa amma kasar na ta gwagwarmayar samar da isasshen kifi domin ci.
Kasar ta dogara ne kacokan kan shigo da kifi inda take kashe kudi masu yawa, lamarin da ke kawo cikas ga kananan manoman kifi na kasar.
Wannan lamari ne da mataimakin minista kan harkokin kifi na kasar Ghana Moses Amin ya koka a kai.
A wani taro wanda ma’aikatar kula da kiwon kifi ta Ghana, Mista Anim ya bayyana cewa ma’aikatarsa a shirye take domin ta habaka samar da isassun kifi a cikin gida da kuma rage shigo da kifin sakamakon halin da ake ciki.
Kamfanin dillancin labara na Ghana ya ruwaito ministan yana cewa “da duka kalubalen da ake fuskanta bayan korona, kasashen da za su kai labari su ne kasashen da za su rage shigo da kayayyaki.”
Kifi ne ke bai wa ‘yan Ghana kashi 60 cikin 100 na sinadarin Protein.
Haka kuma kafafen watsa labarai na kasar sun ruwaito mataimakin ministan yana bayani a lokacin wani taro na ranar manoma ta kasar a Disambar bara inda yake cewa kasar na kashe dala miliyan 240 domin shiga da kifi cikin kasar a duk shekara.
Kasar na samar da kusan tan 600,000 ne na kifi a duk shekara, cikin tan miliyan 1.2 da ya kamata a ce ta samar da kasar ke bukata.
Masana na da yakini kan damar da Ghana ke da shi inda suke ganin za ta iya samar da kifi fiye da hakan.
“Ghana na daga cikin kasashen da ke yanayi mafi kyau na kiwon kifi. Muna da kogi, da tafki da kuma kasa mai kyau da za a yi kududdufi,” kamar yadda Jacob Adzikah, shugaban cibiyar kiwon kifi ta Ghana ya shaida wa TRT Afrika.
Ya bayyana cewa kasar tana da dama fiye da wasu kasashen Yammacin Afirka a wurin kiwon kifi.
Raguwar samar da kifi
Duk da kifin da ake shigarwa kasar da kuma wanda ake kiwo a cikin Ghana, har yanzu akwai karancinsa a kasar.
Lamarin yana da tarihi inda babu wata alama ta ci gaba. Masanin ya bayyana cewa adadin kifin da ke da akwai a kasar da ke Yammacin Afirka yana raguwa.
Kamun kifi ba bisa ka’ida ba a cikin ruwan kasar wadanda har wasu baki suke yi da ke zuwa da jirgin ruwa na daga cikin manyan kalubalen da ke kawo cikas ga yunkurin da Ghana ke yi na samar da isassun kifi.
Ana zargin masu zuwa da jirgin ruwan suna kama kifi kadan ba bisa ka’ida ba – inda a wani lokacin suke sayar wa masu kamun kifi da ba su da galiho.
Wannan sayar da kifin wanda ake yi ba bisa ka’ida ba an fi saninsa da ‘saiko’ inda ake ganin yana rage yawan kifayen kasar, tare da kawo raguwa matuka ga kudi ko ribar da ya kamata Ghana ta samu, da kuma hana jama’ar kasar samun muhimmiyar hanyar samun sinadarin protein.
An sayar da kusan tan 100,000 na kifi da ya kai kimanin dala miliyan 50 zuwa tamanin a 2017 ta haramtaciyyar hanya.
A 2021, gwamnatin kasar Ghana ta haramta kamun kifi ba bisa ka’ida ba da kuma sayar da kananan kifin a bakin teku.
Sai dai wasu sun bayyana cewa hakan bai magance matsalar ba domin damuwar da ake nunawa kan raguwar kifi a Ghana da kuma karuwar jama’a a kasar.
Tsadar abincin kifi
“Muna kawowa wani lokaci, wanda za mu rinka shigo da kifi gaba daya wanda za a ci,” in ji Dakta Kalam-Deen Ali na Cibiyar Nazarin Dokoki da Tsaron Sufurin Teku a Afirka da ke Ghana.
Ya shaida wa manema labarai a lokacin wani taron kara wa juna sani kan batun magance matsalar kamun kifi ba bisa ka’ida ba kan cewa hakan na karar da kifin Ghana.
Baya ga batun magance matsalar kamun kifi ba bisa ka’ida a, wasu masana na ganin akwai bukatar a kara habaka kiwon kifi ga kasar da ke Yammacin Afirika.
Amma manoma kifi na fuskantar kalubale da dama da suka hada da tsadar kudin abincinsu. Kiwon kifin ne ke lashe kashi 60 zuwa 70 na akasarin kudin da ake kashewa wurin kiwon.
“Kudin abincin kifi ya karu da kashi 200 cikin 100 a cikin a cikin watanni takwas,” in ji Jacob Adzika shugaban Cibiyar Kiwon Kifi ta Ghana.
Akwai kuma karancin sanin lafiyar kifaye ga su manoman kifin – inda wasu ba su da ilimin yadda za su kare ‘yan kananan kifaye daga mutuwa.
Za mu kara mayar da hankali
“Adadin kudin ruwan da ake bayarwa idan ka ranto kudi daga banki ya karu. Ya kai kashi 40 cikin 100 a halin yanzu,” in ji Jacob, inda yake kara nuna wani kalubalen.
Gwamnatin Ghana ta ce ta kwana biyu tana kaddamar da tsare-tsare wadanda suke mayar da hankali wurin kara habaka bangaren samar da kifi, daga ciki har da wani shiri mai suna ‘Aquaculture for Fish and Jobs’.
Wannan shirin an kaddamar da shi ne a 2018 domin samar da kayayyakin noman kifi ga manoma domin habaka kiwon kifi.
Mataimakin ministan kiwon kifi Moses Anim ya bayyana cewa gwamnatin kasar na kokarin kara karfin gwiwa domin habaka samar da kifi a cikin kasar ta hanyar hana masu son shigar da kifi cikin kasar kudin kasar waje domin kasuwanci.
Amma Jennifer Sodji, shugaban kungiyar masu kiwon kifi ta Ghana yana ganin cewa akwai bukatar gwamnatin Ghana ta kara kokari.
Akwai bukatar hukumomi “su rage haraji a bangaren” domin rage tsadar abincin kifi wanda akasari shigar da shi kasar ake yi, kamar yadda Sodji ta shaida wa TRT Afrika.
Ta bayyana cewa “bayar da tallafi ga manoman kifi” zai taimaka kiwonsu ya bunkasa” domin samar da kifin a cikin kasar.
“Ina ganin za mu iya yin abubuwa da dama a wannan bangaren” kamar yadda ta bayyana.