Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa za a soma nuna shiri na musamman kan jerin ayyukan Shugaba Muhammadu Buhari a kafafen watsa labarai na kasar.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, ya fitar ranar Lahadi ya ce za a soma nuna shirin ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Mayun 2023 zuwa Talata 23 ga watan na Mayu.
Adesina ya bayyana cewa shirin na musamman kan ayyukan shugaban kasar, wanda ke da tsawon kusan awa guda, zai yi bayani a takaice kan muhimman nasarorin da gwamnatin ta samu tsawon shekara takwas.
“Bayan kammala shekara takwas, wa’adi biyu na mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, bangaren watsa labarai na fadar shugaban kasa ya samar da shiri na musamman mai tsawon minti 55 mai taken ‘Muhammadu Buhari Was Here,” in ji sanarwar.
Buhari ya nemi afuwar mutanen da ya bata wa rai
Sanarwar ta bayyana cewa shirin na musamman wanda zai yi bayani kan muhimman ayyukan gwamnatin za a soma nuna shi a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi 21 ga watan Mayu da misalin karfe 6:00 na yamma.
Haka kuma kafar watsa labarai ta kasar wato NTA za ta nuna a ranar Litinin 22 ga watan Mayu da misalin 8:00 na dare sai kuma kafar watsa labarai ta TVC a ranar Talata 23 ga watan Mayu da misalin karfe 6:00 na yamma.
A ranar 29 ga watan Mayu ne Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ga zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu bayan ya kammala shekara takwas a kan karagar mulki.